Rufe boda ya talautar da Kasuwancinmu---Mutanen Kebbi

Rufe boda ya talautar da Kasuwancinmu---Mutanen Kebbi

 

 

Al'ummar jihar Kebbi musamman mutanen garin Kamba suna Shan bakar wahala sanadiyar koma bayan da aka samu a haujin kasuwanci sanadin rufe boda da tsohuwar gwamnatin Buhari ta yi abin da ya kasa haifar da da mai ido kan haka talakawa suke ta yin tir da wannan tunani na wahala.

A yankin Kamba da Bunza da Dakin Gari da Argungu komai ya tsaya cik a haujin Kasuwanci domin wuraren sun fi aiwatar da kasuwanci na fita wajen kasa zuwa Nijar da Benin.

Mutane a gefen jihar Kebbi kasuwancin nasha bakar wuya  musamman a bangaren kayan da ake shigowa da su ta hanyar kasar Nijar da Benin waton shinkafa da man girki da kayan tufafi na sawa da ake kira Gwanjo da Masara.

Garba Nahali Kamba manomi ne da yake huldar kasuwaanci a Nijar in da yake shigowa da shinkafa da Gwanjo ya ce manyan 'yan kasuwa a Kamba zaune suke a yanzu.

"Rufe boda a gefen Kamba ya shafi kasuwancin al'umma ina tabbatar maka masu tafiya kasar Nijar kashi 40 cikin 60 sun daina zuwa suna zaune ba abin yi, a baaya kafin a rufe bodar mutumin da ya fi karfin miliyan 10 wasu 20, ga yara karkashinsa ana hulda, amma yanzu sun koma zaune ba abin yi da yawansu komai ya kare abin da za su ci sai an taimaka musu.

"Kasuwancin fito  abu ne da yake cikin jini ga kuma sabo wani ya shekara biyar wani 10 yana kasuwancin bai iya wata sana'ar ba sai wannan ga shi an dakatar da ita an kuma ja lokaci," Kalaman Kamba.

 Ya kara da cewar duk kasuwanci da ake yi a gefen ya tabu komai ya tashi sabanin lokacin da ba a rufe boda ba, kasuwanci sirri ne ina tabbatar maka lokacin da boda na bude a kiyasi matasa masu shekara 20 zuwa 35 za ka samu yaro 30 a Kamba kowanensu ya fi karfin miliyan 100 na kansa amma yanzu sai ka samu sai an taimaka masa domin an daina juya dukiya suna zaune ba abin yi.

Mi kake ganin za a yi a farfado da kasuwanci? ya ce ba abin da muke ganin yafi da zai wuce a aminta a shigo da Masara da Shinkafa da Man Girki in aka yi haka duk da akwai tsadaar sefa(kudin Nijar) 1800 na Nijeriya su ne 200 na Nijar ka ga akwai kalubale abin da yafi a sakar mana mara garin Kamba an daina huldar kasuwanci a baya za ka samu a yini mutum zai yi kasuwancin naira miliyan 20 zuwa 30 a yini daya amma yanzu ba wannan maganar komai ya lalace.

Kabiru Shehu Kamba ya ce harkar kasuwancinmu tana bukatar agajin gaggawa domin komai ya mutu anan an yake mana hulda da mutanen Kasar Benin ni mutum ne mai sayo gwanjo da shadda a Binin duk sati a baya sai na tafi na kawo kaya amma yanzu a Nijeriya nake saye kaya saboda an rufe boda kasuwancinmu ya mutum gaskiya a baya duk na sayo kaya bayan na sayar zan iya samu riba sama da dubu 300 amma yanzu kasuwancin ina yi ne domin na ci abinci da iyalina baa zancen riba.

Ya ce akwai bukatar gwamnati ta yi wani abu duk da dai mun cire tsammanin bude boda anan kusa ganin dan Arewa ne da yakamata ya yi kishin 'yan uwansa amma bai yi ba ya rufe, da wuya dan Kudu ya bude ta don kasar nan ta ginu kan kabilanci.

Mu'azu Yusuf dan garin Bunza ne ya koka sosai yanda harkar kasuwanci ta shiga wahala a yankin jihar Kebbi da kewaye kafin rufe boda arzikin yankin nan  yana bunkasa kamar wutar daji za ka samu mutum yana noma yana kasuwanci sai ka samu komai lafiya lau sabanin yanzu da komai sai addu'a, a baya ina kasuwancin shinkafa amma na jingine ganin yanda matsalar kasuwancin ya tabarbare. 

Hanifa Muhammad Kamba ta ce gurguncewar kasuwancinmu kan maganar rufe boda ne ba kamar yadda wasu ke ganin don an samu matsalar konewar kasuwa ne, gobara ba ta sa kasuwanci ya ja baya  kodan, lamarin ne na rufe boda.