Kotu Ta Rusa Zaɓen Fitar Da Gwanin Ɗan Takarar Gwamnan Jam'iyar APC A Jihar Taraba
Daga Ukasha Ibrahim.
Babban kotun tarayyar wacce ke da zamanta a jalingo fadar gwamnatin jihar Taraba ta rushe zaben fitar da gwanin na dan takarar gwamna a karkashin jam'iyar ta APC
Mai shari'a Simon Amobeda ya yanke wanan hukuncin ne ayau Talata inda ya rushe zaben fidda gwani na gwamnan jihar wanda jam'iyar APC ta gudanar a watannin da suka wuce inda dama jami'yar ta sanar da sanata Emmanuel Bwacha amatsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar
Mai shari"ar ya sanar da rushe wanan zaben kamar yadda daya daga cikin "yan takarkarun da suka fadi a awanan zaben mai suna Chief David Sabo Kente ya shigar da kara
Sanan alkalin ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta da tasake gudanar da zaben fitar da gwanin na 'dan takarar gwamnan jihar Taraba karkashin jami'yar APC nan da kwana 14 masu zuwa .
managarciya