HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 33
A motar kowa kallon Jiddah yake, har wasu na tunanin ko dai mutuwa akai mata ko kuma mijinta ya sake ta idan tana aure, hakan yasa.
Mustapha jin kukan Jiddah yake tamkar zubar ruwan dalma a rauninsa. Ji yake tamkar ya janyo ta jikinshi ya lallashe ta , baki ɗaya ya rasa sukuni ko jin daɗi, so yake ya lallashe ta amma ya rasa da waɗanne kyawawan kalmomi ne zai lallashe ta. Hakan yasa ya kife kansa shima ya kama kukan, domin suya zuciyarsa ke yi ba kaɗan ba.
Tashin hankali yake shiga ko a tunani ya hasaso Jiddah a damuwa balle yanzu da take gabansa yana kallonta tana kuka mai cike da damuwa.
Sosai yake jin ina ma ace tana matsayin matarsa ne akai hakan, tabbas da har su isa Kaduna tana lafe jikinsa yana lallashinta da gaya mata kalaman soyayya waɗanda za su saka mata natsuwa ko ya ya ne a zuciyarta.
Hawaye yake sosai duk lokacin daya kalleta yaga nata hawayen sai nashi hawayen sun zubo.
Jiddah kamar ance ta kalli kujerar da yake sai taga yana kuka abin da ya tsaida nata kukan kenan ta tambaye shi da muryar kuka abin da ya sa shi kuka.
Cikin raunanniyar murya ya ce mata, "Na rasa yadda zan yi na lallashe ki ne, don haka kukanki ke sakani kuka nima, wallahi ban so na ganki a damuwa ko naga ranki ya ɓaci sai naji nima nawa ran ya ɓaci ko naji damuwa fiye da taki damuwar ma. Don Allah ki yi haƙuri ki daina kukan nan tunda dai kin gano inda take insha Allah ita ma Mama zata kuɓuta domin ina ji a jikina Alawiyya ba zata taɓa bari a kada ta a shari'ar mahaifiyarta ba. Anya kuwa kin san wacece Barista Alawiyya akan aikinta kuwa? To ita ɗin ta shahara tayi ƙaurin suna kan kada duk wanda ya ja da ita a Shari'a kowace irin Shari'a ce kuwa don haka ki daina damuwa insha Allah muna zuwa nasan komai zai daidai."
Magana yake mata cikin natsuwa da lallashi, sai ta samu kanta da sauke ajiyar zuciya akai-akai. Hannu yasa ya goge mata hawayen fuskarta ya sakar mata murmushi cike da son kore mata damuwa ya ce, "Wai me yasa wasu matan ke ƙara kyau idan suna kuka ne?" Bata san lokacin da dariya ta suɓuce mata ba,ta ce cikin dariyar, "Au dama kuka kyau yake ƙarawa? Ai ban da labari gunka ne Yau farkon jin wannan sharhi na masu kuka to."
Har zuwa yanzu kallonta yake, kallo mai cike da ƙauna da soyayya ya sake murmusawa ya ce, "Ke ba fa wai gane wa nake ba a sauran matan, ke ce dai na lura da hakan gunki a Yau don haka nayi tunanin akwai wasu matan ma masu wannan baiwar kyan idan suna kuka."
Tana lura da har matar dake gefenta sai da tai murmushi jin maganarsa.
Ganin ta kasa magana sai kuma ya ce, "Kin san wani abu ma dake ban mamaki gare ki? Ko da yaushe fara'arki ƙara yawaita take alamar cewa ke baki san Buhari na mulkin Nigeriya ba ko?"
Dole ta sake yin dariya tace, "Kana dai zolaya ta ne kawai, amma ɗan makaranta ina shi ina wani jin daɗin rayuwa balle har aje matakin daka aje Ni."
Matar dake zaune ta kasa haƙuri ta dubi Jiddah tace, "Baiwar Allah gaskiya mijinki na sonki idan fushi kike da shi ko wani abu ya yi maki ki danne a ƙasan zuciyarki domin samun najimi mai ba mace kulawa irin wannan matuƙar wahala yake a wannan lokacin , ke kin samu naga kina son wasa da damarki don Allah ki gyara yarinya kafin lokaci ya ƙure maki."
Kunya ta kamata, domin dai ga dukkan alama ya ji abin da matar tace don sai murmushi yake yana basarwa.
Cikin in'ina tace wa matar, "Ayyah ! Ai ba mijina bane ba, shi ɗin Uncle ɗina ne ko kuma Yayana."
Matar ma murmushi tai, "To gaskiya indai haka ne yana matuƙar ƙaunarki sosai yadda har hakan ya gaza ɓoyuwa ga idanun mutane. Shawarar da zan baki ita ce kar da ki rasa wannan ɗumbin ƙaunar yarinya."
Yau tana ganin ikon Allah! Haka kawai mace daga ganinsu tare sai tace wai soyayya? Ita kam ko kalmar so bata son ana gaya mata, ji take da tana da iko ko damar dakatar da soyayya da yanzun babu mai sake ambatar soyayya a wannan lokacin, don haka sai ta ja bakinta tai shiru kawai fuskarta ba yabo ba fallasa.
Shi kam Mustapha ji ya yi idan ba kyauta ya yi ma matar ba, zuciyarsa ba zata sarara ba, daga tsabar jin daɗin abin da tai mai ba, yana cikin jin daɗin aka tambayi kuɗin mota sai kawai ya bada hada na matar tunda wannan ce hanyar da kawai zai iya bata tukuicin maganarta.
