DUHU DA HASKE: Fita Ta 33
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 33*
~kowa ya zauna shiru ana jiran momy da kanwarta suzo kafin aci abinci, sai hararan ameesha suke ta sunkuyar da kai kasa ƙasa take dariya, sun jima a haka kafin momy ta kira wayar ameesha da sauri ta ɗaga tace "momy"
momy tace "gani gata harma mun kama hanyan gida yanzu haka"
tace "masha Allah momy saikun karaso"
jim kaɗan sukaji karan tsayuwar mota, meesha ce ta tashi zata je ammi tace "tsaya mana zasu karaso ai"
batason yiwa ammi musu shiyasa ta tsaya, knocking akayi da sauri tace "hanan jeki ɗauko cake ɗin bara na ɗauko champagne a fridge"
hanan tace "to"
zuwa tayi ta ɗauko cake da ɗan karamin wuƙa na yankawa ameesha kuwa taje ta ɗauko champagne kwalba biyu a hanunta, kara knocking akayi Ameesha ce ta buɗe kofan fuskanta ɗauke da smiling tace "sannu da zuwa..."
kasss kwalaben hanunta suka faɗi kasa suka tarwatse, hanan lekowa tayi dan ganin me ameesha ta gani ta yarda kwalba haka, cake ɗin hanunta ne ya faɗi kasa turus ta tsaya tana kallon kofa cikin shock, tsaye take cikin baƙin abaya da bakin mayafi tayi kyau sosai da kyakkyawan murmushi akan fuskanta tana gefen momy, man dake kallon ameesha yaga jikinta yana rawa yace "wai menene?"
shiru ta kasa magana sai kallonta take, duk suka tashi harda su baba domin ganin me ta gani, ammi ce ta fara yin ido huɗu da ita, man yayi baya baya yana kallonta yace "ma...manal?"
cikin murmushi me sanyi haɗe da zazzaƙan murya me matukar sanyi tace "أنا لست منال، أنا امل"
momy tace "tace sunanta ba manal ba sunanta Amal"
duk a tsorace suke kallonta, cikin yanayin murmushinta ta kalli momy tace "لماذا ينظرون إليَّ باستغراب، هل يعرفونني؟"
cikin mutuwan jiki momy tace musu "wai meyasa kuke kallonta cikin shock kun santa ne?"
shiru sukayi ameesha ta zuba mata ido wannan tsaban farantaka ta koma yellow, gashi kuma tanada ɗan kiɓa tafi manal kaɗan kuma bata jin hausa ko kaɗan daga jin muryanta da yadda take kallonsu kamar bata sansu ba, wannan tanada yawan murmushi dan ko wannan maganan tana yinshi ne cikin murmushi, gata middle class batada aji kamar manal dan wata useless useless ce haka sai uban kyau na asalin larabawa, farin hanunta me ɗauke da dogayen yatsu ta ɗaura akan luggage nata, man ya kalli hanun yaga yatsunta shida ne ma'ana akwai ɗaya karami a gefen na karshen kuma da alama haka halittanta yake
tana murmushi ta kalli momy tace "أستطيع العودة إذا لم يكونوا سعداء أو مرحبين بي"
cikin mutuwan jiki momy tace musu "wai zata koma idan bakwa farin ciki da ganinta"
tayi maganan idonta yana cika da hawaye, da sauri man yace "no ta tsaya"
tsayawa tayi har yanzu babu wanda ya iya magana cikinsu meesha, kallon hanunta yayi ya kalli ammi dasu ameesha yace "wannan yatsunta shida ne akwai wani karami a gefe ita kuma manal yatsunta biyar ne"
ajiyan zuciya suka sauke Imran kam ɓuya yayi a bayan ameesha yaki yadda su kara haɗa ido da ita, idanunta wani kala ba irin namu ba, idan tana kallon mutum kamar mage ne yake kallonka, ta kalli man sannan tayi magana cikin larabci "shi wannan waye da yace na tsaya?"
ta faɗawa momy, murmushi momy tayi itama cikin larabci tace "sunanshi Abdulrahman ana kiranshi da man ko kuma Abdool"
a hankali tace "abdool?"
