HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita 35
HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 35
Cike da ƙaraji yake faɗin, "Wallahi ita ce ! Tabbas ita ce, matata ce Jiddah ita na fito nema, waye ya bata ikon yin wata shari'a?"
Mutanen motar sai suka ɗauka ko mahaukaci ne dai, domin tun da ya shigo yake wasu abubuwa kamar na zararre. Shi dai mai waya ya samu ya amshi wayarsa kar da ya jefar mai da ita ya ja mai asara haka kawai don bai ga alamar zai samu ko da rabin kuɗin wayar ba a gunsa.
Wani da yafi kowa son jin kwaɓ ya dubi Deeni ya ce, "Shin bawan Allah da gaske matarka ce Barista Jiddah? Amma kuma kana nan tana Kaduna taya ake zaman aure haka?"
Deeni ya ce, cikin muryar kuka-kuka , "Matata ce Jiddah sai dai tsautsayi ne yasa na sake ta, yanzu haka Kano nake da niyyar zuwa don na maidata ɗakinta amma sai na ganta a waya wai ta zama lauya."
Wani ya ce mai, "Amma da gani dai baku taɓa haihuwa ba ko? Don ba alamar ta taɓa haihuwa ma wannan yarinyar."
Deeni ya cije leɓensa ya ce, "Haihuwarta biyu gidana ta biyun ma ƴan biyu ta haifa duk mata, yanzu haka suna gidansu gun mahaifiyarta ko Yau na gansu da zan taho."
Wanda ke gefensa ya ce, "Amma dai kai baka duba ma kanka ba, ai Malam ba a rabuwa da irin waɗannan matan duk gumu duk wahala haƙuri ake da su saboda su ɗin na daban ne, yanzu ba don ka faɗi ba wa zai yadda cewar ta taɓa aure?"
Deeni ya sadda kansa ƙasa yana jin hawaye na zubowa daga idonsa, tabbas ya zama marar rabo ya tabka uban kuskure wanda yanzu yake son gyarawa amma bai san ta ya zai gyara shi ba sam.
Wani saurayi da tun da ya shigo motar bai tanka ba sai yanzu ya ɗago kai ya dubi Deeni ya yi murmushi ya ce, "Ashe akwai ranar da zaka iya zubar da hawaye akan Jiddah? Ashe akwai ranar da zaka iya tuna Jiddah har ka ji tai maka rana Deeni? To idan mafarki kake ka farka domin Jiddah tafi ƙarfin ka a yanzu ta gama zaman ƙunci da takaici da zaman hawan jini a gidanka. Deeni ina son nayi maka albishir ɗin cewa Jiddah ta zama babbar mace wadda tafi ƙarfin irinka ko ada ba ajinka bace ba Jiddah kawai ƙaddara ce da rabon yaran dake tsakaninku yasa aka baka aurenta. Yau Deeni ina taƙama da gadarar da kake nunawa Jiddah? Ina hantara da muguntar da kake nunawa Jiddah? Duk sun wuce nasan yanzu haka Jiddah ta jima da manta anyi ruwanka a duniyar ma."
Deeni ya fashe da kukan gaske yana kallon Likitan dake duba Jiddah duk lokacin da hawan jininta ya tashi, daman ya sha ba shi shawara kan yadda yake tafiyar da rayuwarsa da Jiddah amma sai ya taka mai burki ya ce mai kada ya sake shiga cikin rayuwar aurensa ya tsaya matsayinsa kawai.
Cike da takaici Likitan ya dinga ba mutanen cikin motar labarin Deeni da Jiddah wanda ya sani da wanda ya ji mutane na faɗi. Nan take akai ma Deeni caa a cikin motar har wasu na cewa sakayya ce ke damunsa Allah Ya ƙara Yasa ma Jiddah albarka Ya bi mata haƙƙinta kan shi, yanzu ya fara ganin bala'in rayuwa ma sai nan can gaba zai tantance miye rayuwa. Wani tsoho ya ce, "Ka gode wa Allah yaro tunda ka haihu da ita darajar yaran ta dinga taimaka maka kai ma ka lashi arziƙin yaranka."