Saboda haka sai kawai Jiddah ta janyo wayarta ta fara latse-latse kai tsaye sai kuma ta rubuta sunan Alawiyya ta shiga cikin page ɗinta.
Ta cigaba da karanta abubuwan da suka shafi Alawiyyar tana jin tsantsar farin cikin cewa rayuwar Alawiyya ta yi kyau bayan rabuwarsu, har ta ga inda Alawiyya ke cigiyarta da sunan ta da ɗan wani labari na su wanda zai sa ta gane da ita take.
Hawaye suka zubo mata, "Tabbas ta ji daɗin ganin Alawiyya a matakin da take yanzu, ba mamaki ita iyayenta ba su yi mata yadda nata iyayen su kai mata ba, n yi mata auren wuri ba tare da tayi ilimi mai zurfi ba, ko da yake ai ita Alawiyya daman iyayenta suna sonta kawai ƙaddara ce ta raba su, tasan kuma ita ce ta sake haɗa su har su kai mata jagora ta zama abar alfahari ga jama'a.
Ganin ta koma kukan sai ya ji nashi hawayen sun dawo, ko da wasa bai son ganin damuwa a fuskarta, yana son kallon murmushin nan nata da ko da yaushe yake kan fuskarta.
Alƙawarine ya yi ma kansa duk ranar daya aureta ba zai sake barin hawayen damuwa, ko baƙin ciki zubowa daga kyakkyawar fuskarta ba. Sai dai ko yanzu yana so ya zama babbar katanga mai kange mata zubowarsu amma ta ya zai hakan? Sosai ya yi zurfi a tunanin hanyar da zai bi ya jefa natsuwa da walwala a fuskarta, don har ga Allah ji yake ya fita shiga cikin mayuwacin halin da take ciki, zafi sosai zuciyarsa ke yi, ƙuna yake ji duk sadda hawayenta suka fito ji yake tamkar ana yankan naman jikinsa ko ana gasa zuciyarsa da garwashi.
Jiddah kuwa tai nisa a tunanin Alawiyya sai ta samu kanta da tuno rayuwarsu ta baya, komai ya dawo mata dalla-dalla a cikin zuciyarta. Kawai sai ta tsinci zuciyarta da hasko fuskar mahaifinta, rabon da ta saka shi a idonta tun ranar data haifi su Afnah bata sake ganin sa ba.
Ita kam tasan cewa tafi wani marayan maraici indai akan Uba ne, domin ita nata Uban sam bata ma san inda yake ba balle ace tasan ya yake ba, tana son ko a mafarki ne ta ganta da mahaifinta suna wasa da dariya ta ganta zaune suna magana ba ta faɗa ba, babu zagi babu tsangwama tabbas a ranar da sai ta yi sadaka ta godiya ga Allah, amma abin da yafi ƙarfinta ko a mafarki kenan. Wasu hawayen suka sake zubo mata masu ɗaci wai yaushe ne zata daina hawaye a rayuwarta? Yaushe ne zata daina baƙin ciki a rayuwarta? Allah Sarki Uncle Salim kai ne kawai mai fahimtar damuwa ta ko da ban ce mai komai ba, yakan fahimci abin da take buƙata ko da bata nuna a fuska ba, yakan nema mata mafita kan hanyar data shige mata duhu ko da tai nisa hanyar yakan gajarce mata ita.
Uncle Salim shi ne kawai mai mata albishir da alheri da abin alherin gareta, shi ne ko da yaushe bakinsa na kanta, ko da yaushe shawara yake bata ta tsaya da ƙafarta ta tsaya ma rayuwar yaranta ta zama jaruma jajirtatta kan lamarin ta dana yaranta duk rintsi ta tsira da abu biyu zuwa uku a rayuwarta, karatunta, karatun yaranta, sai kuma sana'a to tabbas ba za ta taɓa wulaƙanta ba.
Shi ne wanda ya biya mata komai na karatunta kamar yasan zai tafi ya barta ya ajiye mata kuɗaɗen da zasu isheta karatunta a bankinta, bata mance ba ya matsa mata kan maganar buɗe banki ya takura mata sai da ta buɗe bankin ashe don ya saka mata kuɗin da zatai karatu da su ne. A fili ta dinga cewa, "Allah ka jiƙan Uncle Salim ɗina, ka gafarta ma shi, kasa ya huta. Allah ka azurta shi da jin daɗin zaman kabari kasa yafi jin daɗin can fiye da yadda ya ji daɗin rayuwar duniya." Kuka take sosai wanda sai da mutanen gun suka dinga yi mata magana kan tai haƙuri, domin yanzu sun fahimci rasuwa ce akai mata jin addu'ar da take ta yi da ƙarfi.
Shi kanshi Mustapha sai rayuwarsa da Salim ta dawo mai sabuwa a ransa.
