Gwamnatin Sakkwato ta bayar da aikin hanya sama da biliyan 8 a mazabar Sani Yakubu

Gwamnatin Sakkwato ta bayar da aikin hanya  sama da biliyan 8 a mazabar Sani Yakubu

Gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ta bayar da kwangilar sake gina hanyar mota daga ƙaramar hukumar Tangaza zuwa ƙaramar hukumar Gudu mazaɓar ɗan majalisar waƙillai Honarabul Sani Yakubu, kwanaki kaɗan bayan ya ƙalubalanci salon Mulkin gwamna da yake ganin yana tafiya daban da ra'ayin talaka.
Majalisar zartarwa ta jiha a ranar Laraba ta amince da a shimfiɗa titin mota da zai haɗa ƙananan hukumomin biyu kan kuɗi sama da  Naira biliyan takwas da miliyan 900.
Kwamishinan yada labarai na jiha Sambo Bello Danchadi ne ya yiwa manema labarai bayani ya ce za a kammala aikin ne cikin wata shida, kamfanin 'Road Nigeria' ne aka baiwa aikin tare da ba su kaso 30 cikin 100 na kuɗi kamar yadda doka ta tanadar.
Sukar da ɗan majalissar ya yi wanda shi ma ɗan jam'iyyar APC ne ta yi amfani ganin a yanzu gwamnati ta waiwayo mutanensa duk da shi matsalar tsaron da yanki ke fama da shi ne yafi bukatar gwamnatin jiha ta dauka da muhimmanci fiye da aikin more rayuwa, kamar yadda yake ta fada a cikin kalamansa.
Hanyar mai tsawon kilomita 36 tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ne ya samar da ita a lokacin mulkinsa, za a sake gyara ta ne bayan da ruwa suka kwashe wani yanki nata. Hanyar tana cikin aiyukka mafi tsada da wannan gwamnatin ta bayar a cikin wannan lokaci na matsin tattalin arziki.