dara daran idanunshi ya zuba mata jin yadda ta kira sunanshi, duk da baya jin larabci yana iya gane me suke faɗa, murmushi tayi mishi sannan ta miƙa mishi hanu alaman su gaisa, kallonta yake sai kuma ya kalli hanunta, yadda take murmushi kamar sokuwa yasa ya girgiza kai alaman ba zai gaisa ba, cikin mutuwan jiki ta sauke hanu ta kalli Imran daya ɓuya a bayan ameesha ta mika mishi hannu alaman su gaisa, da sauri yace "no...no...no"
tafiya yayi ya bar wajen bai yadda ya tsaya bama, shiru tayi, ameesha ta ɗago cake ɗin da bai gama rushewa ba ta mika mata tana murmushi ta mika mata wuƙan, karɓa tayi ta nuna kanta da larabci tace "wa ni?"
ameesha bataji ba amma yadda ta nuna kanta ya tabbatar mata me take nufi, ta gyaɗa mata kai alaman eh, yankawa tayi ta ɗauko babba ta kai bakin ameeshan, da kyar ta buɗe baki ta karɓa, cusa mata tayi duka ameesha ta fara tari domin har maƙogaronta saida yaje, da sauri ta rungumeta tans bubbuga bayanta tana mata sannu da larabci, hanan ce tazo ta janye ameesha daga jikinta shiru tayi tana kallon Abba ta durkusa kasa cikin larabci ta gaisheshi, amsawa yayi ta gaida baba shima ya amsa, wajen ammi taje ta durkusa da sauri ammi tayi baya, ɗago manyan idanunta tayi cikin innocent look nata tace "ina kwana"
ammi kawar da kai tayi ganin momy na kallonta tace "lafiya"
da larabci itama ta amsa, hanunta momy ta rike taja luggage ɗin zasu shiga ciki, ƙafan hagu ta fara sawa sai kuma ta koma baya tasa ƙafan dama, duk akan idon ameesha, shigowa ciki sukayi tana murmushi tana bin falon da kallo, momy tace "bari na shiga da ita ciki tayi wanka ta canja kaya saimu fito muci abincin ko? kuyi hakuri"
duk sukace "to"
ta faɗawa Amal da larabci, girgiza kai tayi cikin harshen larabci tace "bai kamata su jirani har naje nayi wanka kafin muci abinci ba kamata mu fara ci sai naje nayi wankan"
momy ta faɗa musu abinda ta faɗa, duk suka kalleta a hankali ta sunkuyar da kai, luggage ɗin momy ta shigar ciki sannan ta rike hanunta tayi mata iso wajen dinning ɗin da aka ƙawata da manyan warmer's farare, zama tayi akan kujeran alfarma dake wajen, kujera ɗaya ne tsakaninsu da man, ameesha tashi tayi daga kujeranta ta zauna a kujeran dake tsakaninsu ta fara zuba abinci, kowa yasa abinda yake so, cin abincin suke babu wanda yake magana cikinsu, saide suna yawan kallon Amal data ɗago kai saisu janye ido, ameesha saida taga amal ta tashi tace "Alhmdllh"
kafin itama ta tashi, man kallon abincin da taci yayi, wannan tana cin abinci dayawa sannan tana cin taliya ita kuma manal ko kasheta za'ayi ba zataci taliya ba, ameesha ta ɗibi abinci wa Imran domin tunda ya shiga ciki bai fito ba, Amal hanunta cikin na momy suka tafi ɗaki domin tayi wanka, ammi ta bisu da kallo har suka shiga ciki kafin ta sauke kai akan abincin da take ta juya cokali kawai ta kasa cin komai.
yana zaune a bakin gado yana tattara kaya cikin akwati da sauri sauri yake yi sabida ya samu ya tafi, da mamaki ta aje plate na abincin tace "ina zakaje imran kake haɗa kaya?"
yace "barin gidannan zanyi ba zan zauna tareda wannan ba a gida ɗaya wallahi gara naje nayi rayuwar maraicina yafi min"
shiru tayi tana kallonshi yana shirshirya kayan harya gama taga yasa jallabiya akan gajeren wandon jikinshi yaja akwatin yace "nikam na tafi"
ta kasa magana sai binshi take da ido, ganin da gaske yake ta rike akwatin tace "Imran kayi hauka ne? sabida ita zaka tafi ka barmu?"
tureta yayi yaja sannan ya buɗe kofan ya fita, binshi tayi tana kiran sunanshi, man dake zaune yayi shiru akan dinning yaga imran ya fito da kaya ameesha tana binshi, da sauri ya tashi ya shiga gaban Imran ɗin yace "ina zaka je?"
