HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 28
HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 28
Cikin matuƙar farin ciki maigidan ya ce, "Allah Ya amince cewar Fatima ciki ne da ita, tabbas da nafi kowa farin ciki da jin daɗi. Maza Fatima tashi mu je asibiti, yi sauri ki shirya."
Kasa ɓoye ɓacin ransu su kai, don haka kowacce tace, "Wallahi ba dai ciki a gidan nan ba, idan kuwa ya bayyana sai dai ace a jikina ehe."
Shi dai ya kama ni muka nufi sashena, yana ta jera min sannu.
Muna zuwa asibitin akai mana maraba, saboda sun san shi sosai ga dukkan alama, nan da nan akai min duk abin da ya kamata, aka ce mu jira minti biyar za a fitar da sakamakon awon da akai min.
"Congratulations Alh. Ina taya ka murna, domin Hajiya na ɗauke da ciki na tsawon wata uku."
"Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Sai da Alhaji ya jera sau uku sannan ya yi sujjada ya ƙara gode wa Ubangiji, sai kuma ya shiga fito da duk abin da ke aljihunsa yana ba Likitan kyauta.
Ni kaina naji daɗin jin ina ɗauke da ciki duk da cewar ina tantama daman can naga kamar akwai kamar babu saboda nasan yana son haihuwar yasa ban gaya mai ba, kada na sa mai rai akan abin da ban da tabbacin sa.
Muna komawa gida muka iske su Hajiya Turai zaune a babban falon gidan, sun yi jigum-jigum kamar masu zaman takaba ko gaisuwar mutuwa.
Cikin farin ciki ya dinga ɗaga su ɗaya bayan ɗaya yana masu albishir da an kusa jin kukan yaro ko yarinya a cikin gidan nan Insha Allah.
Ba tare da sun ce ƙala ba kowacce ta fincike daga jikinsa ta shige ɗakinta ta banko ƙofa da ƙarfin gaske.
Bai damu ba, shi kawai ta Ni yake, nan da nan ya ce na shirya mu je na siyo abin da nake son ci da sha, kafin na ji yunwa, bai san ina amai ko da wasa don kada na girgiza mai abin da ke cikina.
Tabbas naga farin ciki da gata gun Alh har ya dinga tunamin lokacin da nake da cikin Alawiyya yadda Babanta ya dinga murna yana ɗoki komai ya siyo ya kawo min. Na fakaici idonsa na share hawayen tunawa da Baban Alawiyya da ita kanta Alawiyya da nayi. Amma tabbas idan Allah Ya sauke Ni lafiya zan je na gano Alawiyya na kai masu abin da na haifa. Insha Allah Ni ma zan sake gina zuri'a ba zamu ƙare ba kenan da yardar Allah sai mun fi baya yawa, domin a baya Yayyena huɗu duk maza, to insha Allah zan maida su kaf kuma na maida mahaifiyata da mahaifina tare da Ni karin kaina, nasan mu haka kawai zamu taru mu sake tara zuri'a mai yawan gaske.
Ba ƙananan kaya Alh ya kwaso min ba, har faɗa nake mai ya bari amma kamar ƙara tunzura shi nake haka yake nunawa sai da nace mu tafi gida yunwa nake ji sannan ya haƙura da loda kaya mu ka koma gidan.
Ba kamar yadda na zata ba, na ɗauka zamu sake iske matan gidan a falo sai naga ba kowa, naji daɗin hakan don nasan da suna gun dole ai tashin hankalin kayan daya jibgo min.
Cikin sauri na faɗa sashena ina jin farin ciki, tabbas Yau naji na fara rage damuwa sosai daga cikin tarin damuyoyina. Da kanshi ya girka min abinci mai daɗi, ya yi min daɗi kau, don ba kaɗan na ci ba.
Cikin kwana biyu naga tsantsar kulawa daga maigidan kamar yadda naga muguwar tsana daga gun kishiyoyina.
A lokacin ne na soma muggan mafarkai masu tsoratarwa da saka razana. Ranar da na fara mafarkin ban mantawa wai ina zaune tsakar gida sai ga wani baƙin maciji ya taho da wani irin gudu kuma Ni ya nufo bakinsa a buɗe. Ko da naga hakan sai na ruga amma abin mamakin shi ma sai ya biyo ni da gudun, na samu na faɗa falo na afka ɗakina kawai sai na iske baƙin macijin nan kwance gefen gadona bakinsa buɗe idonsa na tsiyayar hawaye bai numfashi. Washegari da zazzaɓi na tashi mai zafin gaske ga ciwon ciki kamar abin da ke cikin zai fito don azabar ciwo.
Mafarki na biyu kuma ina,zaune a falo sai ga baƙin macijin ya fito daga ɗakin Hajiya Turai da gudu ya nufo Ni jini na zuba a jikinsa, na ruga ɗakina ina shiga na ganshi sai wulle-wulle yake har ya daina motsi. Wannan mafarkin sai da na kwanta asibiti domin ciwon ciki na dinga yi har da zubar jini, ba ƙaramin razana maigidan ya yi ba, don har ya fini jin zafin ciwon ga alama yadda nan da nan ya rame ya faɗa kamar wanda ya yi wata yana jinya.
