MATACCEN ALƘAWARI: Labarin Tausayi Mai Cike Da Jan Hankali

MATACCEN ALƘAWARI: Labarin Tausayi Mai Cike Da Jan Hankali

MATACCEN ALƘAWARI:

Rukayya Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar)

(Labarin da ya yi nasarar shiga cikin jerin labarai 25 da BBC suka tantance a gasar Hikayata 2021)

A hankali na buɗe idanuna wanda nake jin fatarsa tai mini nauyi, na sauke shi a saman rufin ɗakin da ya zamto shamaki tsakanina da ganin sararin samaniya.
 Na yunƙura da ƙyar da niyyar tashi, wani masifaffen zogin ciwo ya mamaye ni.
"Ahhh!" Na saki ƙara mai ƙarfi, amma murya a dashe. 
Marata ke mugun ciwo kamar kayan cikina za su fito waje, dole ta sanya ni komawa na kwanta. Shafa gaban goshina na yi na ji yanda gurin ya yi wani irin ƙololo.
"Ki bi a hankali in sha Allah za ki warware kamar komai bai faru ba." Na ji muryar wata likita maƙwabciyarmu ta faɗa. Da alama Mamana ce ta kira ta har gida don duba lafiyata.
Wani azababben raɗaɗi ya mamaye dukkan ilahirin jikina da zuciyata ”Ba ka yi mini adalci ba Iliya, ka cutar da ni ka manta cewa kai ma ilimin nan zai maka rana a gaba.” Na furta cikin raunanniyar murya.
Jingina bayana na yi a jikin bangon ɗakin ina jimami haɗe da tunani 'anya a duniya za a samu wanda ya yi wa alƙawari riƙon sakainar kashi kamar Iliya kuwa?'
Nan da nan majigin ƙwaƙwalwata ya fara hasko mini abubuwan da suka faru a baya.
A ranar litinin da misalin ƙarfe takwas na safe na yi shirina tsaf domin fita jami'a kamar yanda na saba, mijina yana zaune a falo dubansa na yi na ce “Na shirya zan tafi makaranta.’’ Da murmushi a fuskata na yi zancen.
A maimakon Iliya ya mayar mini da amsa cikin murmushi kamar yanda ya saba kawai sai ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya ce ‘’Yau dai ba inda zaki jikar biro da takarda.’’ Cikin kaɗuwa da razana na kalle shi, ina shirin motsa harshena da ya yi mini nauyi, ya tare ni da cewa,
 ‘’ƙwarai kuwa na riga na yanke hukunci daga yau kin gama yawon jami'a, dama can hanyar lalaci ce da iskancin banza, in ba haka ba me zai kai mace cuɗanya a cikin maza? Banda sakarci irin namu me 'ya mace zata iya bayan aikin gida? Karatun 'ya mace a wajena tamkar watsa wa tafki gishiri ne ya ta fi a banza girman ƙashi babu tsoka."
Abin mamaki agwagwa da ƙin ruwa.
Tamkar mutum-mutumi na ƙame ina yi masa duban mamaki don maganarsa ta kaɗar da ni. Tamkar rediyo haka ya cigaba da zazzaga mini kwandon rashin arziƙi ya shiga ya fita ya jefo mini manya-manyan baƙaƙen maganganun da suka tilasta tunzirar mini da zuciya na katse shi da tunin alƙawarin da ya yi kafin a yi baikonmu "Iliya har ka manta da alƙawarin da ka ɗaukarwa mahaifiyata kan cewa zaka bar ni na ci gaba da karatu? Shi fa alƙawari kaya ne dakonsa ake.’’ Kamar kububuwa ya ta so mini fiye da ɗazu.
"Na yi kuskure a baya da na yarda da wannan alƙawarin sai yanzu na fahimci cewa an ninke ni ne a baibai, don haka na saka gatari na yi fata-fata da banzan alƙawarin!. Ya sauke ya na huci.
Nan take na ji wani irin tuƙuƙi ya turniƙe zuciyata ban san lokacin da na mayar masa da amsa ba. "Idan har kai baka san muhimmancin alƙawari ba ni nasan muhimmanci da darajar ilimi domin kuwa ilimi shi ne gishirin zaman duniya."
"Madallah da sarauniyar masana ta duniya, da alama huɗubar wahalallen tunaninki ya yi nasarar makantar da idonki, to, idan har ni ne mijinki ban yarda ki taka ko da ƙofar gida ba, da sunan karatu, idan kuma kin ƙi ji bakya ƙi gani ba."
Daga haka ya fice daga gidan ya bar ni nan cikin tsananin mamaki.
Zama na yi kan kujera ina tunanin mafita. Abun ya zame mini gaba kura baya sayaki.
  Can kuma na tuna da irin wahalar da mahaifiyata ta yi akan tafarkin nema mini ilimi tun ina ƙanƙanuwata. Ta ƙallafa duk wani burinta da fatanta a kaina, ta sadaukar da duk wani abu da yake mallakinta domin ta tallafawa burina. Akan hakan na ɗaukar mata alƙawarin zan jajirce domin na tabbatarwa da duniya cewar mata ma su na da ƙwaƙwalwar da za su ɗauki ilimin da zai taimaki al'umma.

Ina son in gamsar da masu hasashe irin na mahaifina mace ma zata iya, ba kamar yanda suke tsammani ba.

Ga shi mijina yana ƙoƙarin yi mini katangar ƙarfe tsakanina da burina da nake mafarkin cimma a kullum.

