Yakamata Tambuwal ya sallami Kwamishinan ma'aikatar Muhali

Yakamata Tambuwal ya sallami Kwamishinan ma'aikatar Muhali

 
Daga Muhammad M. Nasir.

 
 
Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya samar da kwamishoninsa ne a gwamnati domin su tallafa masa da aiyukkan da zai gabatar zuwa ga al'ummar jihar Sakkwato domin samar da cigaba mai dorewa.
Kwamishinan Muhali Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa yana cikin kwamishinonin da Tambuwal ya samar domin ya sauke nauyin da ya dauko wa  jama'ar jihar Sakkwato.
A bayanan da Managarciya ta samu wanda ba su  tabbata ba an ce duk wata bukata da ma'aikatar Muhali ke so Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal bai wasa da biyan bukatarsu domin sanin muhimmancin ma'aikatar ga rayuwa da lafiyar jama'ar jihar.
Duk da mayar da hankali da yin tsayin daka da ake ganin Gwamna Tambuwal ya yi ga ma'aikatar muhali ta jihar Sakkwato yakamata ya rika samun dimbin godiya da jinjina amma sai aka rika samun akasin haka abin da ake dangantawa da wakilin Tambuwal a ma'aikatar wanda shi ne kwamishinan Muhali barci ya kwashe shi a aikin da aka daura masa.

A wannan shekara ta 2021 jihar Sakkwato sun samu yawaitar SAURO a dakunan mutane a waje a wurin ko'ina, safe da marece, al'amarin da ya zama sabo a jihar domin a kowace shekara  ta damana ana ganin sauro a lokacin fiye da sauran lokutta sabanin a wannan shekara da wasu ke ganin kamar yana son cimma kuda a wurin yawa a cikin birnin jiha.
A binciken da Managarciya ta gabatar yawaitar sauron a birnin jihar Sakkwato musamman, yana da nasaba ne da yanda Shara ko Bola ta mamaye jihar ta ko'ina ba unguwa ba yanki.
A ziyarar da Managarciya ta yi a titin Mai Tuta da Kahon Karo da Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki da Lokoja da Unguwar Minanata, da sauransu,  ta matukar tausayawa mutanen dake zaune a wuraren domin yanda suke fama da sauron kai kasan dole a samu yawaitar zazzabin cizon sauro a wuraren da wasu ciruta masu alaka da cizon sauro.
Cutar Kwalara jihar Sakkwato na cikin jihohin da ke fama da ita abu na kan gaba da ke haddasa ciwon, kazanta na ciki, kwamishinan muhali ya bari jihar Sakkwato ta kazance gaba daya, ba tare da ya fito ya yi kowane irin bayani duk da wasu na ganin kamar yana tsoron magana a gaban manema labarai.
A yanda Gwamna Tambuwal yake mutum mai son tsafta da son kawata wuri, a ce shi ne Gwamna garin da yake jagoranci yake haka da kazanta kasan kam kwamishinan muhali bai yi masa adalci ba.
Barin Bola a ko'ina cikin jihar nan ba wata hobbasa ta zahiri sai fadin za a yi an bar mutanen da ke kusa da sharar  cikin wahalar daukar ciruta daban-daban, ko ba ka yi karatun addininka ba kasan alhaki ba zai bar kwamishinan muhali ba, domin shi ne wakilin gwamna kuma bai taba kokawa  gwamna bai ba shi hakkin da ya rataya kansa domin gudanar da aikin al'umma na ceto lafiya da rayuwarsu ba.

Managarciya ta tuntubi Kwamishinan Muhali Sagir Attahiru Bafarawa don sanin wannan nauyin dake saman kansa zai iya saukar da shi kuwa, ko dai a shawarci Tambuwal ya kawo jajirtacce da zai fitar da jama'a halin da suke ciki a ga Sakkwato ta dawo FES, TAS sai dai bai dauki kiran wayar da aka yi masa ba, kuma an tura masa sakon kar-ta-kwana har zuwa hada wannan bayani bai ce uffan ba. 
Matukar dai Tambuwal ya ba da duk wani hakki na yin aikin tsaftace Muhali a jihar Sakkwato kuma ake wasa da aikin da ya bayar yakamata ya sallami kwamishinan Muhali domin aikin al'umma ba a sanya gata a cikinsa.