Jihohin  20 Da APC Na Iya Shan Kaye A Zaben 2023 Saboda Rikicin Cikin Gida

Jihohin  20 Da APC Na Iya Shan Kaye A Zaben 2023 Saboda Rikicin Cikin Gida

 

Idan har ikirarin shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, cewa rikicin cikin gida ne ya jawo musu faɗuwa a zaɓen Osun, kuma ya kasance Mai ɗorewa, APC na fuskantar faruwar irin haka a jihohi 20 na tarayyar Nijeriya. 

Jaridar Vanguard ta kalato cewa Mafi yawan rassan jam'iyyar APC na jihohi sun shiga cikin rikici sakamakon saɓani ko kuma wani abu da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani. 
Binciken da aka gudanar a dukkan sassan ƙasar nan ya nuna cewa duk da kiran da shugaban ƙasa Buhari ya yi ga mambobin APC cewa kowa ya maida wuƙar shi kube, wasu da suka fusata basu ɗauki lamarin da sauki ba don suna ci gaba da yin gaban kansu.
Yayin da wasu suka ɗauki matakin sauya jam'iyya, inda wasu suka koma PDP, wssu kuma suna nan daram a APC amma za su iya komawa gefe su yaki jam'iyyar kamar yadda ta faru a jihar Osun. 
Legit.ng Hausa ta haɗa muku jerin sunayen jihohin da APC ke fama da rikicin cikin gida, wanda idan abun da ya faru a Osun ya cigaba, jam'iyyar na fuskantar bazanar faɗuwa.
Jihohin sun haɗa da, Legas, Ondo, Eikiti, Ogun, Oyo, Abiya, Kano, Kaduna, Kebbi, Akwa Ibom, Ribas, Nasarawa, da jihar Benuwai. 
Sauran jihohin su ne; Ebonyi, Kwara, Imo, Kuros Riba, Bauchi, Zamfara da kuma jihar Gombe. 
Jam'iyyar APC na fuskantar yaƙi mai zafi yayin da babban zaɓen 2023 ke tafe. 
Bincike ya nuna matukar ba'a shawo kan mambobin da suka fusata ba, jam'iyyar ka iya faɗuwa a zaɓe, ganin yanda lamurra ke tafiya ba cikin shiri da kimtsi ba .