yace "barin gidannan zanyi ba zan iya zama da wannan a gida ɗaya ba"
man yace "sabida haka zaka tafi ka barmu?"
yace "eh gaskiya gara na rabu da kowa akan na kara shiga rayuwar dana shiga a baya"
ganin yana jan akwatin man ya rike, ja ya fara da karfi yace "ka sakemin kayana wallahi ba zan zauna ba, ka sakemin nikam"
man cikin ɓacin rai ya wankeshi da mari yace "sabida ita zakayi nesa da yayanka?"
dafa kunci yayi yana kuka yace "ba gashi ba tun yanzu ka fara marina tun zuwanta gidannan wallahi ba zan zauna ba"
rungumeshi man yayi yace "dan Allah kada ka tafi ka barni a baya nayi rayuwa babu kai banji daɗin komai ba, kaga itama ameesha ba zataso ka tafi ba kaga kuka ma take yi ko? bakason ganin aurena da ameesha ne? bakason kaima ka zama baba? idan ameesha ta haifamin yaro kaima ai ka zama baba ko? nasan ko bana nan koda na mutu zaka kulamin da ɗana sosai kamar ina raye, idan ka tafi ya zanyi ɗana zai tashi babu kankn babanshi ya gudu ya barsu"
cikin lallashi yake maganan, cikin hawaye Imran yace "to unty ameesha tana da cikin ne? saina jira idan ta haihu saina ɗauki yaron mu tafi"
murmushi man yayi ganin har yanzu Imran ya girma amma babu wayo taya zatayi ciki basuyi aure ba?
yace "a'a bata dashi amma ai nan da wata ɗaya zatayi ciki idan munyi aure"
ameesha rufe ido tayi cikin jin kunyan maganan da yake yi a gabansu abba, Imran yace "to amma idan ta haihu zaku bani yaron na tafi dashi?"
man yace "eh"
alama ya yiwa yazeed ya ɗauki akwatin ya mayar ciki, murmushi yazeed yayi sannan ya riƙe hanun Imran yace "taho mu koma ciki kaida tafiya saika zama baba"
ajiyan zuciya me nauyi man ya sauke ganin ya yadda ya koma, ameesha tace "kaina ya kulle na rasa meke faruwa"
ammi kam tafiya ciki tayi, hanan ma dasu Abba duk suka tafi suka barsu a wajen, man ya matso kusa da ita yace "ki kwantar da hankalinki wannan ba manal bace domin naga bambanci sosai yatsun wannan shida ne kinga kuma halittan Allah ne, sannan wannan batajin hausa kuma bata iya turanci ba ko kaɗan, ita kuma manal bata jin larabci sai turanci da hausa, wannan tana cin taliya ita kuma manal ko kasheta za'ayi ba zataci ba, sannan wannan kamar batada isasshen wayo ita kuma manal kana ganinta kaga wise"
harara ta ɓalla mishi cikin yadda dashi tace "wato wise ko?"
yace "bada manufa na faɗa ba"
tace "gashi ka faɗa"
duka zata kai mishi a kirji ya kauce, da gudu ya bar wajen binshi ta fara suna zagaye falon yace "kiyi hakuri please"
throw pillow ta ɗauka ta wurga mishi, dafa kai yayi yace "wayyo da zafi"
ɗauka yayi shima ya saita kanta ya wurga durkusawa kasa tayi ya wuce ta kanta caraf Amal data fito daga ɗaki yanzu ta cafke, wasa dashi ta fara a hanunta tana kallonshi, ganin ameesha ta durkusa itama alaman bataso ya taɓa ta tana kallonta, ɗagawa tayi ta saita akanshi tana dariya, rikewa yayi ya aje a gefe sannan ya juya ya tafi, jikinta yayi sanyi ameesha ta gane haka a hankali ta tashi taje tana kallonta, tayi wanka tasa abaya baƙi da fari fari a jikin hanu da wuya, ta nuna mata wajen zama alaman ta zauna zama tayi tana kallon ameeshan, murmushi tayi mata itama ameesha tayi mata murmushi, ameesha batajin larabci ita kuma batajin hausa da turanci sai murmushi suke yiwa juna, hanan data fito daga ɗaki yanzu ta watsawa Amal harara sannan taja hanun Ameesha tace "kinga tashi muje kin zauna kusa da ita kina wani sakar mata fuska, wallahi ba dan momy ba saina koreta a gidannan"
