Jiragen yaƙi na sojin Najeriya sun lalata mafakar ƴan bindiga a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa dakarun rundunar sojin saman Najeriya (NAF) sun lalata mafakar babban shugaban ƴan bindiga, Babaro, da ke Dutsen Pauwa a ƙaramar hukumar Kankara, tare da ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida na jihar, Dr. Nasir Mu’azu, ya fitar da sanarwa a ranar Asabar inda ya ce samamen da rundunar sojin saman ta kai da safe ya kai ga hallaka mafakar Babaro, wanda ake zargin shi ne ya jagoranci harin da ya kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu a Unguwar Mantau, ƙaramar hukumar Malumfashi.
Mu’azu ya ce waɗanda aka yi garkuwa da su a harin Unguwar Mantau duka an ceto su, ciki har da mata da yara. Sai dai ya bayyana cewa wani yaro guda ya rasa ransa a lamarin.
Ya ƙara da cewa wannan samame na cikin dabarun kawar da sansanonin masu aikata laifuka, raunana hanyoyinsu, da kawo ƙarshen kashe-kashe, satar mutane da suka addabi jama’a.
“Ceton waɗannan mutane ya nuna tasirin haɗa kai tsakanin hare-haren sama da na ƙasa, yayin da jami’an tsaro ke ƙara ƙaimi wajen fatattakar ƴan bindiga da dawo da kwarin gwiwa ga jama’a,” in ji Mu’azu.
managarciya