Duk da sun kasance ƴan'uwa ne na kusa kuma sa'annin juna to akwai wata shaƙuwa ta musamman dake tsakaninsu, domin ba su ne kawai kai guda ba a cikin dangin nasu ba suna da yawa waɗanda suke kai ɗaya amma basu shiri kamar yadda suke shiri da Salim kaf dangin nasu, ko da yake a gidansu Salim ɗin ma su huɗu ne maza amma da Salim kawai yake shiri. Salim mutum ne mai hangen nesa da sanin ya kamata, bai mantawa duk lokacin daya fuskanci yana cikin damuwa yakan zauna ya dinga ba shi haƙuri ya ce mai, "Musty kana ban mamaki idan kana damuwa da sabgar mata, su fa mata baki ɗaya idan ka fahimce su zama da su sai ka iya haƙuri da kau da kai, sannan sai ka zama shasha gare su, ka zama tamkar ƙaramin yaro wanda komai zai yi sai da shawararsu,amma kai ka kasa fahimtar hakan. Musty dole ne idan kana son farin ciki gidanka kaima ka zama farin cikin ma'ana ko da yaushe ka kasance a cikin farin ciki to dole ne ko ya ya kaima zaka samu daga gare su. Mata basu san nuna masu gadara da girman kai,domin tambarin su ne hakan su kawai suka lamunce idan sun yi maka ba komai amma kai kana yi masu za a samu matsala. Don Allah ka dinga haƙuri ka daina shiga damuwa insha Allah wata rana zaka samu wadda tai daidai da raayinka tabbas zaka samu ko da bamu tare a lokacin mun yi nisa zaka tuna da na gaya maka, domin ina ji a jikina zakai rayuwar aure tamkar ta India." A hankali ya goge hawayensa ya kalli Jiddah cikin ransa ya ce, "Tabbas ka faɗi gaskiya ɗan'uwa, Jiddah ita ce zata goge min damuwata nima ina jin hakan a jiki da zuciyata."
Jiddah ta kalle shi sai hankalinta ya koma kanshi tai mamakin ganin yana kuka, ba dai don tana kuka yake kuka ba? Kai ba zai yiyu ba, da dai abin da akai ko kuma wani ƙwaro ne ya faɗa mai a ido yasa hawaye zubowa daga idonsa, don Hausawa na cewa ido bai son baƙi. Da wannan tunanin tai na'am da wani abu ya shigar mai a ido yasa shi hawaye. Ta dube shi a hankali tace, "Sannu, miye ya faɗa ma a idon?"
Girgiza kanshi ya yi kawai ya share hawayensa bai ce mata komai ba.
Har suka isa Kaduna kowa da tunaninsa .
Tunda Alawiyya ta kama budurwar Oga Dauda tare da wasu daga yaransa sai ta kira amintattun yaranta ta damƙa masu su, sai ta koma gun su Daddy domin tasan komai na iya faruwa da su, saboda ya yadda da hatsabibancin su Hajiya Turai sosai tasan cewa za su iya komai kan lamarin, musamman da suka kasance matsafa to tabbas bibiyarta a gare su ba wani aiki bane. Da sauri ta kira islamiyyar data buɗe tace a sauke mata Alqur'ani kuma ai mata addu'a kan shari'ar dake gabanta domin abin ya shafi tsafi. Cikin ƙwarin gwiwa shugaban makarantar ya yi mata addu'a ya kuma bata wasu addu'o'in ya ce ta lazumci karanta su ko da yaushe tabbas babu tsafin da zai tasiri kan ta.
Safiya tayi tana zaune tana duba saƙonnin wayarta ta ci karo da saƙon daya sa ta tashi zumbur sai kuma ta fashe da kuka, har su Daddy suka taso kanta domin sun ɗauka ko Mamar ce ma ta mutu, sai dai cikin kukan take cewa, "Alhamdulillah! Allah na gode maka ka ida cika mun burina duka na haɗu da Jiddah Daddy." Duk da cewar basu san Jiddah a fili ba amma sun san Jiddah a labarin Alawiyya don haka sai suka samu kansu da jin farin ciki su ma sosai, domin sun san kukan Alawiyya ya ƙare tun da ta haɗu da muhimman mutane biyu da take nema ido rufe a duniyar ta.
Cikin farin ciki ta fara karanta saƙon da Jiddah ta turo mata.
"Ban san da wane irin zance zan fara ba, amma ina so ki sani na sha wahala kan nemanki na yi matuƙar kewarki na shiga nau'in rayuwa sosai bayan mun rabu. Sai dai na manta komai lokacin dana ganki a duniyar Gizo tabbas Alawiyya nayi farin ciki ganin kin samu cigaba a rayuwarki har kin kai babban matsayi tabbas na ji daɗi sosai!
Sai dai na koka sosai dana ga labarin abin da ya faru ga Mama. Yaushe duniya tai lalacewar da ake ɗora ma mutum irin wannan ƙazafin Alawiyya? Tabbas na kai ƙarar mai laifin gun mai duka don nasan shi ne kawai zai saka mata ya bi mata haƙƙinta kan abin da akai mata.
Daga ƙarshe ina maki albishir da zuwana a Yau ɗin nan domin naga Yau ne za a fara zaman kotu. Sai ince sai mun haɗu a can.
Zumbur ta miƙe "Tabbas Yau ne za a fara zaman kotu sai dai bata da babbar shedar da take buƙata a hannunta, amma ba damuwa kowa ya ci tuwo da ita miya ya sha. Tana hawaye ta maida mata amsar.
"A rubutun waya bai isa ki gane yanda nayi matuƙar kewarki ba, na neme ki tamkar yarinyar data ɓace, na sha wahala tamkar ba zan rayu ba, amma daga ƙarshe na ci alwashin cika mana alƙawarinmu na zama Lauya don kauda ɓarna a doron duniya, don ƙwatarwa yara irinmu haƙƙinsu, don samawa yara ƴanci a gun iyayensu.
Ina nan ina dakon zuwanki ƴar'uwata."
Cikin sauri suka shirya don zuwa kotun. Ba su wani ɗau lokaci ba sai gasu kan titin da zai kai su inda Kotun take.
Sai dai harbe tayar motar da suke ciki ne yasa kan motar ta ƙwace daga hannunta kai tsaye motar ta je ta bugi wata bishiya.