Likitan ya yi karaf ya ce, "Sai dai idan bai da kunya amma shi da ya dinga faɗa gaban kowa bai iya riƙe mata yaran tunda ta haifa ta ji da abin ta?"
Mazan motar suka saka Salati baki ɗaya suna kallon Deeni daya gama muzanta a cikin motar.
Likitan ya jawo wayarsa ya ce, "Bari ku ji ina waya da ita Ni saboda ina duba yaranta da Mamarta idan basu lafiya." Ya ƙare maganar yana danna kira a wayarsa.
Da yake handsfree ya saka wayar kowa na iya jin ƙarar ringing ɗin wayar.
Kamar zata katse ta ɗaga kiran,
"Assalamu alaikum Likita bokan Turai."
Yana kallon Deeni ya ce mata, "A kune manya yanzu ai, don yanzu naga wani labari ashe daman da babbar Lauya muke tare ba bayani?"
Suna jin sautin dariyarta a hankali tana cewa, "Kai haba ai duk wasu manya bayan Likitoci suke muna bayanku dai mu."
Deeni sai ya ji muryarta ta ƙara wani tarr sai ya ji tamkar busar sarewa haka yake jin muryarta na dokar dodon kunnensa, ashe haka Jiddah ke da murya mai sanyi da zaƙi bai taɓa ankara ba duk zaman da ya yi da ita ba sai yanzu.
Likita ya ce mata yana duban Deeni, "Sai kuma na samu labarin za ki koma gidan Deeni, nace to bari na kira ki nayi maki Allah Yasa alheri duk da ba a gaya mana ba, mun tsinta a gari ai har ga shi mun kira."
Ta ja wata siririyar dariya tace, "Likita kana magana ne kan wa kenan? Ka sa na shiga tunanin inda nasan sunan ma Ni kai tsaye, ko dai kaine za kai aure kake min ta ƴan birni ne?"
Deeni ya zaro idanuwa waje, wai kardai ace Jiddah da gaske ta manta da shi a rayuwarta? Shi ya ɗauka tana can tana jiran shi ya je ya ce ya maidata ɗakinta ashe ba haka bane ba?
"Kar da ki min haka Jiddah wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba."
Da ƙarfi yake maganar don haka hatta ita ta ji sai dai ko da alama bata ɗauki Muryar mai maganar ba, haka bata ma ɗauka da ita ake ba, don haka tai dariya tace, "Likita afuwan zan ɗan gana da wani bawan Allah ga shi nan yana jirana zan kira ka idan na gama, don Allah ka gaida min su Mama idan ka je gidan."
Ya kashe wayar yana cewa "To babbar Lauya ki huta lafiya sai mun yi waya."
Nan take sai wasu suka amince da maganar Likitan don haka sai suka ga miye abin tausayawa wanda bai san ciwon kansa ba? Sai kawai kowa ya ja bakinsa ya yi shiru akai banza da Deeni dake ta rizgar kuka kamar ƙaramin yaro.
Suna isa Kano kowa ya watse , Deeni ya tsaida abin hawa ya gaya mai unguwar da Mama tai mai kwatance nan ne gidan Hajjo, suka tafi yana ji a ransa ko kwantawa ne ya yi ƙasa zai yi gun ba Hajjo haƙuri indai zata haƙura ta saka baki Jiddah ta koma gidansa.
Hajjo na zaune tana waya da Mustapha yana bata labarin abin da ya faru, Hajjo kamar tai tsalle don murna wai Jiddah ce gaban jama'a tana matsayin Lauya tana kare wata matsayinta na Lauya!
Tabbas Allah ba azzalumin Sarki ba ne ba, daman tana ji a jikinta wata rana Jiddah zata zama abar kwatance kamar yadda ta zama a baya sai dai wannan kwatancen ya sha bambam dana baya domin wannan na alheri ne bana damuwa ba irin wancan ba.
Cike da farin ciki Hajjo ke cewa "Yanzu nan Jiddah da kanta ta tsaya gaban Alƙali tai magana? Gaskiyar magana zan so ganin wannan rana da idona wadda Auta ya so gani Allah bai nufa ba, ko da yaushe burin Auta Jiddah ta zama wani abu Yau ga shi ta zama bai raye! Hawaye suka zubo mata ta goge don tasan Allah mai iko ne akan komai shi ne ya bata shi ne ya amsa.
