Kwanan nan za mu sakar wa kamfanonin jiragen sama na waje dala miliyan 464 da su ka maƙale -- Gwamnati
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokarin ganin an gaggauta sakin dala miliyan 464 na kamfanonin jiragen sama na kasashen waje da suka makale a kasar.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa babban bankin ƙasa, CBN ne ya daƙile sakin kuɗaɗen shiga daga siyar da tikitin da aka tara tun daga shekarar 2021 har zuwa watan Yulin 2022, ta hannun kungiyar sufurin jiragen sama ta kasa da kasa, IATA.
A ranar Alhamis ne daya daga cikin kamfanonin jiragen saman, Emirates Airlines, ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragensa a Najeriya daga ranar 1 ga watan Satumba, saboda rashin iya dawo da kudadensa daga kasar.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a jiya Litinin, yayin ziyarar da ya kai a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, ministan ya bayyana cewa kungiyoyin da abin ya shafa na kokarin ganin an shawo kan lamarin.
"A kan kudaden da su ka maƙale, zan iya gaya muku cewa hukumomin da suka dace suna aiki tukuru a kan wannan batu," in ji shi.
managarciya