Cikin zafin nama Alawiyya ta latsa wata ƴar waya dake hannunta sannan ta samu ta buɗe marfin motar ta fice daga cikin ta, a hankali su Daddy suka fito, cikin ikon Allah babu wanda ya samu ko da kujewa.
Ganin wata baƙar mota ta nufo su yasa Alawiyya saurin janye su da gudu suka shiga dajin.
Ba a jima ba sai ga wasu motoci sun iso gun da gudun tsiya guda biyu suma, sun buɗewa waccan motar dake binsu Alawiyya.
Wata motar ce ta iso cikin hanzari Alawiyya ta saka su Daddy tace su isa kotun zata iso ba da jimawa ba ita ma.
Haka suka tafi duk sun ruɗe saboda ƙarar harbin dake ta tashi a gun.
Sai da Alawiyya taga motar su Daddy tabar wajen sannan ita ma ta fiddo ƙaramar bindigarta ta fara ɗauki ba daɗi da mutanen cikin baƙar motar.
Motocin da suka zo kuwa yaranta ne ta kira suka zo don haka nan da nan suka ƙure baƙar motar ga alama harsashin masu motar ya ƙare don haka suka daina harbin. Cikin jarumta Alawiyya ta isa gun motar ta buɗe sai dai ashe an harbe mutanen dake motar guda biyu. Waya ce ta fara ringing don haka sai ta ɗauka, muryar Oga Dauda ce raɗau cikin wayar yana cewa, "Ina fatan kun kama min ita, kuma baku kashe ta ba? Babanta da mijinta kawai nake son ku harbe ban da ita saboda masoyiyata na gunta da yarana."
Cike da ɓacin rai tace, "Ka makara domin sun tafi inda ba a dawowa sai dai ka turo wasu muna inda suka iske mu." Ta kashe wayar ta jefa aljihu ta nufi gun yaranta. Cikin sauri suka tada mota suka nufi gidan data ɓoye yaran Oga Dauda da budurwarsa.
Tunda ta kama búdurwar Oga Dauda da yaransa, sai ta ɓoye su wani gidanta dake gab da kotun wanda ba kowa zai ɗauka akwai mutane a cikinsa ba, domin ko da yaushe a rufe yake ba wanda zai ce ya taɓa ganinsa a buɗe.
Babu irin tambayar da batai masu ba amma sun ƙi bata haɗin kai, hakan yasa ta fara gana masu azaba ita da amintattun yaranta guda uku waɗanda suka iya aiki suka san makamar aiki, ba ta haɗa su aiki lokaci guda domin kowane guda daga cikin su gayya ne shi kaɗai, ba ƙaramin mamaki su kai ba lokacin da ta kira su kan aiki guda su duka, amma da suka fahimci aikin sai suka gane cewar lamarin babba ne, kuma akwai abin da take nufi da hakan.
Lokacin da suka gidanne Oga Dauda ya kira wayar Alawiyya ya ce mata ya amince zai yadda su haɗu amma da sharaɗin idan ya kaita gidan matsafan da aka kai yaran zata sakar mai yara da budurwa musamman da ya ji cewar akwai ciki jikin masoyiyar ta shi sai yake jin zai iya komai don tsirar da rayuwar gudan jininsa da masoyiyarsa. Hakan yasa Alawiyya kai tsaye ta nufi inda su kai da Oga Dauda za su haɗu tare da yaranta dake bin ta a ɓoye ko da zata neme su cikin gaggawa.
Tana isa gun ta hango motar Oga Dauda, don haka ta tsaya nesa da shi ta kira shi a waya, cike da samun nasara ya ɗaga wayar ya kwashe da dariyar da yake ganin ta mugunta ce ko wayau da ya yi mata. Yasan cewa duk karfin da take taƙama da shi bata kai shi ba, domin shi ɗin irin mazan nan ne ƙarfafa kuma ba haka nan yake zaune lokaci zuwa lokaci yana zuwa gun training yana motsa jiki don ƙara samun lafiya da ƙarfi saboda zuwan irin wannan ranar.
Hakan yasa ya ce cike da yarda da kansa, " Ina so mu yi faɗa da ke, idan har ki ka ci galaba kaina to nayi maki alƙawarin kai ki gidan da yaran suke , idan kuwa Ni na ci galaba kanki to tabbas za ki ban masoyiyata ki sakar min yarana kuma ki je ki nemo yaran da kanki."
Murmushi tai tamkar yana gabanta tace, "Idan har zaka zama mai cika alƙawarin nan to na yadda zan faɗa da kai idan ka ci galaba ta na janye daga shari'ar ma baki ɗaya wannan alƙawari ne."
Kashe wayar tai tana jin sautin dariyarsa.
Tare suka fito daga motocinsu, ba ƙaramin mamaki Oga Dauda ya yi ba, ganin shigar dake jikin Barista Alawiyya ba, ba don yasan tabbas da ita ya yi waya ba, haka yana da tabbacin ita ce tai magana kuma ya ga ita kaɗai ce a motar da cewa zai namiji ne ta turo mai, domin baki ɗaya tayi shigar jarumai ta rufe fuskarta.
Kallon-kallo aka fara a tsakaninsu kowa na hangen inda zai samu galabar abokin faɗan sa. Sai kuma suka fara kaiwa juna farmaki abin da ya ba Oga Dauda mamaki yadda Barista Alawiyya tasan faɗa sosai take kare kanta daga dukansa amma shi a mamakinsa ya kasa kare duk dukan da take mai.
Cikin lokaci ƙalilan Oga Dauda ya fahimci ruwa ba sa'an kwando bane, domin har ya fara kasa kai mata harin sai ita dake neman bazar da shi a ƙasa.
