Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya, mai wakiltar kananan hukumomin Zuru, Fakai Danko, Wasagu da Sakaba, da ke jihar kebbi, Hon Kabir Ibrahim Tukura, kuma shugaban matasan yan majalisun Najeriya, kana kwamitin Sharia a majalisar Najeriya.
Shuwagabannin jam'iyyar APC, dake mazabun Zuru Fakai, Danko Wasagu, da Sakaba, sun amfana da motocin alfarma daga Hon Kabir Ibrahim Tukura.
Tukura ya bayyana cewa jam'iyyar APC a jihar kebbi, a karkashin jagoranci Sanata Abubakar Atiku Bagudu, mai karfin gaske ce kuma wajibi ne ga yayan jam'iyyar APC su rinka miko mata dukkanin tallafin su, domin ganin jam'iyyar ta cigaba da rike matsayin ta.
Shugaban jam'iyyar APC, na jihar kebbi, Abubakar Muhammad Kana ne ya jagoranci rabon motocin ne wanda ya nuna farin cikinsa bisa yadda Hon Kabir Ibrahim Tukura, ya zuba kudinsa masu yawa wajen ganin ya kyautatawa shuwagabannin jam'iyyar APC.
Abubakar Muhammad Kana, shine ya Kaddamar da wannan rabon motoci, ga shuwagabannin jam'iyyar APC, kuma ya ce wajibi ne ga shuwagabannin jam'iyyar APC, suyi biyayya ga jagorancin gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, kuma suyi aiki tukuru domin ganin cigaban jam'iyyar APC da gudanar da ayyuka da hidimtawa jam'iyyar APC a matakin jaha da kananan hukumomi.
Mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar kebbi, Hon Usman Mohammed Ankwe, yana daya daga wadanda suka halarci wannan rabon motocin, kuma yayi godiya da jinjina ga Hon Kabir Ibrahim Tukura, yayin da yake jawabi Ankwe a wurin kaddamar da rabon motoci, ya bayyana Hon Kabir Ibrahim Tukura bisa fadada harkokin dimokradiyya dama samar da romonta ga al'ummar Zuru musamman talakawa.
Wadanda suka amfana da wa'dannan motoci sune shuwagabannin jam'iyyar APC, a matakin kananan hukumomi, 4 Alh Abubakar Abiyola, Zuru, Alh Umar Aliyu Sabo Sakaba, Haruna Abuyayi Chonoko Danko Wasagu, Alh Ummaru Uchiri Fakai.