Jami'ar Bayero Kano ta  Ƙaddamar Da Ƙamus Ɗin Hausa Zuwa Turanci

Jami'ar Bayero Kano ta  Ƙaddamar Da Ƙamus Ɗin Hausa Zuwa Turanci

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

A ranar Asabar da ta gabata an kaddamar da sabon kamus din harshen Hausa zuwa Ingilishi da ya gudana a dakin taro na  Convacation Arena Jami’ar Bayero ta Kano,

Littafin dai yana dauke da shafi 627, wanda Bature kuma masani a bangaren harsuna da ke Jihar Indiana ta Amurka, Paul Newman da maidakinsa, Roxana Ma Newman suka wallafa, kuma madaba’ar jami'ar Bayero ta buga shi.

Newman dai ya taba zama a  Kano ne tun a  shekarar 1972, inda ya  zama Darakta na farko a Cibiyar Koyar da Harsunan Nijeriya a BUK, lokacin tana Kwalejin Abdullahi Bayero.

Da ya ke ta’alikin littafin, Shugaban Hukumar Bunkasa Binciken Ilimi ta Nijeriya (NERDC), Farfesa Isma’il Junaidu, ya ce Kamus din shi ne irinsa mafi girma tun kusan shekarun 1930.

Ya kara da cewa an rubuta littafin ne ta hanyar amfani da daidaitacciyar Hausa, yayin da mawallafin littafin shi kuma yana daya daga cikin masu fada a ji a duniya, a bangaren harsunan yankin Tafkin Chadi.

A jawabinsa na wakilta mawallafin littafin Paul Newman, Shugaban Makarantar Karatun Gaba da Digiri ta Jami'ar Bayero Farfesa Mustapha Ahmad Isa, ya ce kamus din wani muhimmmin cigaba ne a fannin koyarwa da kuma bincike a harshen Hausa.

Kazalika Paul ya ce, “ A cikin shekaru 50 dai-dai da na shafe a Kano sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar rubuta wannan littafi 

“idan aka yi la'akari da yawan Hausawa a duniya r nan da masu amfani da harshen Hausa, babu shakka ta na daya daga cikin harsuna mafi muhimmanci a Afirka, kuma daya daga cikin manya a duniya,” inji Paul.

Tun farko a jawabinsa, Shugaban Jami’ar ta Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce kaddamar da littafin ’yar manuniya ce kan irin gudunmawar BUK a bangaren ilimi.

“BUK na daya daga cikin ja-gaba a cikin jerin cibiyoyin ilimi wajen koyar da Hausa a ciki da wajen Najeriya. Mawallafin wannan littafin sananne ne a fannin harsuna.

“Kuma sai da muka kafa kwamitin masana harsuna suka yi nazari sannan suka ba da shawarwari, kuma marubutansa suka karba suka yi murna, kafin a kammala shi,” inji Farfesa Sagir.

Taron dai ya samu halartar manyan mutane da suka hada da: Jakadiyar kasar Poland a Nijeriya, Joanna Tarnawska da mai taimaka mata Khadija Alƙali, da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da sarakunan Kazaure da Karaye, da kuma wakilan Gwamnonin Jihohin Kano da Bauchi da Jigawa da Katsina da kuma wakilin babban mai kaddamarwa Dr. Alhaji Aminu Alasan  Dantata, da manyan Farfesoshi da Daktoci da suka halatta a daga cikin jami'a da wajen jami'ar.