Sai da tai mai kyakkyawan duka na gaske wanda ya ratsa jikinsa sosai sannan tai mai duka na musamman ya zube a sume. Goran ruwa ta ɗauko ta yayyafa masa ya kasa ko zabura sai da ƙyar ya buɗe idonsa yana kallonta, facemark ɗin fuskarta ta cire sukai ido biyu tace, "Kana ɓata min lokaci domin kotu zan wuce daga can, ka tashi mu tafi."
Haka ya tashi suka tafi yana jinjina irin mugun ƙarfin da Barista Alawiyya ke da shi tamkar saurayin Soja.
Haka suka tafi yana nuna mata hanya, ta kira yaranta suka haɗe a hanya.
Hajiya Turai da Hajiya Tani baki ɗaya lamarin ya basu mamaki, yaushe Fatima ke da gata har haka? Yaushe Fatima ke da wadda zata tsaya mata irin haka? Tabbas sun san wacece Barista Alawiyya Bello Gareji domin da wahala jarida ta fita ba tare da wani sabon labari na Barista Alawiyya Bello Gareji ba.
Kuma ko da wasa Fatima bata taɓa nuna masu tana da wata ɗiya ba ko zuri'a a tsawon zaman da sukai da ita. Bata da ko ƙawa tun da aka kawo ta daga Lagos ba a taɓa sallama da sunan gunta aka zo ba gidan.
Amma Yau rana guda sai ga wata babbar Barista ta bayyana da iƙirarin ita ce ɗiyar Fatima kuma zata kare ta a kotu.
Hakan yasa suka hallara gidansu na sirri don gudanar da zaman sirri kan abin da ya shafi sauran sirrinsu guda da suka rasa yadda za su yi da shi, watau yaran Fatima guda biyu dake hannunsu sun ba dodon tsafi su kyauta, amma har yanzu bai ce komai ba kan kyautar da suka ba shi na yaran, bayan sun sha ba shi kyautar mutane manya, yara, tsoffi, da matasa duk yana hambaɗewa amma yara biyu jarirai na neman fin ƙarfinsa, abin da yasa kenan su duka suka nemi da ƴaƴan ƙungiyar dasu zo a tattauna abin da ke faruwa na lamarin.
Ɗaki ne babba wanda ba komai cikinsa sai wani jan labule da akai ma zanen wani irin kan mutum da ƙaho guda uku akan fuskarsa. Sai tarkacen tukwane da wata ƙwatarniya wadda suke zuba jini a cikinta kowane zama kowa na sha kafin a fara taron da bayan gama taron.
Wani tsamurmurin tsoho ne zaune shi kaɗai sai su kuma sun jera layi kawunansu ƙasa ba mai motsi ko kaɗan tamkar babu rai a jikinsu.
A gefe yaran ne kwance sai halba ƙafafunsu suke suna irin abin nan na wasan yara mai haɗe da gwaranci. Tamkar ba a raba su da mahaifiyarsu ba domin ba rama a tare da yaran ko kaɗan, sai wasa suke ƙarar sautin gwarancinsu ya cika ɗakin baki ɗaya.
Tsohon da ke zaune a daban wanda ga alama shi ne shugabansu ya runtse idonsa ya fara karanta wasu ɗalasiman tsafi ya nuna yaran da hannunsa sai wani haske ya fito ya yi sama da yaran suka ɓace nan take.
Ajiyar zuciya ya saki domin tun da aka kawo yaran nan yake gwada ƙarfin tsafinsa kansu amma a banza babu yadda bai ba da wuƙar tsafinsu ba su ta yanka yaran amma ta kasa duk lokacin daya nuna wuƙar ya nuna su sai wata uwar tsawa ta cika gun wuƙar tai baƙi ta dakushe kamar an dakushe ta.
Hakan yasa yanzu ya kauda yaran don su yi shiri na musamman kan yaran, domin dole ne jinin yaran ya zama kyautar musamman ga dodonsu a Yau ba sai gobe ba.
Kowa ya bada shawarar da yake ganin zata iya fissheshi amma da an gwada sai a ga ba inda zata don bata tasiri kan yaran.
Daga ƙarshe suka yanke shawarar su haɗa ƙarfinsu waje guda su turawa babban nasu ya ji da lamarin yaran su yi kallo kawai su, domin sun san idan aka haɗa ƙarfinsu waje guda tilas ya yi tasiri a kan yaran.
Nan take suka haɗe ƙarfinsu baki ɗaya suka turawa babban su, shi kuma ya ɓace yana dariyar samun nasara.
Bacewarsa ke da wahala sai ga Oga Dauda da Barista tare da yaranta sun shiga cikin gidan, sai dai suna shiga suka dinga cin karo da abubuwan ban tsoro da firgitarwa masu ɗaga hankali, ko da Barista Alawiyya ta lura da yaran nata basu da ƙarfi ta nan gun sai ta basu umarnin su jira ta waje kawai ita ta ja Oga Dauda suka kutsa cikin gidan duk da abubuwan da take hangowa na halakar da mutum.
Shi kan shi Oga Dauda haƙuri yake bata don yasan zai iya rasa ransa a hanyar shiga cikin gidan.
Suna wuce ƙofar farko ta gidan suka ga ƙofar gaba ta koma ƙaton Zaki ya buɗe bakinsa sai kaɗa bindinsa yake.
