INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Uku

Ko da Lantai ta ganta da littafin a hannu ta kuma ji abin da Inna Kande ke cewa saita natsu ta dubi Inna Kanden ta ce, "Wannan littafin da kike gani Inna Kande babu komi cikinshi sai karatu kan darasin rayuwar ƴan mata na rantse da Allah idan kika bari na karanta maki shi za ki yadda da abin da nace maki."

INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Uku

 Page 3

 

Lantai daga cikin ɗakin ta leƙo fuska dagaje-dagaje da hawaye da majina ta ce ma Inna Kande.

"Yo Inna Kande ke don baki ji abin da ya samu Hidaya ɗin nan ba wallahi da sai kin kwana kin wuni kina mata kukan tausayi."

 

Inna Kande ta maka mata harara ta ce, "Allah Ya rabani da kukan ƙarya ni kam."

 

Ai sai Lantai ta buɗe ɗakin ta fito ta kwanta ƙasa ta fara rero kukanta tana cewa,

"Hidaya kinga rayuwa kinga ta kanki wallahi dole duk mai zuciyar imani da sauran tausayi a tare da shi ya zubar maki da hawayen wannan lamari, wayyo Hidaya sannu kin ji ?

 

Inna Kande duk wata ƙulewa ta riga ta gama ƙulewa don haka ta warce littafin ta nufi makewayi da shi tana cewa, "Bari na sako ɗan banza shadda (masai) sai inga abin da za ki sake karantawa ki hau kukan."

 

Lantai na ganin haka ta wage baki ta ce, "Allah Ya sa ki saka ai dai karatun jarabawarmu ne na makarantar da Yayana yace zan je, babu ruwana domin kuɗi ya kashe masu yawa aka ba shi littafin ya bani."

 

Sai Inna Kande tayi tsaye da littafin tana kallon Lantai don tabbatar da abin da ta ce idan gaskiya ne.

 

Lantai kuwa ta sake cewa, "Allah Sarki Yayana kana can kana shan wahala kana samun kuɗi kana sai min littafin karatu Inna Kande na lalatarwa, dole inyi kuka." Ta sake dagewa iyakar ƙarfinta ta saka ihun kuka.

 

Dole Inna Kande ta dawo da littafin ta wurga mata tana cewa "Idan kika sake min kuka a cikin gida sai na ƙwace littafin nakai makarantarku nace a sauya maki dana kirki yo ina amfanin karatun kuka ?

 

Ko da Lantai ta ganta da littafin a hannu ta kuma ji abin da Inna Kande ke cewa saita natsu ta dubi Inna Kanden ta ce, "Wannan littafin da kike gani Inna Kande babu komi cikinshi sai karatu kan darasin rayuwar ƴan mata na rantse da Allah idan kika bari na karanta maki shi za ki yadda da abin da nace maki."

 

Ita dai Inna Kande ta wuceta ta samu waje ta zauna bata tanka ba.

Sai kawai Lantai ta fara ƙoƙarin karantoma Inna Kande labarin dake cikin littafin.

 

Inna Kande tayi shiru tana sauraren labarin tana jinjina yadda akai aka samu labarin ma .

Ta dubi Lantai ta ce, "Yo wai yanzu haka ake yi daman a wannan lokacin ? Lallai kam karatun nan naku akwai faɗakarwa a cikinsa , da ban tausayi amma kuma mu lokacinmu ai bamu san wata soyayya ba mu iyakarmu da kin kai goma akai ki gidan mijinki."

 

Littafin Lantai ta aje tayi shiru tana tunani.

Zuwa can ta dubi Inna Kande ta ce, "Inna Kande ya kike tunanin wanda ya rubuta labarin nan yake?

 

Inna Kande ta dubeta "Au da kina nufin daman ba karatu bane labari ne kika sani inata jinjina abin a ƙasan raina ?

Ni dai nayi mamakin wannan karatu haka naki tiryan-tiryan ashe duk ƙarya ne ?

To bari Yayanki ya zo ai shi ya gane ko wane irin karatu ne.

