'Yan Sanda Sun Kama Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Filato Kwana Biyar BayannTsige shi

'Yan Sanda Sun Kama Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Filato Kwana Biyar BayannTsige shi
'Yan Sanda Sun Kama Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Filato Kwana Biyar BayannTsige shi
Rahotanni daga jihar Filaton Najeriya na cewa jami'an tsaro sun kama shugaban majallisar dokokin da aka tsige ranar Alhamsi din da ta gabata, da kuma wasu 'yan majallisa 10 da ke goyon bayansa.

'Yan sanda sun isa zauren majalisar da karfe 3:15 na rana, kuma ba tare da wata-wata ba suka yi awon gaba da Honorabul Abok Ayuba da 'yan koren nasa su 10.

Wasu rahotannin sun ce jami'an tsaro sun bade wa masu bore a harabar majalisar dokokin da hayaki mai sa hawaye(barkonon tsohuwa).

An ambato dan majalisa mai wakiltar Langtang ta Kudu Honorabul Zinghtin Sohchang yana faɗa wa 'yan jarida cewa "gamu nan jami'an tsaro sun tura mu cikin mota ƙirar Hilux kuma bamu san ina za a je damu ba."

A makon da ya gabata ne 'yan majalisar dokokin jihar Filato suka tsige shugaban majalisar Abok Ayuba, wanda aka dade ana hasashen cewa basa ga maciji da gwamna Simon Lalong na jahar ta filato. 

Musa Dahiru Ajingi