Shi kanshi Mustapha ya ji ba daɗi sosai da tuno Salim amma ya za su yi haka Allah Ya nufa sai su gode ma shi kawai.
Suna gama wayar akai sallama ta amsa tana ta ƙara kakkaɓin abin na sauyar Jiddah zuwa Lauya lokaci guda kwatsam.
Umarnin shigowa ta bada, don haka Deeni ya shiga yana sake maimaita wata sallamar.
"A'uzubillahi minasshaiɗanin rajim! Cewar Hajjo tana kallon Deeni tana ƙara neman tsari daga shaiɗani.
Cike da masifa ta nuna mai inda ya shigo tace, "Maza-maza ka juya ka koma inda ka fito kafin nasa ai maka shegen duka wallahi.
Haka kawai muna cikin farin ciki zaka bayyana gare mu? To Li'ilafi kuraish, wallahi aniyarka ta bika ja'irin yaro insha Allah Jiddah ta gama baƙin ciki a rayuwarta."
Deeni ya tsugunna ƙasa idonsa na zubar hawaye ya ce, "Don Allah Hajjo ki yi haƙuri ki gafarta min laifukan da nayi maki ki saka baki Jiddah ta koma ɗakinta wallahi na sauya halayena yanzu na kimtsu na koma mutumin kirki kamar kowa...
"Kai rufe min baki, tsohon munafukin Allah ta'ala! Watau ka ji labarin yarinya ta yi gaba ta samu matsayar arziƙi a rayuwarta shi ne zaka kwaso tsumman jiki ka zo da maganar ta koma ɗakinta, to nace Uwaka kai da ɗakin.
Tun kafin na kira iyayenta su zo su iske ka suima halinka na rashin mutunci gwara ka bar gidan nan tunda ba naka bane haka ba aika maka akai ba ka zo."
Deeni sai kuka yake yana ba Hajjo haƙuri abin da ya tunzura ta kenan ta kira Mustapha da suka gama waya yanzu tana cewa "Bari na kira maka ita ka ji daga bakinta tunda Ni ka raina Ni."
Mustapha ya ɗaga wayar yana tunanin ko mantuwa Hajjo tai sai kuma ya ji tana cewa, "Kai Mustapha haɗa Ni da Jiddah na gaya mata ga tsohon mijinta nan ya zo ya tasa Ni gaba wai ya maidata ɗakinta."
Cike da tashin hankali Mustapha ke cewa, "Kamar ya kenan Hajjo me ya kawo maganar maidata ɗakinta a nan kamar bata gama idda ba?"
Hajjo tace cikin gatse, "E man ya maidata a matsayin ubanta wanda bai san takan addini ba ko."
Cikin damuwa Mustapha ya ce, "Hajjo maza yabar gidan nan kafin nasa a zo a fitar da shi, ko dai yana shaye-shaye ne ya sha ta gaya mai ƙarya ya zo nan?"
Hajjo tace, "Ni dai ba Jiddah wayar na ba shi ta ja mai kunne kawai tunda ba yarinya bace ba ita."
Kamar tana gabanshi Hajjon haka Mustapha ya zaro idanuwa waje, ai wallahi ko mai zai faru ya gama jin muryar Jiddah kai ko ganinta ba zai sake yi ba ta riga tayi mai nisan da ba zai iya kamota ba. Abin da yake raya wa kenan a ranshi a fili kuma sai ya ce ma Hajjon. "Ai tana ɗakin ganawa da baƙi don haka ba zan iya haɗa su ba, kawai ya koma inda ya fito Hajjo."
Hajjo ta dubi Deeni fuska cike da ɓacin rai tace, "To ka dai ji da kunnenka Jiddah na can na ganawa da baƙin kirki irin albarka sai ka koma inda ka fito kaban waje na gaji da kallonka ina tuna baƙar izayar da ka dinga ganawa yarinya. Kai Allah na tuba ma ba zan musu ba idan aka ce baƙin cikin abin da kake ma yarinyar ne ya kashe mata Uncle Salim ɗinta ba."