ameesha tace "zauna mana hanan wannan da manal bace wannan Amal ce bakiga banbanci sosai ba? kinga wannan akwai kyawawan hali da ganinta ita kuma wancan kina ganinta kinga muguwa"
Hanan tace "tun ina karamar yarinya na tsani irin wannan fuskan tunda ta konamin teddy a school wallahi ko kallon irin fuskan banson yi, ko itace ko ba ita bace wannan matsalatarta ce ni dai ki tashi mu tafi ɗaki banson ganinku tare, kin san Allah har ita momy ba sonta nake ba yanzu sabida tana min kama da manal"
Amal sai kallonta take tana mata murmushi da alama batasan ma akan me take magana ba taji dai tace momy kuma tasan unty rukayya ce momy, tashi ameesha tayi tabi hanan suka tafi ɗaki ba dan taso ba, zama tayi akan sofa, hanan ta zauna a gefenta ta kwantar da kanta a cinyarta tace "kinada saurin yadda"
murmushi tayi ta janyo laptop ta fara danne danne, sallama sukaji kuma muryanta ne, ameesha ce ta amsa, a hankali ta tura kofan ta shigo, a bakin kofa ta tsaya tana wasa da yatsanta da alama so take su zauna tare, hanan zatayi magana ameesha ta rufe mata baki ta yiwa amal alaman ta zauna akan gado, a hankali ta karasa ta zauna a bakin gado tayi shiru tana kallon ɗakin, cikin nutsuwanta ta kalli takadda dake kan gadon ta ɗauka tana dubawa, murmushi take yi ita kaɗai tana karanta takaddan ganin akwai larabci da hausa da kuma turanci yasa take fahimtan na larabcin, kallonta ameesha tayi taga yarinyar kamar abin tausayi gata kamar wacce ta girma a takure akwai tsoro a tare da ita, suna ɗakin har lokacin salla yayi gani sukayi ta tashi ta shiga toilet tayi alwala, zuwa tayi ta shinfiɗa sallaya ta fara salla, koda ta idar a fili take addu'a hanunta a sama tana rokon Allah da kyakkyawan larabci, jikin hanan ya fara sanyi ganin tana addu'a tana kuka da alama an cutar da ita kamar yadda momy ta faɗa.
Ammi tana zaune akan gado gefenta baba ne tayi shiru da alama nasiha yake mata
"ki kwantar da hankalinki mana salma idan ma itace ai zamu gane a hankali bale ma wannan ba ita bace sabida akwai banbanci sosai, sannan faɗawa su Ameesha zaisa hankalinsu ya kara tashi kinga su yara ne, ya kamata ki rike a ranki koda kina jin cewa ita ɗince, amma idan kika faɗa musu me akayi kenan? kawai de kisa ido sosai kada ki rinƙa barinsu ba tareda kin san me suke yi ba"
a hankali tace "amma fa kasan wahalan da mukasha akan manal sannan kasan yanzu haka auren ameesha da man saura sati uku ne kada fa wani abin ya faru ya hana auren kaga yarannan suna matukar son junansu musamman man da yake kasa ɓoye soyayyan da yake mata, shaƙuwa fa ba wasa ba, banso wani abu ya hana wannan auren, da tazo bayan aurenne gaskiya da yafi"
baba yace "babu komai addu'a yafi karfin komai mu iyayensu mu dage musu da addu'a babu abinda zai faru, duk inda iyaye suke yiwa ƴaƴansu addu'a to yana biye dasu insha Allah"
a hankali tace "to shikenan zanyi kokarin dannewa"
yace "to salmata yimin murmushi"
murmushi tayi mishi ya fara share mata hawayen haɗe da janyota jikinshi, Imran ne ya turo kofan sai kuma ya juya baya yace "sorry ban san kana nan ba"
zai fita baba yace "dawo Imran"
a hankali ya juyo baba yace "zoka zauna"
zuwa yayi ya zauna a kasan gadon kanshi kasa yace "gaskiya baba ina tsoro"
ammi ta sauko a gadon tayi hugging nashi tace "haba mana Imran kana namiji kana tsoron mace? bale ma wannan ba manal bace, manal nice na riketa tun tana ƴar karama da itace nice farko da zan fara ganeta, amma kaga wannan akwai banbanci sosai kama ne kawai amma ba sosai ba ga wanda ya kula"
yace "da gaske ammi?"