Ga alama kuma ta cikin bakin zakin ƙofar shiga gidan take, Oga Dauda ya dinga ihu ina neman taimako amma ba mai jinsa, haka yana ji yana gani suka turfafi ƙofar gidan gadan-gadan ko a jikin Barista Alawiyya bata razana ba balle ta fasa shiga bakin zakin dake ta zaburowa yana kawo masu hari tamkar wanda aka ɗaure yake son katsewa yaga abinci.
Lokacin da suka isa gaban zakin ya wangame bakinsa baki ɗaya Barista Alawiyya tai bisimillah ta runtse idonta ta afka cikin bakin sai gasu sun bayyana a harabar gidan, ɗakuna birjik a jere.
Oga Dauda yai ajiyar zuciya ya jinjina wa taurin kan Barista Alawiyya da shaiɗancinta ya ƙara tabbatar da cewa Yau zai sha kallon artabu gun matsafa da wadda bai san a wane sahu zai aje ta ba.
Ɗakin farko Barista Alawiyya ta buɗe da ƙafarta ya kuwa buɗe, ta kunna kai don ta saki Oga Dauda saboda ya gama yi mata aiki yanzu tasan bai iya fita gidan, ko da ya fita yaranta za su kama shi cikin sauƙi.
Tana leƙawa ta ga mutane zaune duk an aske masu kai, ba riga a jikinsu duka maza ne, ga wani abinci nan wanda da gani su aka ba suka kasa cin sa a ajiye kudaje na binsa.
Fita tai ta buɗe na kusa da shi, nan kuma mata ne birjik su ma duk ba riguna an aske masu gashin kai wasu kwance wasu zaune duk sun fice hayyacinsu da gani sun jima a ɗakin, ba mamaki ɗauki ɗai-ɗai ake masu a kowace rana don haka suke ta ramewa don zullumi da fargaba.
Sai da ta shiga ɗakuna kusan takwas kowane da abin da zata gani cikinsa.
Wasu ɗakunan ta hango can gefe guda, cikin sauri ta isa inda suke, na farko ta tura ta shige. Suna zaune kamar masu zaman makoki, duk sun shafe fuskarsu da jan fenti, kawai gani su kai mutum ya shigo cikin baƙaƙen kaya fuskarsa a rufe, domin ba wanda zai ga shigar Barista Alawiyya ya ɗauka mace ce ba namiji ba, shi ma namijin irin zaratan jaruman nan da suke fitowa a cikin finafinan indiya ko China.
Tare suka tashi tsaye, suna mamakin wane irin taƙadarin shaiɗani ne ya karya masu alkadarin kahin (Kahi) da su kai ma gidan ya shigo? Tabbas ko waye ba ƙaramin shiri gare shi ba, ko kuma yasan sirrin gidan ne don haka ya shigo a daidai lokacin da suke cikin neman mafita kan damuwarsu.
Da yake Barista Alawiyya bata san fuskokinsu Hajiya Turai da Hajiya Tani ba, sai tai tsaye tana nazarin kaf matan dake wajen a zaune.
Mataimakin shugaba ne ya fusata da ganin tsaurin idon ko waye ma ya tashi cike da mugun nufi ya ɗauki wuƙar tsafinsu ya tunkari Barista Alawiyya.
Murmushi tai, don tasan ko hannu biyu ba zai amfani da su ba gun kwantar da shi ƙasa.
Sai dai wannan tamkar wata hanya ce guda da su Hajiya Turai za su fallasa kansu gareta idan ta tsaya mai kama da tsoffin can ya sauke mata wuƙar suka ga bata kama ta ba, tabbas za su san wacece ita kai tsaye.
Haka kuwa akai, yana zuwa cikin azama da sauri ya caka mutumin wuƙar hannunsa sai yaga wuƙar ta daka tsalle ta faɗi ƙasa ta karye gida biyu. Abin da ya razana shi tare da sauran dake zaune suna kallon abin da ke faruwa.
Hajiya Turai ta kalli Hajiya Tani ido waje tace, "Tani anya ba shegiyar yarinyar nan bace ta zo nan gun ba ɗiyar Fatima?" Hajiya Tani ta haɗe miyau da ƙyar tace, "Kin rigani a fili na rigaki a zuci Turai."
Tamkar raɗa ko gulma haka suke maganar amma ba kalmar da Barista Alawiyya bata ji ba, don haka ta murmusa ta ɗaga tsohon dake gabanta da hannu ɗaya ta maka da ƙasa.
Ko da ganin hakan sai sauran mazan gun suka tasar ma Alawiyya da nufin taruwa baki ɗaya su kama ta.
Sai dai abin mamaki wani irin duka take masu mai zafin gaske, tasan inda take duka nan take gun ya samu matsala. Ganin wankin hula na niyyar kaisu dare yasa wani ya hura wani ƙaho nan take gidan ya amsa kuwwar ƙarar sautin ƙahon.
Gidan ya kama girgiza sai duhu ya mamaye wajen baki ɗaya ko tafin hannu ba a iya gani don tsananin duhu.
Duk abin nan kiran sunayen Ubangiji bai bar bakin Alawiyya da zuciyarta ba, don haka sai ta ɗora da wata addu'arma nan take duhun ya yaye haske ya bayyana tamkar farkon shigowar ta ɗakin. Sai ga su ta gansu suna ɗauke da wani irin ƙaho ba irin wanda aka busa da farko ba mai tsinin gaske sun nufota, cikin sauri ta duƙe ta fice daga tsakiyarsu ta dira a bayansu.
