HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Shida
HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 16
Ina nan kwance na kasa gane abin da zai fissheni Safiya tai sallama ta shigo ta iske ni a yanayin tana sanye da kayana da Abban Haidar ya bata, ta zauna ta dubeni tace, "Jiddah wai ke don Allah wace irin mace ce wadda bata san ciwon kanta ba? Ke ace komai naki a sake ba wani tsauri kamar ba mace ba. Yanzu don Allah ji yadda kika kwashi kuɗi kika ba shi yaje yana bin matan banza ƙauye -ƙauye ke kina nan zaune sake da baki cikin gida ke wai dole mai neman aljannah ko? To wallahi bari ki ji Deeni kullum sai ya zage ki gabana, bai da wadda yake tsina yake aibantawa idan ba ke ba... Yau dai ya kamata na nuna wa Safiya riƙon Iyami ce ni, tashin Lagos don haka na tashi zaune na dube ta sosai nace, "Anya kuwa Safiya akwai Jakka, daƙiƙiyar da na taɓa cin karo da ita kaf tarihin rayuwata? Ni wallahi da farko na ɗauka don kina auren tsoho yasa kika liƙewa yaro amma yanzu na fahimci tsabar iya karuwanci ne da neman kuɗi ta kowace hanyar yasa kike biye da Deeni, sai dai ina so daga rana irin ta Yau kada ki sake zuwa inda nake, wallahi kika sake zuwa gidana sai na rufe gidan nayi maki tsinannen duka. Wai ke a tunaninki tsoronki nake ji da na ƙyale ki kina min akuyanci ban ɗauki mataki ba? To kar da ki yi ma kanki karatun banza ni da kike gani na iya dubun alheri kamar yadda na iya duban rashin mutunci don haka babu sauran ƙawance a tsakaninmu sai dai ki tsaya a matsayin karuwar mijina maciya amana wadda ta ƙware da cin mutuncin abota. Cike da fusatar zuciya da jin takaicin kayana da Deeni ya kwashe yasa na sake daka mata tsawa, nace "Safiya daga Yau sai Yau babu ni babu ke idan kika sake tabbas nice zan datse maki igiyar auren da kike wahal wa a banza. Na nuna mata ƙofa maza ki bar min gida karuwar mijina karuwar yaran gari mai iskancin Naira ɗari da dubu guda."
Tsabar mamaki da tsoro suka sa Safiya kasa miƙewa tsaye sai da taga na zabura zan miƙe tsaye na afka mata da duka ta kwasa tai waje ta bar takalmanta da jakarta a ɗakina.
Bayan fitar ta gidan na dinga jin azabar tafasar zuciya ji nake me yasa ban lallasa ta ba ta daku tai tubus ba? Me yasa ban rufe gidan ba na cicci mata mutunci ba? Me yasa wai na tsaya gaya mata magana madadin duka? Amma ba komai duk ranar da ta sake dawowa gidan nan sai na koya mata hankali.
Har dare ban sake jin motsin Abban Haidar ba har na kwanta, zuciyata nata min ciwo kaina nata ciwo kamar zai tsage.
Can ya shigo ina jin shi yai min tsaye kan kaina, nai shiru ban motsa ba, haka ban da alamar motsawa saboda Yau ji nake ina daidai da aikata komai nayi daidai a guna,amma ina tuna faɗan Mama sai jikina ya yi sanyi na kasa samun natsuwa da aikata mai rashin kunya don haka na yi kamar barci nake kawai.
Washegari ya dube ni da zai fita yana cika yana batsewa, "To mai kuɗi na fara sana'ar saida kayan hatsi na abinci don haka sai ki sakar min mara inyi fitsari , kar da ki ɗauka wata tsiya nayi da kuɗin." Ya fice ya barni ina binsa da kallon mamaki. Amma har ga Allah naji daɗin yadda ya kama sana'a idan har da gaske yake kenan tabbas zan farin ciki da hakan, domin na tsani zaman da yake ba sana'a ba aiki tunda ya aje aikinsa a cewarsa wahala ake sha ya dawo zaman gida da bin ƙauyuka gun matan ƙauye.
Cikin sati guda da fara sana'ar Abban Haidar komi ya fara min daɗi don yana ban abinci sau guda a rana nayi har dare sai da safe ne dai sai yaga dama yake ban kuɗin kalaci, hakan na damuna domin Haidar akwai shan nono ko da yaushe don haka nan da nan nayi rama na koma kamar an zana one.
Ɓangaren zamana da Abban Haidar kuwa ba a cewa komai domin ba daɗi ba rashin daɗi, tsakanina da shi idone kawai ba ruwansa da maganar sabulun wanki ko wanka balle kuɗin mota ko mashin idan tafiyar hakan ta kamani .
Amma maganar bin matansa bai daina ba sai dai idan bai ga dama ba, duk lokacin da abin ya motsa zai ce na shirya na je gun Mama ko can gidansu ko gidansu Babana na yini sai dare na dawo.
Har zuwa yanzu ban saka Babana a idona ba tun abin na damuna har ya daina damuna na saka a raina zan rayu ko babu shi.
