Gwamnan kogi ya Tsallake rijiya da baya
Sakamakon harin da masu bata gari suka kaimasa.
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, CON, ya tsallake rijiya da baya. A wani hari da wasu mahara sanye da kayan sojoji suka kai wa tawagarsa.
Al’amarin ya faru ne a kusa da Babban Birnin Tarayya, Abuja, a ranar Lahadi 22 ga watan Oktoba, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, lokacin da Gwamnan ke ƙoƙarin komawa Lokaja don ya gabatar da wasu al’amuran gwamnati.
Kamar yadda wani rahoto daga fadar gwamnatin Kogin ya bayyana cewa, maharan sun buɗe wa a yarin motocin gwamnan wuta, sai dai jami’an tsaron da ke kula da Gwamnan sun yi nasarar ba shi kariya.
An buƙaci mutane da su kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro.
Gwamnatin jihar ta Kogin ta ce tana haɗa guiwa da sauran hukumomin tsaro domin kare al’ummar jihar.
managarciya