Zanyi duk mai yiwuwa  wajen yaki da shan kwaya a Nijeriya– Aisha Buhari

Zanyi duk mai yiwuwa  wajen yaki da shan kwaya a Nijeriya– Aisha Buhari

 

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

 

Uwargidan shugaban Nijeriya Hajiya Aisha Buhari ta ce sai inda karfinta ya kare wajen yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa maza da mata a da ke fadin kasar nan.

 
Hajiya Aisha Buhari ta yi wannan fadakarwa a taron kan yaki da shan kwaya na shekarar 2022, Aisha Buhari ta bukaci masu ruwa da tsaki da su hada hannu waje daya  domin ganin an yi wa tufkar hanci a duk fadin kasar.
 
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa uwargidan shugaban kasar ta fuskar watsa labarai Sani Zoro ya rabawa manema labarai a Abuja ta bukaci masu sarautun gargajiya da su ci gaba da ba da irin gudunmuwar da suka saba bayarwa wajen ganin matsalar ta kau a tsakanin matasa.