Kotu ta Ɗaure Wani Mutum Kan Ya Tura Bidiyon Tsiraici Ga Matar Aure

Kotu ta Ɗaure Wani Mutum Kan Ya Tura Bidiyon Tsiraici Ga Matar Aure

Kotun Shari'a dake zama a kofar Kudu a jihar Kano ta ɗaure wani bakanike mai suna Yanusa Adamu tsawon wata shidda a gidan gyaran hali bayan ta same shi da laifin tura bidiyon tsiraici(blue fim) a cikin wayar matar aure.
Mai gabatar da Shari'a ya sanar da Alƙali  kotu Isah Rabi'u Kademi Gaya cewa wanda ake zargi ya sanya nambar matar auren ne gurup na watsapp yana tura mata bidiyon tsiraici.
Ya ce mutumin ya samu wayar matar ne a lokacin da ta kai masa keke ɗinkinta domin ya gyara mata.
Abin da mutumin ya yi laifi ne da ya saɓawa kundin dokar jiha waton penal code sashe na 388.