Muna ta rayu da daɗi ba daɗi har na yaye Haidar a lokacin ne ƴan matan Fulani suka cinye jarin Abban Haidar tas, don wadda ya gani zai ce yana so, su kuma dama sana'ar fura su ke don haka sai su ce ya basu gero da masara ko dawa, a haka dai har jarin ya ƙare tas ya koma babu komai na sana'ar.
Amma a hakan ma yasha cemin, "Wallahi duk ranar da kika aika na baki cefane ji nake baƙin ciki tamkar ya kashe Ni, ban jin takaici sai naga na fitar da Naira biyar da sunan ke za ki amfana wallahi kamar in mutu haka nake ji don takaici, Ni dai idan yana surutunsa ban kula shi sam, ya gama faɗansa ya haƙura ban tankawa Ni dai.
A hakan watarana na je gun Mama na wuni ya je da dare don mu tafi tare yace na amshi wayar Mama mun haska wayar shi babu caji. Na koma na amso wayar Mama muka tafi muna zuwa na ɗauka zai ban wayar sai naga ya fice da ita, washegari ma bai ban wayar ba ina so nayi ma shi magana kuma ina tsoron yace don tana ta Mamana yasa nace ya ban, sai nayi shiru na bar maganar duk da abin na damuna.
Bayan sati da amsar wayar sai na daina ganinta wajen shi, ga shi ina son ya ban wayarta na kai mata amma na rasa yadda zan yi har ma ga shi ya daina ganinta alamar ya salwantar da ita.
Ina zaune ina tunanin yadda zan na amshi wayar na shiga ɗaki kamar ance na duba akwatin kayan Abban Haidar sai ga batir ɗin wayar da layin wayar (Sim card) na ɗauka na riƙe ina jiran ya dawo na mai magana Yau dai ya ban wayar tun da naga batir da sim card ɗin.
Sai kuma akai rashin sa'ar har barci ya kwashe ni babu Abban Haidar ba labarinsa sai da safe ne zai fita na shiga bayan na gaida shi nace, "Abban Haidar ina wayar Mama zan kai mata ga dai sim card ɗin da batir ɗin na gani na ɗaukar mata."
Kamar saukar aradu haka naji Abban Haidar yace, "Don Ubanki ban batir ɗin!
Ya Salam! Zagi kuma ? Abin da zuciyata tace kenan ban san ya akai ba na dube shi nace, "Ban badawa don Uban daya haifi Uban Uwarka! Fau ya kawo min mari na kuwa duƙe ya mari iska.
Cikin ɓacin rai da takaici na ɗago cike da masifa nace, "Wallahi ba zan yi auren zagi da duka ba, Yau ko Ni ko kai a cikin gidan nan, daga kawai nace kaban wayar mahaifiyata sai zagi ? To Ubanka ka zaga ba nawa ba... Kawai ya nufo Ni da zummar rufe Ni da duka.
Na ɗaga mai hannu nace "Idan faɗan ka ke ji bari na zo." Cikin sauri na ɗauki dogon wando na saka na cire zanina na je na rufe gidan na saka sakata na iske shi tsaye ɗakin yana huci.
Saukar mari naji kan kumatuna, ban ƙasa a gwiwa ba nima na fidda hannu na wanke fuskarsa da mari ban bari ya dawo hayyacinsa ba na sake marinsa a ɗayan kumatun.
Nan da nan kokowa ta kaure tsakanina da Deeni, tun muna yi cikin ɗaki har muka fito waje.
Nasan da Deeni ya tabbatar da cewa zai sha wahala gareni babu abin da zai sa shi haye mun, amma ganin ina mai kawaici ina kauda kai daga duk abin da yake min yasa yake ganin zan iya jure zagi da dukansa.
Cikin ikon Allah na kama shi na shaƙe gam, na ga hakan bai min ba na wawure shi na maka da ƙasa na haye ruwan cikinsa na dinga jibgarsa tamkar filin dambe.
Ko da Deeni ya fahimci cewar bai cin komai kaina sai wahalar banza kuma sai jibgarsa nake sai kawai ya kama katanga ya haye nufinsa ya dire waje tunda katangar bata da girma.
Raina a ɓace yake daman ban iya faɗa ba don haka na sake wawuro shi na yarɓo shi ƙasa ya fasa uwar ƙara yana kiran za ki kashe Ni, wai ke baki da imani ne?"
Ban san ya akai ba naga makwabtana na leƙen katangar gidan suna ganin yadda Deeni ke kuka yana neman na ƙyale shi ya gaji da faɗan amma Ni ji nake tamkar yanzu aka soma faɗan, duk sanda na tuna zagin nan sai naji tamkar na cinye shi ɗanye.
Sai da wata dattijuwa ta leƙo ta katanga tace, "Ke Jiddah idan baki ƙyale shi haka nan ba sai na ɓata maki rai."
Jin furucin tsohuwar yasa na ƙyale Deeni dake ta maida numfashi alamar yana jin jiki.
Zuwa nayi na buɗe gidan mijin Binta ya shigo da wasu suka cicciɓe shi suka fice naji suna cewa gidansu za su kai shi gun Mamarsa, naga to zaman me zan yi cikin gidan? Sai kawai na ɗauki yarona na goye na bi bayansu mutane nata kallona.
To masu karatu ku biyo Haupha don jin ya za a kaya ga dai Jiddah ta baje Deeni an tafi kai shi gidansu ta kuma bi su.
Taku a kullum Haupha!!!
managarciya