Yajin-aiki: Rikakkun Farfesoshi da SANs 46 Za Su Kare ASUU a Kyauta a Gaban Kotu

Yajin-aiki: Rikakkun Farfesoshi da SANs 46 Za Su Kare ASUU a Kyauta a Gaban Kotu

 

‘Ya ‘yan kungiyar ASUU wadanda sun kware a harkar shari’a za su kare malaman jami’a a shari’ar da za ayi tsakaninsu da gwamnatin tarayya. Sun ta kawo rahoto cewa malaman jami’a da sun kai mataki da SAN a Najeriya da kuma Farfesoshin shari’a 46 ne za su zama lauyoyin kungiyar ASUU. 

Punch tace wani daga cikin ‘yan majalisar koli na kungiyar ASUU yace za suyi amfani da lauyoyin da suke da su a jami’o’in gwamnatin kasar nan.
Wannan malamin jami’a da bai bari an kama sunansa ba, yace ASUU tana da Farfesoshin shari’a da manyan Lauyoyi na SAN da za su tsaya mata.  
“Shugaban kungiya za iyi wannan jawabi, amma za mu je kotu a yau (Litinin); muna da SAN da Farfesoshi a cikin ‘yan kungiyarmu, za su kare ASUU a kyauta.”