Kwamitin Mutum 19: Fargaba Ta Kama Mukaraban Tsohuwar Gwamnatin Tambuwal

Kwamitin Mutum 19: Fargaba Ta Kama Mukaraban Tsohuwar Gwamnatin Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sakkwato ya aminta da kafa kwamitin mutane 19 domin sake duba gwanjon kayan gwamnati da tsohuwar gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta aiwatar, domin ana zargin akwai wadan da aka yi ba bisa ka'ida ba.
Gwamnan ya daurawa kwamitin alhakin duba dukkan gwanjon kayan gwamnati da tsohuwar gwamnatin Tambuwal ta aiwatar wanda yake ba bisa ka'ida ba an yi ne domin gadara da kusanci.
Kwamitin na karkashin jagorancin Alhaji Jelani Kalgo a matsayin shugaba, sai Mustapha Alkali zai zama Sakatare.
Sauran mambobin sun hada da Col. Garba Moyi, Hon. Isah Sadik Achida, Dalhatu Sidi Mamman, Alhaji Harande Mahe, Hon. Nasiru Shehu Bodinga, Alhaji Mu'azu Suleiman, Alhaji  Sanusi Danfulani, Alhaji  Ibrahim Hassan, Alhaji Isah Mai Shinkafa,  Alhaji  Nasiru Manjo da Abubakar Salame.
Sauran su ne wakili daga ma'aikatar aiyukka da ta kananan hukumomin jiha, da wakili a hukumar Safiyo ta jiha, da wakili a hukumar 'yan sandan jiha, da wakili a hukumar rundunar tsaro waton DSS da cibil difens.
An zargi Tambuwal da yiwa kansa gwanjon motocin alfarma da  ya yiwa kwamishinoninsa da kantomomin kananan hukumomi 23 gwanjon motocin hawa.