"Yanzu Basma haka zaki zura ido a lalata miki burin da kuka yi shekara da shekaru ku na rainonsa ke da mahaifiyarki da rana tsaka? Ai aure ba hauka ba ne." Wani ɓangare na zuciyata ya tuna mini.

Zumbur na miƙe saboda tunawa da na yi cewa ranar ne zamu yi jarabawar ƙarshe a zango na biyu matakin aji na uku a jami'ar.

Gama tuna hakan ke da wuya na miƙe tare da fita, na riga na ƙeƙashe ido akan cewa sai na tafi makaranta a yau idan ya so in na dawo komai ta fanjama fanjam, na sani za a mana sulhu daga baya.

Agogon da ke manne a bangon ɗakin na kalla “kai! haka lokaci ya tafi?.’’ na furta da mamaki.
 Ba don ina saka ran za a bar ni na zana jarabawar ba, na nufi makarantar, zuciyata cunkushe da tunanin abinda zai je ya dawo.

Can bayan kamar awa biyu na nufo hanyar gida zuciyata na tsananta bugu, wannan fa shi ne an ɓata goma ɗaya bata gyaru ba, domin mijina ya riga ya jaza mini makarar da na yi asarar jarabawata.
Gabana sai dukan tara-tara yake yi da na tuna cewa na fito ne ba da izininsa ba.
‘’Assalamu alaikum wa…..’’
Sallamar ce ta maƙale a can ƙasan maƙoshina saboda abunda idona ya ci karo da shi a tsakar gidan ya matuƙar gigita ni.
Iliya ne tsaye riƙe da kwalin dukkan wasu takarduna masu muhimmanci da suka shafi boko ya cinna musu wuta, yana kallon yanda suke ƙonewa sai dariya ya ke. Wahalallen kuka ya kufce mini.
"Ƙarshen Alewa ƙasa, yau zan ga ƙarshen ƙaryar boko a gidan nan, Basma ba dai kin raina ni ba? To, yanzu sai na ga yanda za a ci gaba da karatun." Ya faɗa fuskarsa ɗauke da annuri yana dariyar Mugunta.
A take ganina ya disashe na tafi luu zan faɗi, sai na yi sa'a bangon gidan ya tarbe ni.
Babban burina  bai wuce hasken ilimin da na samu a rayuwa ya haskaka rayuwar mahaifiyata da ta jure dukkannin gwagwarmaya da nau'ikan cin zarafin da mahaifina yake mata don kawai na zo wannan matakin ba.
"Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un!, Yanzu me zan faɗa wa mahaifiyata da ta sadaukar da igiyar aurenta a dalilin waɗannan takardun?." Na faɗa muryata na rawa.
Sai a lokacin ya lura da wanzuwata a gurin don haka ya ƙyalkyale da dariya ya ce, "ke kika san me zaki faɗa wa iyalan masu watsa wa kare ciyawa ."
"Ya isa haka Iliya! komai zaka faɗa ya ƙare a kaina amma ba zan lamunci cin zarafin mahaifiyata ba." Na faɗa cikin ɗaga murya.
Takardun da suka jima da zama toka ya taka ya wuce ɗaki. Jim kaɗan sai ga shi ya fito da dorina mai baki biyu ya hau jibgata ba ji ba gani, garin tsalle-tsalle na ƙuma kaina a bango, ba ko tausayi ya ci gaba da jibgata ina ihu. Sai da ya mini lilis sannan ya jefa mini wata takardar a jikina. Ya kulle ƙofofin ɗakunan gidan duka ya tsallake ni, ya fice abinsa. Tabbas na ji lokacin da wani damshi ya fara bin cinyoyina sai dai kafin na tantance menene hankalina ya yi bankwana da ƙwaƙwalwata.
Tun da ga lokacin ban san me ya kuma faruwa ba sai yanzu da na buɗe idona na ganni a ɗakin mahaifiyata. A nan na fahimci wannan takardar ta saki ce.
 Ina nan zaune cikin jimami sai ga Mamana ta shigo ɗakin tana faɗar "Yau zai ga hauka da naɗe-naɗe, domin Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ce zata raba mu, abun ya yi yawa shege da hauka. Haba! Ga mari ga tsinka jaka?"
Kallona ta yi ta ce "Ƙaramin cikin da ke jikinki ya zube, amma ki kwantar da hankalinki, in dai ni ce Mahaifiyarki sai na tabbatar da na sama miki adalci. Na gode Allah ma da ya saka Suhaima ta je gidan kan lokaci da sai dai mu ji mummunan labari."
Ni dai jinta kawai nake ta ya zan samu nutsuwar ruhi bayan tarin ƙalubalen da na fuskanta a rayuwa? 
"Tabbas wannan shi ne mafi ƙololuwar zalunci da na fuskanta a duniyata, ka tauye mini haƙƙina Iliya." Na faɗa tare da rufe idona ina jin yanda zuciyata ke mini zafi.

Bayan wani ɗan lokaci jikina ya yi kyau sosai, Mamana ta cika alƙawarinta. Tuni Iliya ya shiga komar hukuma har ma ya girbi irin da ya shuka.
Daga ƙarshe hukumar ta tsaya mun kai-da-fata domin dawo da ni a duniyar bil'adama masu 'yanci, har ma na ci gaba da yaƙin neman tabbatuwar dadaɗɗen Burina.

Ƙarshe!