Tambuwal Zai Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2022 A Ranar Litinin

Tambuwal Zai Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2022 A Ranar Litinin
Tambuwal Zai Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2022 A Ranar Litinin
 
Majalisar Dokokin jihar Sakkwato ta amince gwamna Aminu waziri Tambuwal ya zo ranar Litinin 15 ga Nuwamba domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2022.
A zaman majalisa wanda mataimakin shugaban majalisa Abubakar Magaji ya jagoranta sun amince gwamna da mukarabansa su zo majalisar domin gabatar da kasafin.
Jagoran 'yan majalisar APC a majalisa Honarabul Bello Isah Ambarura dake wakiltar karamar hukumar Illela ya gabatar da kudiri a gaban majalisa na jingine dokar hana zaman majalisa a ranar Litinin da Jumu'a domin baiwa Gwamna Tambuwal damar shigowa majalisa a ranar Litinin, ya gabatar da kasafin 2022, kuma ya yi kira ga 'yan majalisa su zauna a wannan ranar, kai tsaye majalisa ta amince da kudirin, abin da ya baiwa Gwamna da tawagarsa damar su halarci taron yanda yakamata.
Bayan nan majalisa ta dage zamanta har zuwa ranar Litinin domin shedar bukin gabatar da kasafin shekarar 2022.