Kotu Ta Ɗaure Abdurrashed Maina Kan Sama Da Faɗi Da Biliyan 2 Na Fansho

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ce ta gabatar da Abdulraheed Maina gaban kuliya domin amsa tuhuma kan zargin da ake masa na badakalar kudade. Tun da farko Alkalin kotun ya baiwa Abdulraheed Maina damar gabatar da hujjoji domin kare kansa, amma mutum daya tak ya gabatar a matsayin hujja, shima ya gaza gamsar da Alkalin akan tulin hujjojin da EFCC suka gabatar suna tuhumar Maina.  Idan ba a manta ba a kwanakin baya wata kotun ta daure dan gidan Abdulraheed Maina wato Faisal Maina akan zarge zargen dake da alaka da cin hanci da rashawa. Kotu ta ɗaure shi shekara 8 kan kama shi dai laifin da ake tuhumarsa.

Kotu Ta Ɗaure Abdurrashed Maina Kan Sama Da Faɗi Da Biliyan 2 Na Fansho
Abdurrashed Maina
Wata babbar kotu a Abuja babban birnin tarayya, ta samu tsohon shugaban hukumar Alkinta Fansho ta kasa Abdulraheed Maina da laifin yin sama da fadi da tsabar kudi Naira Miliyan dari da saba'in da daya.
Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ce ta gabatar da Abdulraheed Maina gaban kuliya domin amsa tuhuma kan zargin da ake masa na badakalar kudade. Tun da farko Alkalin kotun ya baiwa Abdulraheed Maina damar gabatar da hujjoji domin kare kansa, amma mutum daya tak ya gabatar a matsayin hujja, shima ya gaza gamsar da Alkalin akan tulin hujjojin da EFCC suka gabatar suna tuhumar Maina. 
Idan ba a manta ba a kwanakin baya wata kotun ta daure dan gidan Abdulraheed Maina wato Faisal Maina akan zarge zargen dake da alaka da cin hanci da rashawa.
Kotu ta ɗaure shi shekara takwas kan kama shi dai laifin da ake tuhumarsa.
An same shi mallakar wasu kudaɗe da bana gaskiya ba a cikin asusun ajiyar iyalansa.