Sai kuma ɗakin ya kama girgiza wani uban rami ya bayyana gaban Alawiyya yana ƙara zurfi da faɗi yana wawake wajen har ya kusa isowa inda take, sai su duka suka ɓaɓbake da dariya. Wanda ya kawo mata hari da wuƙa ya ce, "Ya kai wannan jarumi ka sani cewa tabbas kayi ƙoƙari amma fa irin ƙoƙarin mai shiga rijiya domin ba zaka taɓa barin gidan nan da rai ba, sai dai kayan jikinka su bar gidan nan. Ina so ka sani tunda aka kafa gidan nan shekaru da dama da suka wuce muke ayyukanmu cikin sirri bamu taɓa samun wanda ya shigo gidan nan ba sai dai idan mu ne muka shigo da mutum amma ga shi Yau ka karya mana wannan tarihi ka shigo cikin gidan nan ba wani tsoro ko tashin hankali har ka yi fito-na-fito da mu. Ina maka albishir da cewa idan taƙamarka hatsabibi to muma iyayen hatsabiban ne ko ma ince Kakansa. Shawarar da zan baka shi ne ka miƙa wuya kawai, daman a Yau ne za mu ba Dodo kyautar jinin tagwaye tabbas zai murna ya samu da naka jinin ko shakka babu sai mun samu alheri mai gwaɓi daga albarkar dodo."
Barista Alawiyya ta nufi ramin gadan-gadan ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, domin ta yadda Ubangiji ba zai taɓa basu dama kanta ba, balle su samu nasara kanta ba.
Sai ga shi tana shiga gun ya koma ba komai ramin ya ɓace wajen ya koma yadda yake.
Sai ga wasu irin ƙattin maza sun fito daga wani ɗaki ɗauke da muggan makamai sun durfafi inda take tsaye.
Gyara tsayuwa tai ta ja tunga tana jiran zuwan nasu, cike da jarumta da ɗaukar wa rai.
Nan da nan wajen ya kacame da faɗan gaske tamkar a filin yaƙi amma abin mamaki su duka an kasa samun wanda ko sau ɗaya ya taɓa jikin Alawiyya da makamin hannunsa. Ita kam duk ta ji masu rauni babu wanda jini bai fita daga jikinsa ba.
Kafin kace me? Alawiyya ta zubar da su tas, ta ja tunga tana ƙare wa mutanen kallo, zuwa yanzu ranta baki ɗaya a ɓace yake domin ta ƙagara ta gama da su ta nemo inda yaran suke don bata ga alamar su a gidan ba.
Ganin haka yasa wasu da dama su ka ɓace ɓat! Sai ga shi an bar su Hajiya Turai kawai, suka dubi Alawiyya cikin tafasar zuciya suka kece da dariya lokaci guda, sai kuma suka haɗe rai. Hajiya Turai ta dubi Alawiyya tace cikin ɗaga murya, "Nasan ko baki gaya mana ba,kece Alawiyya ko ince Barista dake kare Fatima, to ina so ki sani babu wanda muka taɓa raya za mu yi wani abu da shi muka fasa, don haka dole ne rayuwar Mahaifiyarki data ƙannenki ta salwanta kamar yadda mu ma muka haƙura da rayuwar mijinmu data yaranmu da muka ba dodon tsafi ya cinye.
Bari na baki wani labari wanda nasan ba dole bane idan Uwar taki ta baki shi ba, mu ne nan muka kashe Alhaji! Haka mu ne nan muka salwantar wa uwarki da idanunta muka asirce su yadda ba zata sake gani ba har sai ranar da dodon tsafinmu ya halaka, abin tausayi abin dariya shi ne ba zai taɓa halaka ba duk don shekaru ɗari masu zuwa, domin muma a haka muka shigo ƙungiyar muka ganshi kuma har gobe yana a yadda yake.
Sannan idan taƙamarki kice za ki maka mu a shari'arki kan wannan harka ta tsafi to ruwa kike domin akwai manya-manyan ƙusoshin gwamnati dake cikin wannan harka dumu-dumu." Ta dubi Hajiya Tani tai mata inkiya sai kuwa ita ma tace, "Yarinya ina so ki sani ƙannenki na cikin gidan nan amma a inda baki isa ki je gun ba, domin suna ɗakin dodo wanda ko mu da kike gani ba duka bane kowa ya taɓa shiga ɗakin ba, nasan zuwa yanzu sun riga da sun zama gawa ƙannenki don haka ki shirya binsu domin labarin zuwanki ya iske dodo ko shakka babu yana tafe gunki. Da wannan muke maki ta'aziyya domin dai ba za ki sake ganinmu ba duk inda za ki bincika mun riga mun maki nisan da ba za ki iya kamo mu ba.
Ku ki riƙe a ranki za ki sha mamaki a kotu domin mun yi kyakkyawan tanadi a can ma wanda muka tura mutanen mu don tabbatar da cewa an yanke ma Fatima hukuncin kisa kamar yadda muke buƙata a bainar nasi." Kawai gani tai sun ɓace su ma ba kowa gun sai ƙattin data kwantar ƙasa ke ta nishi.
KOTU
Kotu ta cika ta batse, da mutane kowa son ganin matar data kashe mijinta yake, miji kuma babbar Soja kamar Captain Aliyu Masani wanda yanzu ya jima da yin ritaya, ya amshi manyan ayyuka sosai ya ji da su, gwamnati na matuƙar ji da shi, amma matarsa ta kashe shi.
Alƙali ya shigo, don haka kowa ya nabba'a ya natsu ya yi shiru tamkar ba mutane sai ƙarar fanka da takardun da baristoci ke buɗewa kawai ake ji.
Magatakarda ya tashi ya fara karanto shari'ar da za a fara.
Magatakarda, "Kotu na buƙatar a matso da Fatima Aliyu Masani."
