Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Matar Ƙanen Sanata Babba Kaita A Katsina
Wasu da ake kyautata zaton yan ta’addan daji ne sun ziyarci karamar hukumar Kankia a jahar Katsina dake Arewa Maso Yammacin Najeriya inda suka shiga gidan wani mutum mai suna Mani Babba Kaita wanda ya kasance kane ne ga Sanata Ahmed Babba Kaita suka dauki matarshi uwar gida mai suna Jamila suka tafi da ita.
Majiyar Jakadiya ta ruwaito cewa, yan ta’addan sun je gidan da ke wata unguwa da ake kira bakin kasuwa a jiya Lahadi da misalin karfe 12 da wani abu na dare.
Bayan sun sanya diga sun fasa bangon gidan sun shiga sun nemi Jamila da ta bude dakin ita kuma ta ki budewa, to anan take suka sanya bindiga suka harbe kubar kyauren dakin ya bude suka shiga suka fito da ita.
Tun da farko dai a lokacin da suka isa gidan suna kokarin yadda za su shiga shi kuma mijin dama bai dade da dawo wa gida ba sai ya ji alamun ana taba kyaure, nan take ya nufo bakin get din inda ya ji maganganunsu suna cewa da yayi gardama kawai a kashe shi.
Jin wannan furuci na yan ta’addan ke da wuya shi kuma sai ya juya ya nufi wani wuri daga karshen bangon gida ya samu ya haura katanga ya dira wani gida da ke makotaka da gidan nashi.
Hakazalika, an ce bayan Daukar matar kanen Sanatan sun kuma hada da wasu mutum biyu da ke makotaka da su sun tafi.
Unguwar Bakin Kasuwa dai na cikin garin na Kankia kuma an ce akwai jami’an tsaro a kusa da wurin da yan ta’addan suka je sai dai babu wata hubbasa daga gare su.
Sanata Babba Kaita a yanzu haka, shine Sanata mai ci kuma mai wakilintar shiyyar Daura mahaifar shugaba Buhari inda a da ya ke a Jam’iyyar APC kafin daga baya ya koma Jam’iyyar PDP kuma ya ke zaman dan takarar Sanatan jam’iyyar a zaben 2023.
managarciya