Gwamnatin Tinubu Ta Fara Biyan Tallafin Man Fetur  A Boye

Gwamnatin Tinubu Ta Fara Biyan Tallafin Man Fetur  A Boye
 

Akwai alamun da ke nuna gwamnatin tarayya ta cigaba da biyan tallafin man fetur, bayan Bola Ahmed Tinubu ya soke tsarin. Rahoto da aka samu a The Guardian ya ce gwamnatin Najeriya na amfani da kamfanin NNPP da aka cefanar wajen hana farashi tashi. 

Kusan har yanzu NNPC kadai ke da wuka da nama wajen sha’anin man fetur a Najeriya. 
Binciken da aka yi ya nuna an yi asarar Naira biliyan 318 a kamfanin NNPC wajen shigo da man fetur duk da ana cewa an tara kudi. 
Ana biyan wadannan kudi ne a boye bayan Bola Tinubu ya sanar da nasarorin da aka samu a sakamakon cire hannun gwamnatinsa. Bayan an yi canjin gwamnati a kasar ne Huub Stokman na NNPC ya zama shugaban kungiyar MOMAN na manyan dillalan man fetur. 
Gwamnatin Bola Tinubu ta na yi wa ‘yan kasuwan rangwame ta hanyar ba su dala a farashi mai rahusa, bayan an daidaita farashin. 
Duk da NMDPRA ta ba kamfanoni lasisin dauko fetur daga kasashen waje, ‘yan kungiyar MOMON ba su samun dala da araha. 
Lissafin da aka yi ya nuna a karshen Agusta, kudin kowane litar man fetur ya karu da 19.88% zuwa kimanin N617 a kasuwannin duniya. Baya ga haka kafin ya iso gidajen mai sai an biya kudin dako a ruwa da na jigila daga tasohihi, amma har yau farashi bai motsa ba.
Sai da Dalar Amurka ta zarce N900 a hannun ‘yan canji, wanda hakan ya nuna babu abin da zai hana fetur kara tashi daga N615-N620. Da gwamnati ba ta fito da wannan dabara ba, farashin man fetur zai zama tsakanin N818 da N833 domin a N728.64 ya ke isowa Najeriya.