Lantai ta zumɓura baki ta ce, "Ke fa Inna Kande haka kike wallahi to miye abin kika saka Yayana cikin wannan maganar ?

Ba shi ne ko da yaushe yake ce min jaka ba ? To yanzu kinga ai na zama mai ƙokari tunda ina iya karantawa.

 

Inna Kande dai bata gane ba don haka tai shigewarta ɗaki tana tsogumi akan abin.

 

Lantai ta ƙurama sunan marubucin ido tamkar shi ne take kallo, murmushi kawai take tana jin ya burgeta sosai yadda ya iya yin wannan bajinta ta rubuta labarin soyayya mai tsuma zuciya irin haka.

Tabbas soyayyar Yaya Sadik da Hidaya ta burgeta sai dai ƙaddarar data afkama soyayyar ke sata kuka sosai.

Shi kanshi Hasib soyayyarsu ta burgeta don ya bata tausayi sosai ba kamar wajen da suka aikata abin da ya jawo ƙalubale ga rayuwar Hidayar .

 

Sai Lantai ta dinga ganin tamkar a gabanta ake abin, sai ta kama kuka tana surutai .

 

Tun abin na ba Inna Kande haushi har ya koma bata tsoro don ko barci Lantai ke yi sai taita surutai tana kiran suna Yaya Sadik ko taita ambatar Hidaya kin ban tausayi wayyo Hidaya sannu .

 

Sai da Lantai tafi sati duk fejin data karanta sai ta aje littafin ta kama kuka tana surutai kamar wadda ta zare, abin kamar zauci haka ya koma ma Lantai.

Inna Kande abin yafi ƙarfinta don haka ta koma yi mata tofi a ruwa tana bata wai ko tayi gamo ne a littafin .

 

Cikin lokacin Lantai ta daina aikin komi na gidan ko aikenta Inna Kande tayi sai ta ɓoye littafin ta je ta samu waje taita karantawa idan anzo inda ke bata tausayi taita kuka duk wanda zai wuce sai ya tambaye ta abin da akai mata take kuka.

Ita kam sai dai ta dinga cewa Hidaya ke ban tausayi ita da Hasib amma shi kanshi Yaya Sadik abin tausayi ne wallahi.

Ba fahimtar inda zancenta ya nufa suke ba sai su raɓata su wuce masu dama ne ke cewa ta koma gida tai haƙuri.

 

Wasa-wasa Lantai ta rage surutu ta rage tsokanar mutane hatta abinci sai Inna Kande tasha fama da ita kafin ta ci, ga shi ta kasa ida labarin wai bata so ta ida karantawa taga abin da bai kamata ba ga Hidayar .

 

Sai Allah yasa ɗan tsakanin sam Yayanta Hafiz bai zo ba yana can burni sai dai yana yawan yo masu aike .

 

Inna Kande sosai abin ya dameta don haka ta shirya tsab ta nufi makarantar ba tare da sanin Lantai ba.

Ko da ta je da Malam Muntasir ta fara cin karo.

Yana ganinta ya shaidata Inna Kanden Nuratu ce don haka ya gaidata yana mai mamakin abin da ya kawota makarantar bayan Nuratu ta gama karatunta .

 

Inna Kande ta dubeshi ta fashe da kuka ta ce, "Ɗan nan baku kyauta min ba wallahi baku dubamin ba sam, ai wannan zalunci ne na rantse dana san haka kuke da komi Hafizu zai yi ba zan bari ya kawo Lantai wannan makaranta ba Allah."

 

Sai kan Malam Muntasir ya ɗaure sosai da maganganun Inna Kande, domin yanzu dai babu makaranta ga Nuratu balle ace kan Nuratu ne aka samu matsala amma sai ya dubeta cike da kulawa yace, "Inna ku daina kuka ku yi bayanin abin da akai maku don Allah."

Ta dube shi ta ce, "Yaro kana nufin baka san abin da ke faruwa da Lantai ba ?

Gabanshi ya faɗi Daram !

 

"Me ya faru da Nuratun ne Inna ?

Bata lafiya ne ko me ?