Kwana biyu nayi a asibitin amma an kasa gane asalin inda damuwar take komai lafiya a jikina amma jini yana fita wanda an rasa ko na miye jinin. Ƙarshe suka bamu shawarar mu koma mu yi na Islamic zai fi tunda su basu fahimci komai ba.
Haka kuwa akai daga can ya wuce da Ni gun wani mai maganin Islamic ya yi mai bayani, ya yi min tambayoyi sannan ya haɗa mun magunguna ya gaya min yadda zan yi amfani da su muka wuce gida.
Masu gidan na zaune kowacce fuska ba yabo ba fallasa muka iske su, sun zube kaji da lemuka kala-kala gabansu suna ci amma ba wani nishaɗi a fuskarsu tamkar ma dole akai masu na zama cin abincin. Sallamar da mukai ce tasa duk suka watso mana idanuwa, tamkar masu neman wani abu, ganin ɗan cikina daya fara tasowa yasa tare suka ja tsaki suka bar gun ba wadda ta juyo.
"Allah Ya kyauta maku Yasa ku yi hankali." Cewar maigidan kenan yana mun wajen zama bisa kujera.
Cikin Ikon Allah ina fara amfani da magungunan sai jinin ya ɗauke kuma na daina muggan mafarkan da nake duk dare.
Cikina na wata bakwai babu abin da Alh bai siyo min ba duk na ƙasar waje, haihuwar kawai yake jira. Kullum ce min yake so yake na haifi mai kama da Ni, zai farin ciki sosai da hakan.
Cikina na wata takwas wata rana ina zaune ina shan mangwaro Alh bai nan an tura shi Lagos wani aiki na kwana uku, babu yadda ban yi da shi ba kan ya je da Ni amma ya ce sam. Na bari sai na haihu sai na je na kai abin da na haifa amma zai je gun su Inna zai kira Ni a kan wayar gidan mu gaisa. Kamar jiran ya tafi matan gidan ke yi, suka dinga shigowa har sashena suna ci mun mutunci suna gaya min ba zan taɓa haihuwa ba a cikin gidan nan, idan kuma na matsa to tabbas zan ga abin da zai faru daga Ni har shi abin da zan haifa hatta maigidan zai gane kurensa.
Ina zaune ina ta jiran wayar Alh don mu gaisa da su Inna amma shiru sai ga su Hajiya Turai sun faɗo, ba ƙaramar razana ba nayi da ganinsu, domin sirinjin allura ne (injection) cire da ruwan magani a hannun Hajiya Turai, gadan-gadan suka nufo Ni , kafin nayi wani yunƙuri sun taushe Ni Hajiya Turai ta tsira min allurar nan, sai da ta juye ruwan tas sannan suka sake Ni, suka kama dungure min kai suna cewa, "Don uwarki sai ki haihun mu gani ai, ko ba haihuwa ba, to haihun mu amsar maki ita, shegiya mai suffar matsiyatan India." Nan suka fice suna ta shewa suka bar Ni kwance, kafin minti biyu har cikina ya fara yamutsa, nan da nan na fice hayyacina, nakuɗa ta taho min da gasken-gaske, sai kawai naga jini na bin ƙafafuwa na, nishi ya taho da gaske kawai sai jin faɗowar abin da ke cikina nayi, kamar a mafarki naji kukan jariri, cikin farin ciki na saka hannu na ɗauki jararin ashe namiji ne, hakan ya yi daidai da sake shigowar su Hajiya Turai ɗakin.
Tamkar sunga mugun abu haka suka kwartsa uban ihu har suna rige-rigen zuwa inda nake tsugunne da yaron.
Kawai ji nayi an wafce yaron daga hannu na har cibiyar ta tsinke ba shiri ya kuwa yi wani kuka sai ɗaya numfashinsa ya ɗauke.
"Ai wallahi ba dai nan gidan ba zaka rayu ba,yaro kai kyan kai da ka koma inda ka fito, don ko zan yawo tsirara sai ka mutu zan samu sa'ida a rayuwata kambu! Cewar Hajiya Tani kenan tana jijjiga yaron don ta gani ko bai idasa mutuwa ba.
"Ai ke Hajiya Tani gwara ke da sauran imaninki, to Ni na rantse da Allah duk sanda ta sake ɗaukar ciki a gidan nan ta ɗauki ajalinta sai dai ta haihu a lahira." Cewar Hajiya Turai tana tiƙa min dundu a bayana, wanda yasa mahaifa faɗowa ba shiri.
Tsabar rashin tausayi haka suka jefar da yaron gabana suka fice suna shewar jin daɗi. Daidai nan wayar gidan tai ƙara alamar ana kira.
