Kebbi Radio: Ɓarayi ɗauke da makamai sun kwashe wasu muhimman kayan aiki a gidan rediyo 

Kebbi Radio: Ɓarayi ɗauke da makamai sun kwashe wasu muhimman kayan aiki a gidan rediyo 
Daga Sani Twoeffect Yawuri.
Ɓarayin waɗanda yawan su yakai kimanin mutane goma sha biyar (15) ɗauke da manyan makamai sun kai hari ranar Alhamis da ta gabata inda suka farwa masu gadin gidan rediyon harda jami'in tsaro na Civil Defense dake gadin gidan rediyon.
Ɓarayin sun yi amfani da bindiga da adduna inda suka jiwa masu gadin rauni kuma daga karshe suka daure su da waya.
Bayan sun ɗaure masu gadin ne suka shiga cikin ofisoshin gidan rediyon suka kwashe wasu manyan kayan aiki masu muhimmanci.
Ɓarayin sun shiga ofishin manajan gidan rediyon da kuma ofisoshin wasu daraktoci da kuma taransifomar wutar gidan rediyon da kuma dakin gabatar da shirye-shirye suka kwashe kaya masu yawa.
Daga cikin kayan da suka kwashe sun haɗa da; wayoyin taransifoma 33KVA, cables na janareto guda biyu, manyan baturori, armored cables, TV na bango, komfutoci, da kuma wasu manyan wayoyin dakin gabatar shirye-shirye masu muhimmanci.
Bayan samun wannan labarin ne, Kwamishinan yada labarai na jihar Kebbi Alhaji Yakubu Ahmed Bk da Mai baiwa Gwamna shawara akan harkokin yaɗa labarai Alhaji Yahaya Sarki tare da rakiyar Manajan gidan rediyon Injiniya Mahe Mohammed da manajan gidan talabijin wato KB TV Alhaji Aminu Sani Kamba da wasu jami'an tsaro suka kai ziyarar gani da ido gidan rediyon domin duba irin ɓarnar da barayin sukayi domin ɗaukar matakan da suka dace.
Da yake magana bayan kammala zagayen duba irin ɓarnar da barayin suka yi, Kwamishinan yada labarai da raya al'adun Jihar Kebbi Alhaji Yakubu Ahmed BK ya bayyana kaɗuwar sa bisa samun wannan mummunan labarin.
Haka kuma ya bayyana cewar wannan shine karo na uku (3) da ake kaiwa wannan gidan rediyo irin wannan harin amma wannan yafi kowani muni.
Kwamishinan ya bayyana cewar za'a ƙaddamar da gudanar da ƙwaƙwƙwaran bincike da kuma gudanar da garambawul akan harkokin tsaron gidan.
Haka kuma ya nuna bacin ransa bisa kasancewar wannan ɓarnar zata durƙusar da aikin gidan rediyon na wani lokaci inda za'a dauki lokaci ba'aji shirye-shiryen gidan rediyon ba saboda irin mummunar ɓarnar da ɓarayin sukayi na sace manyan Kayan aikin gidan.
Kwamishinan ya ƙara da cewar jami'an tsaro zasu gudanar ƙwaƙwƙwaran bincike tareda kama waɗanda suka gudanar da wannan mummunan aiki tareda tabbatar an samar da ingantaccen tsaro a gidan domin magance sake faruwar irin wannan a gaba.
Shima mai baiwa Gwamna shawara akan harkokin yaɗa labarai Alhaji Yahaya Sarki da manajojin gidajen talabijin da rediyon da suke nasu jawabin sun nuna rashin jindaɗinsu bisa wannan mummunan al'amari da ya faru a wannan gidan rediyon.
Sun bayyana wannan a matsayin abin baƙin ciki musamman da a halin yanzu maigirma Gwamna yana ƙoƙarin gyarawa da zamanantar da gidajen talabijin da rediyon jihar.
Haka kuma sun tabbatar da cewar za'a ɗauki dukkanin matakan da suka dace wajen tabbatar da ingantaccen tsaro a wannan wurin.
Bayan kammala zagayen duba wurin, jami'an Gwamnatin sun garzaya zuwa asibitin Sir Yahaya domin duba lafiyar masu gadin da ɓarayin sukayi wa rauni daban-daban.
A lokacin ziyarar duban nasu a asibitin, maigirma Kwamishinan yada labarai da raya al'adun Jihar Kebbi Alhaji Yakubu Ahmed BK ya ɗauki nauyin biyan kuɗin maganin masu gadin da akayi wa rauni a lokacin satar.
Tuni dai jami'an tsaro suka bazama wajen tabbatar da kama dukkanin waɗanda keda hannu a cikin aikata wannan mummunan aikin