Ko da Deeni ya ji Hajjo na neman ɗora mai kisan kai sai ya tashi yana share hawaye ya fice daga gidan bai san inda za shi ba.
Mustapha na zaune duk ranshi ya ɓaci akan me ma Hajjo zata bar wani banzan tsohon mijinta ya shigar mata gida har da cewa wai ya maida Jiddah ɗakinta? Ɗakin ubansa ya maida ta? Tabbas akwai aiki a gabansa duk da yasan cewa babu yadda za ai Jiddah ta koma gidan mijinta amma kuma yana hango barazana daga Alƙalin nan yadda yake ƙure Jiddah da kallo, komi tace bai mata jayayya kai tsaye yake amsar buƙatar ta.
Shi kam ya zai yi ne ya tunkari Jiddah da maganar dake cin ranshi ta ƙaunarta? Yasan cewa yana cikin matsala a gidansa amma hakan bai hana shi jin so da ƙaunarta ba a ranshi ba.
Yana zaune abin duniya duk ya dame shi Jiddah ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi kamar yadda take ko da yaushe.
Ta dube shi tace, "Akwai yiyuwar zan fita na je gidan da Mamar Alawiyya ta zauna zan duba wasu abubuwan da nake buƙata, don haka mu je gidan da aka ban ka huta Ni sai na wuce."
Kallonta yake yana jin tamkar ya haɗe ta don so, ji yake tamkar ya maidata ciki ya huta da munafukan da ke mata kallon so, amma ba dama, sai dai ba zai amince tai yawo ita kaɗai ba dole ne duk inda ta aje ƙafa ya ɗora tashi ƙafar a gun. Don haka ya miƙe ya ce, "Mu je ai ban gaji ba, kuma daman amfanin rakiyar kenan ai."
Ta juya ya bita a baya suka fice wata mota suka nufa suka zauna a baya dukkansu ya ja suka nufi gidan Major.
Ko a motar sai kallonta yake yana ƙara jin ƙaunarta na yawo a ranshi, ita kuma sai karanta file ɗin case ɗin take tana nazari wani lokacin tai murmushi wani lokacin ta ja tsaki.
Suna isa gidan mai gadin gidan ya gaya masu masu gidan sun ce kada a bar kowa ya shigar masu gida hutawa suke.
Jiddah ta fito fuskarta ba alamar damuwa tace, "Saƙo mai kyau, amma ka sani a cikin dokar tasu ban da ta masu bincike don haka maza buɗe mana ƙofa, da ƙafa ma za mu yi tattaki har ciki."
Ba yanda zai, kuma sai yaga yarinyar tai mai ƙwar jini, sai fara'a take ba wani haɗe rai da nuna isa, don haka ya samu kanshi da buɗe masu ƙofar gidan.
Ita da Mustapha suka shiga gidan suna kalle -kallen yadda tsarin ginin gidan yake.
Har suka isa ƙofar falon gidan su kai sallama ba wanda ya amsa ma su, sai da su kai sau uku ba amsa don haka ta shige gaba yana bin ta a baya suka zauna kan kujerun falon Jiddah na ƙarewa falon kallo da nazarinsa.
Tun da suka shigo Hajiya Turai ke kallonsu tana mamakin daga inda suke.
Ganin sun zauna kamar wasu mutanen gidan yasa ta fito cike da taƙama da alfarma ta isa gabansu ta jefa masu tambayar wa suke nema?
Jiddah tai murmushi tace, "Ke muke nema domin gunki muka zo, ina fatan za ki ban haɗin kai kamar yadda aka saba?"
Hajiya Turai ta zubama Jiddah ido tana mamakin tsaurin idon yarinyar, da tunanin wace ce ita kuma? Daga ina ma take? Waye ya turo ta?
Jiddah ta gyara zaman tabaran fuskarta tace, "Sunana Barista Jiddah nice sabuwar Lauyar da ke kare Fatima a shari'ar da ake gwabzawa."
Hajiya Turai ta yamutsa fuska, "Maganar banza to Ni ina ruwana da wannan can ku ta shafa ai."
Jiddah tai murmushi sosai tace, "Ko zan iya sanin alaƙar ki da Fatima?"
Cikin masifa Hajiya Turai tace, "Kishiya ta ce sai me kuma?"