 

Inna Kande ta ce, "Yo ai gwara ciwon da abin da ke faruwa ga Lantai yaro domin yanzu Lantai ta zama kurma banda kuka babu abin da take yi kai dole in maku Allah Ya isa wallahi yaro, domin ni kam banji daɗin karatun Lantai ba ko kaɗan wallahi."

 

Har zuwa yanzu Malam Muntasir bai fahimci inda Inna Kande ta nufa ba, don haka ya sake jefa mata tambaya.

 

"Inna kwance Nuratun take ne ko me ?

 

Kamar ta shafe fuskar yaron da mari haka take ji amma ta daure don so take ya je ya amshe wancan karatun ya sauya mata da wani.

Ta kada baki ta ce, "Yaro littafin da kuka ba Lantai shi ne sanadin haukacewarta domin tunda ta fara karanta littafin ta susuce ta lalace ta fice daga kuzarinta banda sana'ar kuka babu abin da take yi yanzu, kai ko barci Lantai ke yi sunayen mutanen cikin littafin nan take ambata tana kuka."

 

Yanzu ya fara gano bakin zaren amma dai da sauran bayani.

 

Don haka ya miƙe tsaye yace, "Mu je gidan inga littafin Inna."

 

Inna Kande ta miƙe tsaye tana ta faɗa.

"Ya kamata dai ku ji tsoron Allah ku daina ba yara littafin da zasu dinga mafarki suna kuka irinna Lantai idan ba haka ba na rantse wata rana sai na kai ku gun mai gari anyi mana shari'a."

 

Shi dai Malam Muntasir binta kawai yake yana kaɗa don yasan indai Inna Kande ce tafi haka akan Lantai.

 

Amma wane littafine Nuratu ke karantawa tana shiga wani yanayi haka ?

Yaushe Nuratu ta fara karatun litattafai ne ?

Abin da mamaki fa.

 

Suna zuwa gidan cikin sa'a Lantai na kwance kamar tana barci amma idonta biyu kawai hasko abubuwa take a ranta.

Wai ga Hadiya nan zaune tana kuka tana ba iyayenta haƙuri ita ba zata auri Yaya Sadik ba saboda tana da hujja.

Mahaifinta sai kashe ta da mari yake yana bata isa ba.

A fili take cewa "Hidaya kin yi wauta amma ya za ki yi kawai ki gayama Baba abin da kika aikata ba mamaki su bar maganar aurenki da Yaya Sadik."

Hawaye wasu na korar wasu daga idanun Lantai.

Inna Kande ta nuna ma Malam Muntasir Lantai ta ce, "Idonka ya gane maka tsiyar da kuka bata ta maida yarinya salihar ƙarfi da yaji."

 

Shi kam Malam Muntasir sai ya ƙame waje guda yana nazari tare da mamakin abin da ke damuwar yarinyar haka.

 

Tun tana magana a hankali harta dinga yi da ƙarfi sautin kukanta na sake hauhawa.

A hankali ya taka ya isa gareta ya tsugunna cikin sanyin murya ya kira sunanta.

 

"Nuratu,

Nuratu ,

Nuratu , kira uku yayi mata amma bata san yana yi ba, don haka ya taɓa ta yana ambatar sunanta.

 

Tana ankara da shi ta zabura tsoro ya bayyana a kan fuskarta sosai.

 

"Malam don Allah kayi haƙuri don Allah kai mun rai don Allah Malam."

 

Kallon tsab yayi mata sanan ya tariyo maganarta sai kawai ya fahimci akwai abin da tayi ma shi na laifi , Nuratu tafi kowace ɗaluba laifi a wajenshi da sauran Malaman makarantar domin yadda take da tsokana da jan faɗa sannan bata jin magana haka bata tsoron duka .

Kallonta yake sosai kallon da bata so don haka ta toshe bakinta tana kallon ƙofa ko bai tambaya ba yasan neman hanyar guduwa take don haka ya riƙe mata hannu yana mata magana da tsawa.

 

"Nuratu Kabir me ke faruwa ne da ke ?

Wane littafine kike karantawa ?

