Minister Ya Maida Rubuta Jarrabawar Ƙarin Matsayi Na Kukumomin NIS, NSCDC Jihohi
Ministan harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayar da umarnin a riƙa gudanar da jarabawar karin matsayi ga ma’aikatan Hukumar Shige-da-fice ta Ƙasa, NIS, da ta kashe gobara, da hukumar kare fararen hula, NSCDC da kuma hukumar kula da gidajen yari zuwa jihohi, maimakon Abuja kadai.
Ministan ya fadi hakan a jiya Talata, ya na mai cewa cibiyar da hukumomin ke amfani da ita wajen jarrabawar ta na da cunkoson jama’a, kuma hakan ba zai bayar da sakamakon da a ke buƙata ba.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Afonja Ajibola ya fitar, ta ce ministan ya ba da umarnin ne a lokacin da ya ziyarci Cibiyar Jarrabawa ta yanar gizo, CBT ta Saascon International School da ke Abuja.
Hukumar na amfani da wannan cibiya wajen gudanar da jarabawar karin girma ga hukumomi hudu da ke karkashinta.
Kakakin ma’aikatar ya ce Aregbesola ya lura cewa jarrabawar a cikin irin wannan yanayi mai cike da cunkoson jama’a ba zai ba wa tsarin mutuncin da ya dace ba.
Don haka ya umarci sakatariyar hukumar Aisha Rufa’i da ta gudanar da jarabawar karin girma a jihohi daban-daban na tarayya.
Aregbesola ya ce akwai cibiyoyi na CBT a fadin jihohin da za a yi amfani da su wajen gudanar da jarrabawar ba tare da wata matsala ba.
managarciya