Gwamnatin Buhari Zai Sayawa Kasar Nijar Motoci Na Naira Biliyan 1.4

Gwamnatin Buhari Zai Sayawa Kasar Nijar Motoci Na Naira Biliyan 1.4

 

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta amince da sayen motocin da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.4 ga makwabciyarta jamhuriyar Nijar domin magance matsalar rashin tsaro. 

Rahoton Channels TV Ministar  kudi, da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ta tabbatar da hakan a ranar Larabar da ta gabata, inda ta bayyana cewa yin kyauta ga makwabciyarta Jamhuriyar Nijar ba sabon abu ba ne, kuma hakkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da siyan. 
A cewarta, shugaba Buhari, mutum ne da ba za ta iya tambayarsa dalilin daukar wasu matakai ba, saboda yana da hakkin yanke shawarar da zai amfani Najeriya. 
Ministan wacce tayi magana bayan taron majalisar zartaswa ta tarayya da shugaban kasa ya jagoranta, ta amsa tambayoyi dangane da wasu takardu da aka fitar a shafukan sada zumunta wadanda suka nuna cewa shugaban ya amince da fitar da kudaden ne a ranar 22 ga watan Fabrairun 2022 ga Jamhuriyar Niger.