Akwai 'yan siyasa da kuma iyayen gida wadanda suke da wani irin karfin iko a jihohinsu na juya akalar siyasar jihar tun suna mulki har da yanzu da suka sauka, komai kuwa zafin da siyasar jihar ta dauka.
A Najeriya, wadannan iyayen gidan a siyasa suna da yawa kuma har yanzu ana mutunta su, suna da karfin iko tare da magoya baya masu tarin yawa ko bayan sun bar kujerunsu.
Wadannan kwararrun a siyasa sun kiyaye yadda za a dinga damawa dasu a siyasar Najeriya tun bayan dawowar mulkin damokaradiyya a Najeriya a 1999.
1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Tinubu shi ne babban misali a irin wadannan 'yan siyasan.
Tsohon gwamnan jihar Legas din shi ke jan gaban siyasar jiharsa da ta yankin kudu maso yamma.
Tinubu ya tabbatar da hawa mulkin gwamnoni 3 tun bayan da ya bar kujerar a 2007 kuma lokacin da daya daga cikinsu yayi kokarin bijire masa, Jagaban Borgu ya saka yaransu sun saita masa hanya.
2. Chief James Onanefe Ibori Ibori ba dan siyasa ba ne kamar kowanne iri. Akwai wuya a samu mutum a siyasa wanda zai iya fito na fito da shi a jihar Delta.
Yayin da Tinubu ke da 'yan tawaye, Ibori bashi da wata matsala tun 1999.
3. Emeka Ihedioha Kusan watanni 8 yayi a kujerar gwamnan jihar, amma Ihedioha ya zama babban dan siyasa a Imo. A ziyarar karshe da ya kai jihar Imo, tun daga filin jirgi magoya bayansa suka dinga bin sa har gidansa.
4. Bukola Saraki 'Yan siyasa irinsu Oloye ba kasafai ake samun irinsu ba. Mutum ne da ya gaji mahaifinsa kuma ya daga sunan gidansu.
A shekaru 57 da yake a duniya, ya zama hadimin shugaban kasa, gwamna sau biyu, shugaban zauren gwamnoni, shugaban kwamitin muhalli a majalisar dattawa kuma shugaban majalisar dattawa.
5. Rabiu Kwankwaso Babu dan siyasa mai karfin iko da magoya baya a Arewa kamar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Ana danganta yanayin siyasarsa da ta Malam Aminu Kano.
A duk inda ya shiga, ruwan jajayen huluna ake gani. Babu shakka halayyarsa ta gina kananan 'yan siyasa da tallafawa jama'a ne yasa yake da wadannan mabiyan.
6. Sule Lamido Dan siyasan mai shekaru 72, Sule Lamido yana daga cikin 'yan siyasan dake fadi a ji a jiharsa.
Baya iya jurewa shirme, Lamido ya samu sunansa ne saboda yanayin ayyukansa da salon siyasarsa.
7. Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko dan siyasa ne da yake rike da mukamin siyasa tun bayan dawowar dimukuradiyya a 1999, ana damawa da shi yana da magoya baya a jiharsa ta Sakkwato kuma shi ne jagoran tafiyar siyasarsa da ta yaye dimbin jama'a.
Wamakko dan siyasa ne da yake da magoya baya biye da shi abin da ke kara taimakonsa wajen cigaba da jan ragamar siyasar Sakkwato.