Sai ga Fatima wasu matan ƴan sanda sun rako ta, sun kai ta har inda zata tsaya.
Magatakarda, "Kotu na tuhumar Fatima da kashe mijinta marigayi Captain Aliyu Masani ta hanyar yanka ma shi wuya da caccaka mai wuƙa a cikinsa."
Alƙali, "Malama Fatima kin ji abin da kotu ke tuhumar ki da aikatawa na kashe mijinki ta hanyar yanka wuyansa da caka mai wuƙa a cikinsa."
Fatima ta fashe da kuka ta sadda kanta ƙasa ta kasa furta ko da kalma guda.
Mutane duk suka zuba mata ido, wasu tausayinta suke yayin da wasu ke mata kallon munafuka kawai, ta kashe mijinta tana kukan munafurci.
Alƙali ya sake maimaita tambayarsa amma Fatima ban da kuka babu abin da take yi, don haka Alƙali ya buƙaci da lauyan wadda ake tuhuma ya fito tare da Lauyan mai ƙara.
Sai dai abin mamaki Lauyan mai ƙara ne kawai ya fito,babu Lauyan wadda ake tuhuma.
Sai kotu ta hartsine da magana, kowa da abin da yake cewa, sai da Alƙali ya yi tsawatar sannan akai shiru.
Alƙali ya gama rubuce-rubucensa ya ce, "Kotu ta ba, Fatima kwana biyu ta bayyana gaskiyar lamari tunda bata da Lauya...
"Assalamu alaikum, a gafarce ni ya mai girma Alƙali. Haƙiƙa Fatima na da Lauya har guda biyu, ko don ko da aiki ya yi wa guda yawa insha Allah za a samu guda kamar dai yanzu. Ina ƙara neman afuwar Alƙali saboda rashin zuwana da wuri, hakan ya faru ne saboda doguwar tafiyar da nayo.
Sunana Barista Hawwa'u Bello Dawa, Ni ce Lauyar dake kare wadda ake tuhuma watau Fatima Aliyu Masani."
Sai kallo ya koma sama, Shaho ya ɗauki Giwa!
Mustapha mamaki kamar ya kashe shi, wai dama Jiddah Lauya ce? Dama tana aikin Lauya bai sani ba? To yaushe ta fara aikin bai da masaniya!
Alƙali ya yi murmushi domin jawabin Lauyar ya birge shi, tabbas tasan aikinta ga alama, don haka ya amshi uzurinta ya ce a fara Shari'a.
Barista Jiddah ta ƙarasa gaban Maman Alawiyya tace, "Kotu na buƙatar jin sunanki tare da jin kaɗan daga alaƙar ki da mijinki."
Fatima, "Kuka kawai take har zuwa yanzu bata furta ko da kalma guda ba, sai dai a cikin zuciyarta tana tambayar kanta ina Alawiyya take? Wacece wannan to? Kar dai ace Jiddah ce ta Iyami? Sosai take son yin magana amma bakinta ya kasa furta ko da kalma guda.
Lauyan mai ƙara ya tashi ya ce, "Ina son kotu taban damar tambayar mai laifi ba mamaki nadamar abin da ta aikata ne yasa ta kuka har ta kasa magana."
Barista Jiddah, "Ya mai girma mai Shari'a ina son kotu ta tsawatar wa da Lauyan mai tuhuma domin yana razana wadda ake zargi ta hanyar jingina mata laifin da babu tabbacin ta aikata shi, hakan kuwa bai kamata ba ya mai girma mai Shari'a."
Alƙali, "Kotu ta karɓi uzurinki, Lauyan mai ƙara ka gyara kalaminka."
Barista Jiddah, "Na gode sosai Ya mai girma mai Shari'a."
Lauyan mai ƙara, "Fatima ina son ki gaya min auren dole ki kai da magariyi mijinki shi yasa kika kashe shi, ko ko saboda kuɗi ki ka kashe shi?"
Fatima, "Kuka kawai take fiye dana farko, domin ta lura bakinta ba zai taɓa furta ko da kalma guda ba.
Barista Jiddah, "Cike da sanin daraja da kimar wannan kotu nake son ta ɗaga wannan zama zuwa gaba, domin bincikar lafiyar wadda ake zargi."
Alƙali, "Kotu ta amince, ta ɗage zaman sai zuwa 25/8/2022."
Magatakarda ya sake karanta ƙarar gaba.
Jiddah ta nufi office ɗin da ta shiga ta amso aron kayan Lauya gun wata ƴar classmate ɗin ta da su kai karatu tare. Tana mata godiya kenan Mustapha ya shigo har zuwa yanzu akwai ɗumbin mamaki akan fuskarsa.
"Dama ke Lauya ce Jiddah?" Cewarsa yana kallonta.
Murmushi tai, "Tabbas haka ne sai dai Ni Lauya ce mai zaman kanta wadda bata taɓa ɗaukar aikin da zuciyar zata iya ba, saboda rashin katangu guda biyu dana rasa, amma Yau ina zuwa nan sai naji Ni a cikakkiyar Lauya mai ji da kanta ta kowane fanni.
Sannan zan bi kowace hanya don ganin na ci nasara akan wannan shari'ar ko da Alawiyya bata bayyana ba, tabbas sai na binciko gaskiyar lamarin nan."
Sai a lokacin ya samu natsuwa, har yake hango tarin nasara a gabanta ya ƙara ji a ransa cewa tabbas ita ce cikar burinsa.
To masu karatu kun ji dai ana wata ga wata.
Taku a kullum Haupha 