Haɗin Allah:Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Biyu
Page 12
Na ɗago kaina fuskata cike da al'ajabi da matuƙar mamaki na sauke su kan Safiya dake tsaye tana ta washe min baki, "Wai baki jin nauyin cikin nan kike shara haka? Gaskiya ki rage aikin wahala saboda gun haihuwa ake gudun wahala." Cewar Safiya tana kallon cikina. Baki ɗaya sai na samu kaina da rashin sanin me zan ce mata, ashe rashin kunyar ba Deeni kawai ya iya taba, har ita ma ƙawar tawa tayi digiri akan rashin kunyar. Bakina ya yi min nauyi don haka da ido kawai nake bin ta, cike da jinjina ma ƙarfin halinta, shin bata gudun abin da zai je ya dawo tsakaninmu? Bata tunanin har yanzu ina riƙe da ita a cikin zuciyata? Ko gani tai kashin dankalin yafi ƙarfin kuɗina ne don haka ta sake biyoni gidana a gaban idona?" Sai ta nemi waje ta zauna bakin simintin shiga ɗakina.
Ina tsaye ni ban ci-gaba da shara ba, ni ban yi mata magana ba, to ai duk wata jijiyar dake bada gudummawar yin magana ta jikina ta daina aiki tsabar mamakin zuwan Safiya gidana cikin kwanciyar hankali da natsuwa, sai washe baki take tamkar lokutan baya, da muke rayuwa cikin duhu Ni da ita, ban san wainar da suke toyawa ba ita da Deeni. Tsam ta miƙe ta shige ɗakin, duk dai ina tsaye tamkar an dasa ni inda nake tsaye da tsintsiya a hannu baki sake kamar benten Sakarya.
Ta ɗan jima kafin ta fito da takalmina fari da jakarshi tana saka farin gyalensu cikin jakar tace, "Kin ganni nan wallahi biki zan je nace bari na zo na ɗauki jaka da takalma farare don da su zan je." Tabbas idan baka san bariki ba, an barka Tasha, baki ɗaya sai ta halakar dani ma na rasa tudun dafawa. Anya kuwa akwai wanda ya ɗauke ni marar wayau da rashin sanin ciwon kanta irin Safiya? Yau fa kwana uku kacal da ganinta da mijina cikin gidan nan amma ta sake dawowa da fuskar abota gare Ni?" Ban kai ga magana ba maigidan ya shigo, ina kallonsu suka dubi juna suka saki murmushi, karaf naji tace, "Har ka dawo kenan? Amma baku ma jima ba, ina ka baro Nasirun?" Kamar a Film haka naga Deeni ya saki murmushi yana kallonta yace, "Ashe nan kika yo na kira wayarki ai bata shiga ba, na je gidan kuma kai maki kankanar da kika ce na taho maki da ita baki nan, tana bayan mashin ɗin Nasirun na barta da dare sai na kai maki." Ina dai ta ganin ikon Allah ni Jiddah sai ita ma tace tana dariyar da ji ta rainin hankali ce, "Ka manta na gayama zan sai da wayar nayi kuɗin motar zuwa bikin ƙawata Sadiya ne Ɗan'agundi? To can zan tafi ai, dama na biyo ne nayi mata ta'aziyyar rashin daka ce anyi mata ne na kuma ari waɗannan kayan gunta." Ai sai kawai na yada tsintsiyar na zauna daɓas ƙasa ina sauraren yadda da tsinin tsiya suke so su taru su halakar da ni lokaci guda. Ya ɗan kalli jakar kayan yace, "To ke akwai aro ne tsakaninku? Kawai kice kin zo ɗaukar kayan da kike son amfani dasu kawai zan fi ganewa miye abin kiran aro a ciki? Kawai ki ɗauka na baki daman ba wani iya sasu take ba da wancan uban cikin." Ya watsa min hararar da na kasa gane da ni yake ko da cikin yake. Ta wuce gaba ya bita baya tana cemin sai ta dawo, har za su fice ta dawo cikin gidan tace mai, "Don Allah kaban aron wayarka nayi kira kar da naje bata nan inda zan fara zuwan." Cike da fara'a ya fiddo wayar ya miƙa mata yana cewa, "Ɗazun kuwa akai min tallar wata waya, ki ban sim card ɗin kawai na je na amshi waccan sai na tura maki kati, ai ba a tafiya babu waya yanzu." Zuwa yanzu abin nasu ya wuce halakarwa ya koma lumarwa don haka nayi gyaran murya don ya tuna wayata ce zai kyautar ba tashi ba. Ya watsa min harara yace, "Ke dai kin shiga uku da mugun hali ƙawar taki ma jin zafi kike mata don zan bata wannan wayar?" Girgiza mai kai nayi kawai na sadda kaina, ina gani ta cire sim card ɗinta ta ba shi nashi ta fice da wayar tana cewa kar tai dare ya zo su je ya bata kankanar.