Waye ya baki littafin ?

 

Lantai ta kama mazurai tana firi-firi da idanu irin na marassa gaskiya.

 

Inna Kande ta dubi Malam Muntasir fuska turɓune ta ce, "Ban gane ba, ka zo zaka ƙara mata wani kukan ni da na kira ka don ka amshe littafin ka sauya mata wani, amma ka tsare ta da idanu kana ƙara firgitamin yarinya."

 

Ko da Lantai taji maganar Inna Kande sai ta ida wage bakinta ta fara magana.

"Kai haƙuri Malam ba laifina bane laifin Inna Kande ne ita ce ke hanani karanta littafin da yanzu na gama ."

 

Sarai ya fahimci komi yanzu, sai dai zarginshi yake son ya ida tabbata kawai.

 

Inna Kande ta kama neman littafin don ta ba shi tsiyarsu ko Lantai ta samu kwanciyar hankali ta daina mafarkai tana kiraye-kirayen sunaye kamar kamun miyagu cikin dare.

 

Sai dai tayi neman duniya ta kasa ganin littafin duk inda tasan zata samu littafin ta duba bata ganshi ba a ɗakin.

 

Malam Muntasir ya miƙe tsaye yace, "Inna ku ƙyaleta zan bincika insha Allah zan gane ko miye ko kuma na kira Hafiz musan yadda za ai."

 

"Mi kace ? Tabdijan wallahi kada kasa Yayana dukan ajali zai mun kawai ya tsaya iyakar mu nan kawai ."

 

Kamar yayi dariya ya daure ya fice yana cema Inna Kanden "Inna ta dinga zuwa makaranta ana masu lesson kafin fitowar jarabawarsu."

Wani sanyi Lantai taji da bai kira Yayan ba haka bai matsa sai ta ba shi littafin ba ita wa yaga littafinshi a gunta ?

 

Inna Kande ta watsawa harara ta ce, "Na rantse wajen neman maganarki wataran sai kin sa an mun dukan mutuwa Inna Kande.

Kowa yasa kika je makarantar ma?

 

Inna Kande tai biris da ita don har ga Allah abin na damunta tun sanda Lantai ta tarkaci koke-koken nan komi ya tsaya mata yarinya duk tayi ɗan wuya ba siɗi ba saɗaɗa.

 

Washe gari da wuri Lantai ta kimtsa bayan ta adana littafin domin tasha alwashin ko kasheta zai ba zata maida ma shi littafin ba sai dai duk yadda zai yi yayi.

Ita fata take ma ya sake ajiye wani littafin ta kuma ɗaukewa .

 

Tana zuwa kuwa ta iske shi kaɗai ne a office ɗin yana duba wani littafi, sunan marubucin littafin kawai ta karanta don bala'i .

 

Nura Sada Nasimat

 

Wayyo Allah daɗi kashe ni yayo sabo ashe ?

 

Tsalle take tana ihun murna tana nanata yayo sabo ashe ?

 

Malam Muntasir ya tsira mata ido kawai yana kallonta sai ranshi ya ba shi sabbin kayan daya saka take ma wannan iskancin domin ta ƙware da ƙirga kayan malamai daman kowa yasan hakan a makarantar malamai sun sha dukanta akan hakan amma bata dainawa sai idan malami bai sanyo sabbin kaya ba.

 

Kallonta yake yana girgiza kai ganin bata da niyyar natsuwa yasa ya buga mata tsawa yace, "Nuratu Kabir me ye hakan ?

 

Sai lokacin ta natsu ta gane ta kwabsa amma fa duk tsiya yau bata tafiya gida sai da littafin Tauraronta Nasimat.

 

Shi kuma Malam Muntasir ya zo da littafin ne don ya gwadata daman ya ga shin littafin da kwanaki ya aje ne ya ɓace ke gunta koko ?

 

 

To ya kenan jama'a ?

 

Ita dai ta rantse da littafin zata koma gida, shi kuma ya zo da littafin ne don ya gane idan ita ta ɗauke ma shi wancan akan shi ne take koke-koken.

 

Haupha