Layin wutar lantarki na ƙasa ya sake sauka karo na biyu a kasa da sa'o'i 24 

Layin wutar lantarki na ƙasa ya sake sauka karo na biyu a kasa da sa'o'i 24 

Saukar Latin ta afku ne da misalin karfe 9:17 na safiyar yau Talata, lamarin da ya jefa sassan kasar da dama cikin wani yanayi na katsewar wutar lantarki.

Da ya ke tabbatar da saukar layin, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Eko (EKEDC), a wani sakon da ya wallafa ta hanyar X ya ce: “Mu na sanar da ku cewa an samu saukar layin da karfe 09:17 na safe, wanda ya yi sanadin asarar wutar lantarki a fadin hanyar sadarwar mu. .

“A halin yanzu muna aiki tare da abokan aikinmu kamar yadda muke fatan sake dawo da layin da gaggawa.  Za mu sanar da ku da zarar an dawo da wutar lantarki.”

Wannan shine karo na biyu da layin ya sauka cikin cikin kasa da sa'o'i 24.