EFCC Ta Kama Wasu Mutane 33 Da Take Zargi Za ZambaTa Intanet A Legas

EFCC Ta Kama Wasu Mutane 33 Da Take Zargi Za ZambaTa Intanet A Legas
Jami’an hukumar EFCC reshen jihar Legas ta kama  wasu mutane talatin da uku da ta ke zargi da zamba ta intanet a jihar Legas.
Wanda ake tuhumar sun hada da: John Oshogbo Ekpo, Samuel Afolabi Micheal, Erezi Sydney, Oghenemaro Ayoola, Nathaniel Joseph, Seye Victor Abolaji, Abdulrasheed Mayowa, Ojo Abiola, Damilola Afolabi, Innocent Alidu, Coker Taiwo, Ajiboye Odunayo, Olamilekan Agbaje, Wasiu Oluwasegun, Olonade Ridwan da Lucky John.
 
Sauran sun hada da Olonade Wasiu, Babatunde Asibojo, Adekunle Nurudeen, Balogun seun, Igwe Ossi, Oruen Daniel, Abiodun Hammed, Tizhe Lucky, Oghenekome Louis, Sodiha Sanya, Damilare Owotutu, Oladipupo Muyideen, Akintunde Olufemi, Afolabi Oluwasanmi, Ibrahim Salisu, John Eze da Asubiodo Jelili.
An kama su ne ranar Laraba 9 ga watan Maris, 2022, a rukunin gidajen Rotimi Williams Farm Estate dake Ogba, jihar Legas biyo bayan bayanan sirri da hukumar EFCC ta samu akan aiyukan dasuke aikatawa na zamba ta intanet.
An kama wasu  motoci goma sha hudu, kwamfiyutoci, da wayoyi a hannun su.