Kungiyar 'Yan Jarida Ta Shawarci Gwamnatin Sokoto  Kan Motocin Sufuri Da Suka Yi Batan Dabo

Kungiyar 'Yan Jarida Ta Shawarci Gwamnatin Sokoto  Kan Motocin Sufuri Da Suka Yi Batan Dabo

Kungiyar yan jarida reshen Jihar sakkwato, ta bukaci Gwamnatin sakkwato da ta fito da motocin da ta Kaddamar  domin sufuri a ciki da wajen sakkwato domin rage radadin tsadar ababen hawa da cire tallafin man fetur ya jawo.

Wannan Kiran yana kunshe ne jawabin bayan taro da kungiyar ta fitar Wanda  Shugaban kungiyar  Abdullahi Safiyar Magori da Sakatarensa Muhammad Nasir Bello suka sanyawa hannu.

Idan za'a iya tunawa, Gwamnan Ahmad Aliyu Sokoto ya kaddamar da motocin sufuri a yayin da yake bukin cika kwana dari a kan karagar mulki, bayan kaddamarwar ba a sake jin duriyar motocin ba sun yi batan dabo, abin da kowa ke tofa albarkacin bakinsa kan motar, amma dai gwamnati ba ta ce komai ba.

Haka zakila, Kungiyar tayi kira da Gwamnatin jihar da ta ƙara himma wajen raba kayan Abinci na Tallafi da ta samar duba da halin da Al'umma ke ciki na matsin tattalin arziki.

Kungiyar NUJ ta jinjinawa Gwamnatin jiha aka kokarinta wurin samar da tsaro kana sun bukaci a matsa kaimi domin kai karshen wannan matsalar.