Sharar da ban ida ba kenan na shige ɗaki na dasa sabon kuka ina jin matuƙar ciwo a cikin zuciyata, kaina na matuƙar sarawa,ji nake tamkar na haɗa kayana nabar gidan, to amma idan nabar gidan ina zan je? Shin da wannan cikin wa zan nufa? Mamana na cikin yanayin rashin mijinta, sai wa ke gare Ni? Allah Sarki Alawiyya ina fatan baki kasance yadda na kasance ba, ina addu'ar Allah Yasa kin ga iyayenki."
Haka nan na ida kai dare cikin mummunan yanayi, har lokacin da sha biyu na dare ya buga, Deeni ya shigo gidan yana jin waƙa. Kamar yadda na yi tsammani haka ya faru, ko kallon inda nake bai yi ba,ya wuce cikin ɗaki yana waƙarsa. Bai jima ba ya fito da robar dana kwaɓa fulawa yace, "Wane sabon rashin mutunci ne wannan na kwaɓa fulawa ki barta haka nan? Saboda baki san zafin nema ba ko? To wallahi dama kin tattala domin ban yarda da almubazzaranci ba, ko da yake kin kusa haihuwa a kawo wani daga gidanku ai." Cikin muryar data sha kuka nace, "Tun ɗazun na kwaɓa zan toya ta amma ba manja kuma kuɗin da zan siyo ne ka ɗauka duka ka fice." Taɓe bakinsa ya yi ya koma ɗakin kamar bai ji me nace ba.
Washegari tunda safe na shirya nace ma Deeni zan je wajen zaman ta'aziyyar Baba, amma ya ɗago kai cikin alamar barci yace, "Ban ce ba, kuma ki fice mun daga nan kafin na ɓata maki rai." Ƙafafuna kasa ɗauka ta su kai don haka nayi jim tamkar ba zan tafi ba, ya sake buɗe ido ya kalleni a ƙufule yace, "Ke wai mi kika taka ne kwanakin nan naga kina neman kawo min sabon raini? Na rantse sai na ɓata maki rai fiye da zatonki, ke daga Yau ma na hanaki fita ki ci-gaba da zama cikin gidan ki dinga ganin ƙul uwar daka, kin san dai baki isa ki hanani yin duk abin da naga dama ba, kuɗina ne gidana ne ba uban da ya cika mun lokacin dana siya." Dole na ja ƙafafuna da tsiya nabar gun zuciyata na ƙuna. Ganin ba abin da zan na fita na fara sharar tsakar gida, na gama tas na fitar da kayan wanke-wanke na duk da wankakkune kawai sun jima ne duk sun ƙura ga rashin madafa yasa na ci-gaba da wanke su. Tsab na gyara gidan na koma na share falon na goge na kunna tsintsiyar ƙamshi na wuce ƙurya na fara kaude-kaude ina kakkaɓe-kakkabe na gama na ɗauko tsintsiya na fara shara Deeni ya ja uban tsaki, "Kai Allah Ya kyauta kin yi dace da mugun hali wallahi, don munafurci baki tashi shara na lura kullum sai ina barci kin dinga taɓa nan taɓa can, don kina baƙin ciki da barcina."
"Kai haƙuri, gani nayi tunda ba inda za ni gyara ko gidan na gyara yafi zaman haka nan ɗin." Wani tsakin ya sake ja ya ja zanin gado ya sake lulluɓewa. Ajiyar zuciya na sauke nace a raina "Oh ni Jiddah ina ganin rayuwa! Na samu dai na gama sharar na kunna tsintsiyar ƙamshi ɗakin na fice zuwa falo ina jin ciwon kan nan daya ƙi sauka yana addabata. Zuwa yanzu na saba da damuwa da ciwon kai, ban da wahalar zubowar hawaye, hatta cikina na kalla hawaye zubo min suke, tambayar kaina nake "Yanzu duk abin da na haifa haka zai taso cikin wannan ƙuncin rayuwar? Yanzu haka zai ganni kullum sai nayi kuka? Me zan gaya ma shi ranar da ya tambaye ni kukan me nake?" Tambayoyi da dama ke damuna a duk lokacin dana zauna. Yau kwana biyu da rasuwar mijin Mama amma tun da naje sau ɗaya ban sake zuwa ba, yanzu idan da ace Babana ne hakan zan yi?" Daram! Gabana ya faɗi jin sunan Babana a cikin tunanina. "Babana! Tabbas ina da Baba kuma a raye amma yana ina? Wane laifi nayi ma shi wanda yasa bai amshe ni matsayin ɗiya? Me yasa sam bai damu da ni duk wasu lamurrana ba?" Hawaye masu ciwo suka zubo min ina son Babana duk da shi bai sona, amma ina jin son shi a raina sosai, duk lokacin da naga Uba da ƴaƴansa birge ni suke musamman mata, yaushe ne zan rayu cikin farin ciki da Babana? Me yasa har yanzu bai zo gidana ba duk da cewar an ce ya zo garin kuma an gaya mai nayi aure amma sam bai damu da zuwa inda nake ba, wane irin Uba ne Allah Ya ban ?
