Wahalar man fetur: NNPC ya sake ƙullawa ruwan sama
Kamfanin mai na kasa, NNPC ya alakanta karancin mai da ake fuskanta wanda ya haifar da layi a gidajen mai da mamakon ruwa sama da ake yi da tsawa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa wannan shine kari na biyu da NNPCL din ya ɗora alhakin karancin man akan ruwan sama.
NAN ya rawaito cewa mataimakin shugaban kamfanin, Dapo Segun ne ya bayyana hakan ga manema labarai a shelkwatar kamfanin dake Abuja.
Layuka dai sun karu a gidajen mai yayin da wasu ke siyar da duk Lita 1 kan Naira dubu 1.
Da yake neman afuwa kan matsalar karancin man, Segun a jiya Talata ya ce yanayin damuna da ake ciki ne ya haifar da tsaiko wajen rarraba man a fadin kasar nan, amma ya tabbatar da cewa komai zai daidaita nan bada jimawa ba.
"Muna so mu nemi afuwar 'yan Nijeriya bisa samun layuka a gidajen mai. Muna ganin hakan na kara yawaita. Abubuwan da suka haifar da hakan suna dayawa amma muna yi bakin kokarinmu", inji Segun.
Kamfanin na NNPC ya kuma ce akwai kalubale na hanyoyi wajen rarraba man, amma suna kokarin wajen kawar da matsalar.
managarciya