Jiddah ta dubeta sosai tace "Kishiyarki kuma? Dama Fatima nada kishiya ne?"
Hajiya Tani dake isowa gun tace, "Ga wata ma nan, domin ni ma kishiya tace Fatima."
Jiddah tai murmushi tace, "Na fahimta sosai na gane lamarin, sai dai na kasa fahimtar abin da yasa ban ga an rubuta Fatima nada kishiya ko ɗaya ba a file ɗin case ɗinta ba."
Suka fashe da dariya suka taɓa, Hajiya Turai tace, "Saboda Fatima ba asalin kishiya muka ɗauke ta ba, tun fil azal daman baiwa muka ɗauki Fatima a gidan nan."
Hajiya Tani tace, "To ban da ma wauta ina mu ina kishi da Fatima daman Hajiya Turai? Ai Fatima kasada ce tasa ta auri mijinmu ba komai ba, ko da yake rabon makance ne yasa ta shigo gidan nan." Suka sake kashewa da dariya.
Mustapha ji yake kamar a mafarki lamarin, kamar ba da gaske ba abin ke faruwa, mamakin wane irin mutane ne waɗannan yake a ransa, ta gefe kuma jinjina wa Jiddah yake yadda ta maze take jefa masu tambaya kawai yake.
Suna cikin dariyar ita ma Jiddah ta tuntsire da dariyar sai su kai shiru suna kallonta da mamakin dariyar me take ita kuma?
Jiddah cikin sautin dariyarta tace, "Wai daman sai da kuka fara makantar da Fatima a gidan nan ashe?"
Su kai tsit, wace irin yarinya ce wannan kuma?
Ta dakatar da dariyarta tace, "Amma kuma nayi mamakin yadda fasahar maidata makauniya ta zo maku amma ta sheƙeta bata zo maku ba kai tsaye sai da dole ku kai mata ƙazafin kisan mijinta. Ko kun ɗauka ta haka ne kawai kuke ga zaku iya halakar da ita?"
Hajiya Turai ta zaro idanuwa ta dubi Hajiya Tani su kai shiru, sai kuma suka miƙe kowacce ta nufi ɓangarenta.
Jiddah sai ta gyara zama tace, "Waye ya gaya maku ana Shari'a da kurma? Waye ya gaya maku ana Shari'a da mahaukaci?"
Tare suka juyo, "To ai Fatima ba kurma bace kuma ba mahaukaciya bace mu ne muka maidata hakan."
Jiddah ta fashe da dariya tace, "Kun kyauta, na jinjina maku ta yadda kuka buga wasanku kuka saka kyautar ku sannan kuka dawo kuka cinye abinku."
Kallon ban fahimce ki ba su kai mata.
Ta sake sakar masu murmushi tace, "A tsarin doka baka shari'a da kurma domin kurma bai cikin cikakkun mutanen da addinin musulunci ya amince su yi waɗannan abubuwan.
1. Shugabanci
2. Limancin
3. Bada shaida a kuto
4. Wakilci
Sannan ina kuka taɓa ji ko ganin inda makaho ya yi kisan kai irin wanda ake tuhumar Fatima da shi?
Don haka Fatima kai tsaye kotu zata sallame ta da nayi niyyar hakan da tuni an sallame ta, sai dai na tsawaita abin ne don kawai na baku damar gyara abin da kuka ɓata, hakan ne kawai zai sa ku samu abin da kuke buƙata."
Ta miƙe tsaye ta dubi Mustapha tace, "Mu je na gama abin da ya kawo Ni."
Haka suka fice suka bar su Hajiya Turai na kallon juna sun kasa furta ko da kalma guda.
Har motarsu ta bar gun, sannan Hajiya Tani tace, "Kin ga mun yi wauta ashe ba a Shari'a da kurma muka rufe mata baki?"
Hajiya Turai tace, "Ai ban san hakan ba da bamu yi ba, amma ko yanzu ai zamu iya gyara wannan matsalar mu buɗe mata idanu da bakinta."
To ko hakan zai sa su cimma manufarsu?
Anya ba shigo-shigo ba zurfi ba Jiddah tai masu ba?
Taku a kullum Haupha ✍️
managarciya