tace "eh mana jeka kara kallonta wannan ma basuyi kama sosai ba a ido ne kawai zaka ga kamar suna kama"
sai yanzu ya sauke ajiyan zuciya yace "yawwa ammi sai yanzu naji sauki a raina"
tace "karka damu"
tashi yayi yace "bari naje na maida kayana cikin wardrobe"
tace "good boy jeka"
tafiya yayi, ta kalli baba tayi kalan tausayi tace "kenan haka zan rinƙa musu karya ina kwantar musu da hankali?"
yace "bakida tabbacin karya kike musu dan har yanzu baki tabbatar manal bace"
tace "haka ne kuma"
Imran yana tafiya yana murmushi harya koma ɗakinsu ya fara maida kayan cikin wardrobe man da ameesha ne suka shigo suna kallonshi ya gama maida kayan, juyowa yayi suka haɗa ido man yace "ka gama?"
yace "eh"
ameesha tayi kamar zatayi kuka tace "dama dama munzo mu faɗa maka wani magana ne"
a tsorace yace "magana name?"
tace "dama wannan itace manal"
a mugun firgice ya koma zai fara tattara kayanshi ameesha ta rungumeshi ta baya tace "kai matsoraci ba gaskiya bane ba ita bace"
fahad dake kan gado yace "gaskiya anty ameesha wannan yarinyar batamin ba gaskiya nima a tsorace nake"
zaunar da Imran tayi a gefen gado sannan suma suka zauna da man, hanunshi ta rike tace "Imran meyasa kake tsoron mace haka? kasan idan kana tsoro babu abin kirki da zakayi? wannan ba manal bace wannan ameesha ce amma hakan ba zai hana musa mata ido sosai mu san duk wani motsinta a gidannan ba, idan har mukace zamuji tsoronta to zataci galaba a kanmu amma idan muka haɗa kai ba tareda ta sani ba zamu gane ko wacece ita, dani da kai da fahad da man...."
hanan ce ta turo kofan tace "dani da kuma ya yazeed"
shima ya shigo yayi kyau cikin baƙin singlet da wando three quarter, murmushi ameesha tayi tace "kaga mu shida ita kuma ita kaɗai, bama mu shida ba nasan har ammi ba zata daina sa ido akanta ba kaga mun zama mu bakwai, ba lalle mutum ɗaya taci galaba akan mutum bakwai ba, ya zama dole kowa yasan yadda zai zauna da ita, hakan ba zaiyi ba har sai mun shaƙu da ita ma'ana mu jawota jiki kada mu nuna mata akwai wani abinda ya taɓa faruwa tsakaninmu da manal, sabida naga kamar momy ma bata gaya mata komai ba"
man yace "to waye zaifi kusanci da ita domin ya gane mana ita wacece?"
kallon Imran sukayi su duka, dafa kirji yayi idanunshi a waje yace "ni kuma me yasa kuke kallona?"
duk sukace "kaine zaka zama na kusa da ita"
yace "wallahi na rantse da girman Allah ba zan iya ba, kuna gani fa sharrin fyaɗe fa tamin nida ban san yadda ake s*x bama tace na mata fyaɗe to idan ta kara min wani sharrin fa?"
abdool yayi dariya ganin yadda kanin nashi ya ruɗe, meesha tace "to shikenan tunda a tsorace kake bari mu canja"
kallon fahad tayi yace "wallahi A,a nima tace nayi mata fyaɗe azo ace da gaske"
dariya man yayi sosai a wannan karon harda rike ciki, ameesha ta ɗan bigeshi tace "ba dariya zakayi ba solution zamu nema"
man yace "to ko dai ni...."
Ameesha tace "no ban yadda ba"
yazeed ya kalleshi ganin yana dariyan tsokana yace "ni zanyi"
duk sukace "good kaine daidai amma kayi a hankali karka faɗa love"
cewar man, yayi tsaki yace "ko mata sun kare zanyi soyayya da wannan me kama da wacce ta jefa rayuwar kowa cikin masifa ne? naje na kasa bacci kullum ina cikin fargaba"
hanan tace "dan Allah yaya kasan yadda zakayi kada ka faɗa sharrinta ka rinƙa kulawa sosai banason wani abu ya sameka"
yadda hanan take sanshi yana ji a ranshi ba zai taɓa bari komai ya sameshi ba, yana hango tashin hankali a idonta idan taga yana cikin damuwa ko rashin lafiya, murmushi yayi mata yace "karki damu babygirl"
tace "to yaya"
_Jiddah Ce....
managarciya