Jam'iyar APC a jihar Sakkwato ta nuna rashin jindadinta ga bashin da Gwamnan jiha Aminu Waziri Tambuwal zai karbo na naira biliyan 28.7 wanda suke ganin hakan ci baya ne.
Shugaban jam'iyar a jihar Alhaji Isah Sadik Achida ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya kira a hidikwatar jam'iyar a birnin jiha ya ce "Wannan matakin na karbo bashin ya mayar da jihar Sakkwato a mataki na biyu a dukkan jihohin Nijeriya cikin wadanda aka fi bi bashi Lagos ce kawai gaban Sakkwato", a cewarsa.
Ya ce dole ne su damu kamar jihar Sakkwato da tattalin arzikinta yake kasa a mayar da ita kantar bashi da za a gadarwa yaran da ma ba a haifa ba, da wuya a yi amfani da kudin in da ya dace.
Achida ya kara da cewar sun fahimci yanda ake cire mutane a cikin tsarin biyan albashin kananan hukumomi da gangan, wannan cirewar wani makami ne PDP ke amfani da shi na musgunawa don haka take kira gwamnatin Sakkwato ta dakatarda wannan bita da kullin na siyasa in ba a daina ba za su dauki matakin da ya dace kai tsaye sun fahimci ana son musgunawa 'yan jam'iyarsu ne kai tsaye.
"Abin mamaki da yawan mutane ba su iya bambanta siyasa da gwamnati, gaba daya gwamnatin Sakkwato ta gaza saboda a lokacin da wasu jihohi ke murnar samun romon dimukuradiyya, mu anan jihar Sakkwato ba wani abin murna", a cewar Achida.