Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Tsoron Kai Harin Ta'addanci

Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Tsoron Kai Harin Ta'addanci

 

Babban kantin Jabi Lake Mall dake unguwar Utako a birnin tarayya Abuja ta rufe dukkan shagunanta ranar Alhamis sakamakon barazanar tsaron da ake yiwa garin.

 A jawabin da kantin ya daura a shafinsa na Instagram @jabilakemallnigeria, hukumomin sun bayyana cewa duk da cewa ba tada niyyar tadawa mutane hankali, sun yanke shawaran haka ne domin kare rayukan masu zuwa siyayya da ma'aikatanta. 
Sun kara da cewa suna bibiyan yadda alamarin ke gudana kuma idan komai ya daidaita za'a bude. 
"Ga dukkan kwastamominmu, zamu rufe Jabi Lake Mall yau, Alhamis, 27 ga Oktoba, 2022." "Mun yanke wannan shawara ne don kare lafiya ma'aikatanmu da kwastamominmu." 
"Muna bibiyan lamarin kuma muna shawara da hukumomin tsaro kuma zamu sanar da ku lokacin da zamu bude." "Muna ba da hakuri bisa wannan abu, mun gode."