Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Shugaban Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa Farfesa Mahmood Yakubu
Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Shugaban Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa Farfesa Mahmood Yakubu.
Daga : Janaidu Amadu Doro.
Rahotanni dai sun bayyana cewar sun gayyaceshi ne kan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da za6en fidda gwani na jam’iyyun siyasa.
Hakan ya biyo bayan da dan majalisa mai wakiltar maza6ar Yagba East/Yagba West/Mopa-Muro na jihar Kogi, Rep. Leke Abejide ya gabatar da kudirin gaggawa ga jama’a a yauAlhamis a Abuja yayin zaman majalisar.
Farfesa Yakubu zai gurfana a gaban kwamitocin kasafin kudi da harkokin za6e domin yin magana kan lamarin.
A cikin kudirin, Abejide ya ja hankali kan rade-radin da ake yi na cewa za a kashe sama da Naira biliyan 500 ga jam’iyyun siyasa domin gudanar da za6en fidda gwani kai tsaye gabanin babban za6en 2023.
Kudin da za a kashe dai zai iya kawo ce ce-ku ce kan makomar dokar za6e ta shekarar 2021 da har yanzu ke gaban shugaba Buhari.
Kudirin dai ya dauki za6en fidda gwani kai tsaye a matsayin tsarin za6en ‘yan takarar jam’iyyun siyasa don za6en gaba.
Ya yi nuni da cewa INEC ce ta fi dacewa ta fadi komai kan kudin da za a kashe a za6en fidda gwanin kai tsaye tunda ita ce alkaliyar da ke kula da za6ukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa da na manyan za6uka.
managarciya