Matukar Gwamna Ya Dauki Gyaran Matsalar Tsaro Ba Tashi Ba Ce Harkar Ba Za Ta Gyaru Ba-----Ibrahim Liman

Matukar Gwamna Ya Dauki Gyaran Matsalar Tsaro Ba Tashi Ba Ce Harkar Ba Za Ta Gyaru Ba-----Ibrahim Liman
 
Dan takarar Gwamna a jam'iyar ADP a Sakkwato Ibrahim Muhammad Liman Sifawa ya fadi yanda za a magance matsalar tsaro a jihohin Nijeriya in dai har da gaske ake yi kan matsalar dole ne gwamna ya dauki harkar tsaro tasa ce ba gwamnatin tarayya ba.
Ibrahim Liman a muhawarar 'yan takarar gwamnan Sakkwato da gidan Rediyon VOA ya shirya aka gudanar a cikin jami'ar Usman Danfodiyo dake Sakkwato ya ce wai sai ka ji gwamna ya fadi harkar tsaro ba ta sa ba ce bayan kuma shi ne shugaban tsaro a jiha.
Ya ce harkar tsaro bayan gwamna ya aminta aikinsa ne ya samar da tsaro aka ji tsoron Allah ya rike amana kan gudanar mulki hakan zai sa a magance matsalar tsaro in da ake fama da su.
Liman in ya samu dama ya ce zai yi aiki da dubaru na kwarewa domin magance matsalar tsaro a jihar Sakkwato.