Matasan Arewa Na roƙon Sanata Goje Ya Fito Takarar Zama Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa
Ahmed Afauwala, yace jam’iyyar APC a halin yanzu tana bukatar mutum irinSanata Goje, a matsayin shugaban ta, ya kuma bukaci Danzago ya yi isa musa da kiran su ga Sanata Goje ya tsaya takarar shugabancin neman wannan matsayi na jam’iyyar su wanda yake da cancantar da ta kai a zabe shi a matsayin sa na tsohon ministan wutar lantarki, tsohon gwamnan jihar Gombe da yayi karo biyu sannan yanzu yake Sanata zababbe karo na uku da yake wakiltar Gombe ta tsakiya a Majalisar Dattawa. A cewar sa “muna bukatar ya tallafa ma harkar mu idan bukatar hakan ta taso, tare da sakon taya murna ga Alhaji Ahmadu Haruna Danzago, bisa nasarar da ya samu a kotu bayan wasu matsaloli da suka faru.
Daga Habu Rabeel, Gombe.
Wata Kungiyar matasan arewacin Najeriya mai fafutukar neman Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa, ta jaddada kiran ta gareshi kan batun yarda ya fito neman takarar kujerar shugabncin jam’iyyar na APC a kasa.
Shugaban kungiyar ne na kasa Kwamared Ahmed Abubakar Afauwala, tare da sauran jiga-jigan kungiyar kungiyar wajen jefawa Sanata Goje kuri’ar amincewa kan ya amince ya fito ya nemo wannan kujerar dan cire musu kitse a wuta.
Ahmed Afauwala, yace jam’iyyar APC a halin yanzu tana bukatar mutum irinSanata Goje, a matsayin shugaban ta, ya kuma bukaci Danzago ya yi isa musa da kiran su ga Sanata Goje ya tsaya takarar shugabancin neman wannan matsayi na jam’iyyar su wanda yake da cancantar da ta kai a zabe shi a matsayin sa na tsohon ministan wutar lantarki, tsohon gwamnan jihar Gombe da yayi karo biyu sannan yanzu yake Sanata zababbe karo na uku da yake wakiltar Gombe ta tsakiya a Majalisar Dattawa.
A cewar sa “muna bukatar ya tallafa ma harkar mu idan bukatar hakan ta taso, tare da sakon taya murna ga Alhaji Ahmadu Haruna Danzago, bisa nasarar da ya samu a kotu bayan wasu matsaloli da suka faru.
Da yake mayar da jawabi Alhaji Ahmad Haruna Danzago, cewa yayi yana da kyau a siyasan ce a nuna yatsa ga wanda ya dace irin Sanata Muhammad Danjuma Goje, da yake da kwarewa shi ya dace ya rike wannan babban mukami dan sake ceto Jam’iyyar APC da al’ummar Najeriya,
Daga nan sai yace Goje, ne zai iya kawo karshen matsalolin da suka dabai baye Jam’iyar APC a fadain kasar nan,idan Allah ya yi mana jagora.
managarciya