Na cire Sunan Osinbanjo Da Boss Don Su Mayar Da Hankali Ga Ayukkan Cigaban Kasa---Buhari

Na cire Sunan Osinbanjo Da Boss Don Su Mayar Da Hankali Ga Ayukkan Cigaban Kasa---Buhari

Daga Jabir Ridwan.

Jam'iyar APC Mai Mulki a najeriya ta bayyana cewa shugaba Buhari ne yace a fitarda sunan mataimakinsa farfesa Yemi Osinbanjo da Kuma na sakataren gwamnatin sa Boss Mustafa domin su Kara mayarda hankali ga Ayukkan Cigaban Kasa.

Rahotanni sun karade shafukan sada zumunta na rashin sunan mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbanjo cikin jerin sunayen mambobin kwamitin Yekuwar Zabe da zai soma a kwanaki masu zuwa.

Jaridar Intelregion ta ruwaito cewa sakamakon ganin Babu sunan shugaban kasa a yakin Neman Zabe Dan takarar shugabanci kasa karkashin inuwar jami'iyar APC wato Bola Ahmed tinubu da Dan takarar mataimaki Kashim shettima,  wasu sun alakanta Hakan da rashin nasarar da mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbanjo yayi a zaben fitar da gwani.

Da yake mayarda martani acikin wani bayani karamin ministan kwadago da Samar da ayukkan Yi Festus keyamo Wanda shine Mai magana da yawun Yan takarar shugabanci kasa karkashin inuwar jami'iyar APC yace shugaba Buhari ne yabayarda umurnin cire sunan mataimakinsa ga sha'anin Yekuwar Zabe ta yanda zasu cigaba da mayarda hankali wajen samarwa kasa ayukkan more rayuwa.

Hakama yace wannan kwamitin yakin Neman Zabe ba shine na karshe ba domin akwai yuwar sake bita akanshi tareda sauyashi a wasu kwanaki masu zuwa.