Ina zaune ya fito zai wuce na dube shi cikin ƙarfin hali nace, "Ka manta baka ban kuɗin kalaci ba." Idan ya tanka bangon dake ɗakin ya tanka ya wuce bai ko waigo ba.
Ƙarfe goma cikina ya dinga wutsilniya yunwa tai min dirar milikiya na kasa tsaye na kasa zaune, ganin yunwa na neman illatar da Ni na hura wuta na zuba ruwan zafi, suna tafasa na ɗebo fulawa na kwaɓa kamar zan koko na dama, ban san ko zai ba ko ba zai ba, ni dai na dama kawai don kar yunwa ta kashe Ni, babu sukari haka na zauna na sha kunun na cika cikina na shimfiɗa tabarma ƙofar ɗakina na zauna na buga uban tagumi ina tunanin da rana kuma me zan ci? Anya kuwa zan iya wannan rayuwar ta zaman yunwa ga ciki? To idan ban iyawa ina zan je? Sallamar yaran makwabtan Mamarmu ne yasa na ɗaga kai na kalle su, ɗauke da kwanon abinci suka aje gabana suna gaidani, "Ga shi in ji Innarku tace ai maki ya jiki, kuma ya jikin naki?" Allah Sarki Mamana! Abin da nace a zuciyata kenan, duk da halin da take ciki hankalinta na kaina. Allah bai barin bawa a mugun hali, yanzu nake tunanin me zan ci idan rana tai sai ga abinci daga gunta, alhamdulillah! Nan suka wuni har yamma sannan suka tafi. Naji daɗin zuwansu domin damuwata ta rage sosai.
Sai dare ma na ɗauko abincin zan ci kenan Deeni ya shigo,sai da gabana ya faɗi, ya kalleni ya taɓe baki ya wuce ciki, zuwa can ya ƙwaɗa min kira, "Ke! Cikin yanayin tashin masu ciki na ɓaɓbaka da ƙyar na shiga gunshi.
"Ke wai mi yasa baki san kanki ba? Ina nawa abincin to? Allah ki guji ɓacin raina a gidan nan." Mamaki ya hana ni magana na saki baki ina kallonshi baki buɗe, yaushe ya kawo abincin da zan ba shi, fulawa ce kawai a gidan ko gishiri babu a gidan amma zai ce in ba shi abinci? Cike da ladabi nace "Ai babu komai a gidan na fadawa sai garin fulawa nayi maka magana baka bada ba." Ya wani zaburo kamar zai mare ni yace, "To ke daga ina kika samu wanda naga kin baje cikinki kina ci?" Kaina ƙasa nace "Mama ta aiko min da shi ɗazun." Ya jima yana kallona kamar mai nazari sai kuma yace, "Amma kin cika muguwa wallahi yanzu Innarku ta aiko da abincin ki kasa ban? Kina nufin ke kaɗai ta aiko mawa ko me? Dilla je ki kawo min nawa na ci na fita Ni."
Haka na juya ina tunanin in kai mai abincin ko kar in kai mai? Amma dai ƙarshe na ɗauki abincin na kai mai ba don na ƙoshi ba, sai don na huta da masifarsa.
Haka nayi ta rayuwa daɗi ba daɗi, har akai kwana shiga da shiga tashin hankalin rayuwata, ranar Talata sati guda da faruwar komai da dare ciwon ciki ya turnuke Ni, wanda ban taɓa jin irinsa ba, mara ta ma tai ta yamutsata na rasa gane kalar ciwon da nake ji. Ganin na kasa jurewa na rarrafa na shiga ƙurya na tada Deeni dake barci na gaya mai ban lafiya.
"To ni me zan iya maki don kin gaya min?" Ya gyara kwanciyarsa ya ci-gaba da barci ya barni tsugunne gaban gado ina Salatin Annabi.
Can dai ko komi ya gani ya dube ni yace, "Ki koma falo mana kin dame ni da Salati kan kunne." Cikin azabar ciwo nace, "Don Allah ka kira min Mama kar in mutu don Allah! Tamkar ba da shi nake ba, haka ya yi, da rarrafe na koma falo na rasa damuwata na rasa jin daɗi ji nake tamkar mutuwa zan, Salati nake ina ƙarawa iyakar ƙarfina.
Ina cikin yanayin ya fito yana ta tsaki ya raɓa ni ya wuce sai dai naji ƙarar buɗe gidansa. "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un!!!
To masu karatu mu haɗe shafin gaba don jin yadda Jiddah zata ƙare ga shi dai ita kaɗai cikin gida ga ciwon nakuɗa, kuma haihuwa farko.
Daga taku a kullum Haupha.
managarciya