Buhari Zai Hanawa ’Yan Najeriya Cin Ganda Domin Ba Ta Da  Amfani

Buhari Zai Hanawa ’Yan Najeriya Cin Ganda Domin Ba Ta Da  Amfani

 

Gwamnatin Najeriya na shirin kawo kudirin dokar da zai haramta cin fatar dabbobi da aka fi sani Ponmo ko kuma Ganda a kasar saboda habaka masana'antun fata.

Muhammad Yakubu, babban daraktan cibiyar fata da kimiyya ta NILEST dake Zaria ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, TheCable ta ruwaito. 

Yakubu ya ce wannan yunkuri ya zama dole domin farfaɗo da masana'antun fata a fadin Najeriya. 
Ya kuma bayyana cewa, cibiyar da yake kula da ita da kuma sauran masana'antun fata za su tunkari majalisar dokokin kasar da na jihohi don tabbatar da haramcin. 
"A iya sani na, 'yan Najeriya ne kadai mutanen da a duniya suke rage darajar fata ta hanyar mai da ita abinci, duk da cewa Ponmo bai da wani amfani a jiki.
"A wani lokaci, an taɓa kai batun gaban majalisun biyu na dokokin kasar nan, kuma an yi muhawara a kai, amma ban san me shashashantar da batun ba." 
A fahimtarsa, yawan cin fatan dabbobi a Najeriya na daga cikin dalilan da suka kawo koma-baya a fannin masana'antun fata. 
Ya kuma bayyana cewa, duk da haka dokar kasa a fannin fata ta kawo wasu sauye-sauyen da suka rage matsalolin da fannin ke fuskanta, haka nan People's Gazette ta ruwaito. 
"Idan muka inganta masana'antun fatunmu, kuma kuma ana samar da takalma da sauran kayan fata a Najeriya, zai ba jama'a wahala su samu fata balle ma su iya ci.
"Idan aka tabbatar da dokar gaba daya, zata sauya durkusassun masana'antun fatu da dama sannan a samu sakamako mai gwabi."