Bayan watanni 15 Gwamnatin Kebbi Ta  Inganta Lafiyar Yaron Da Uwayensa Suka Daure Shi A Cikin Dabbobi

Bayan watanni 15 Gwamnatin Kebbi Ta  Inganta Lafiyar Yaron Da Uwayensa Suka Daure Shi A Cikin Dabbobi
 

 

Gwamnatin Kebbi karkashin jagorancin Sanata Atiku Bagudu ta yi  kokarin inganta lafiyar  Jibril Aliyu, yaron da aka gano iyayen shi sun daure shi a cikin dabbobi a tsawon lokaci abin da ya haifar masa da cutar kwakwalwa har yake cin kashinsa dana dabbobi. 

Yaron mai shekara 12 an samu bayaninsa ne tun a watan Augustan shekarar 2020 a Unguwar  Badariya dake birnin kebbi in da kungiyar lauyoyi mata da wasu na sa-kai suka shiga lamarin.

Gwamnati ta shiga lamarin inda ta mika yaron  ga shugaban Asibitin tunawa da Sarki Yahaya dake birnin Kebbi watau Dakta Yahaya Aliyu Bunza tare da mataimakansa 20 domin ceto rayuwar yaron.
 
Yaron a gano shi ne a ranar 9/08/2020 aka mika shi ga ma'aikatan kiwon lafiya ranar 10/08/2020 kana suka dawo dashi ranar Talata 7/12/2021 watau yayi wata 15 a hannun ma'aikatan kiwon lafiya kenan. 
Daya cikin kungiyoyin sa-kai da suka taimaki yaron kafin gwamnati ta shiga lamarin wakilimnu ya tuntube ta kan wannan cigaban da aka samu ta ce "ba zan ce komai ba kan lamarin yaron domin an hana mu yi magana kan abin da ya shafi yaron,"in ji ta.
Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya ce bayan samun saukin yaron gwamnati ta dauki matakan cigaba da kulawa da lafiyar yaron bayan gina masa gida shi da uwayensa da ba shi tallafin karatu.