Da sauri Hajiya Turai ta ɗaga kiran cikin muryar kuka tace, "Wayyo Allah Alh! Fatima ta haifi bakwaini amma babu rai, kuma wallahi Alh namiji ne ta haifa ya koma." Ta cigaba da rera kukanta kamar gaske. Ban san abin da ya ce mata ba, dai naji tace, "Yanzu haka tana wanka Hajiya Tani nayi mata, lafiyarta lau yanzu za a rufo yaron don ya yi kuka."
Kalmar kuka da ta ambata tasa nima na ji kukan ya zo min, tabbas kisan kai ne wannan,amma wa zan gaya mawa? Waye gare Ni da zai iya bi min haƙƙina? Yau ga ranar iyayena da dangina, tabbas da muna tare sai sun bi min haƙƙina kan wannan zalunci nasan ko shakka babu ba zasu kashe banza ba.
Haka suka barni ina ta kuka suka fice, da ƙyar na samu na kai kaina toilet na haɗa ruwan zafi ina jin ciwo ina komai na fara wanka na gama na shiga cikin ruwan zafin ina jin tamkar na fice don azaba amma na daure .
Bayan na gama wankan na fita na iske su zaune a ɗakin ko su gyara min, haka na zage na gyara ɗakin na kunna turaren wuta.
Hajiya Turai ta zabga min mari tace, "Allah idan Alh ya dawo gidan nan ki ka gaya mai wani abu daya shafi abin da ya faru sai na lahira yafi ki jin daɗi, wai tsabar neman abin duniya ma wai namiji kika haifa, kan uban can namiji fa ke? Allah na tuba ko mace baki isa ki haifa ba balle namiji ba a gidan nan."
Haka dai suka dinga min kashedi da barazana son ransu suka gaji suka fice suna ƙara jaddada min da kar na yi masu ba daidai ba gun maigidan.
Ba ƙaramar takurawa su ke min ba, cikin lokacin sai da Allah Ya maido Alh sannan suka shiga tattalina suna nuna mugun tausayina gabansa, hakan yasa ya ji daɗi har ya yi mana kyautar zinari mai tsadar gaske.
Ban san me suka tsara ba amma dai naga yanzu idan yana gida to tare muke cin abinci suna ta fira don Ni ban saka baki, saboda nasan duk shiri ne, yana fita suke shigowa ɗakina su yi mun tas, har dukana su ke kamar ɗiyarsu haka suke maida ni bayan idon maigidan.
Sai da ya yi wata guda da dawowa sannan yake gayamin ai ya je gidan Inna amma bata nan, amma an gaya mai ta bar Alawiyya wajen wata Iyami mai saida abinci, ya je can ma ya iske Iyami ta bi dare ta gudu ƙasarsu da yaran ba wanda yasan inda take .
Na yi kuka sosai na shiga damuwa domin na fahimci cewa Alawiyya da Inna sun rabu kenan rayuwar Alawiyya ta shiga cikin gararanba da ha'ula'i kenan. Sai da Alh ya yi da gaske na daina nuna damuwata a gaban idonsa sai ya tafi nake cin kukana iyakar son raina su Hajiya Turai na mun dariya.
Wata rana kamar ance na duba inda nake ajiye kuɗaɗe da sarƙoƙin da Alh ke saimana sai naga babu komai gun, abin ya tabbatar min da cewa an sace su kenan. Duk da ance zargi bai da kyau amma Ni dai su Hajiya Turai na zarga domin ban da kowa sai su, haka zalika ban da ƙawa ko abokan arziƙin dake shigowa gidan da sunan waje na suka zo tunda nake a gidan ban da kowa, to ta ya za a shigo ai min sata? Kamar na gayama Alh sai kuma na fasa na barsu da Allah nasan shi ne kawai zai iya sakamun.
BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR.
Komi ya sauya min baki ɗaya ga ciki ga Alh ya tsane Ni wai an gaya mai duk ɓarin da nayi a baya nice ke zubar da cikin don ban ƙaunar haihuwa da shi, ban san jininsa. Hakan yasa baki ɗaya ya fita sabgata ya daina min magana sannan ya daina shiga sashena ya ce shima cikin na jikina bai so na zubar .
Ga wannan karon wani irin azanabben ciki na samu mai shegen laulayi da kwaɗai amma ban da ikon cin ko da cinyar kaza ce a gidan, sai abin da suka ban kawai don mugunta sun san ban san wake da shinkafa sai suka dinga ban ita kullum safe rana dare, duk sanda na ci sai nayi amai na galabaita na fita hayyacina amma ko a jikinsu, ga shi cikin ya yi wani uban girma ƙafafuna duk sun yi kumburi sosai Ni kaina tsoron girman cikin nake idan ina tsaye gaban madubi.
Haka na sha baƙar wahala har Allah Yasa cikin ya kai wata tara cif, wata rana da rana ina zaune naji alamar haihuwa, kuma na ji motsin maigan a falo don haka na rarrafa na isa inda yake zaune ina kuka na riƙe mai ƙafa nace ya taimaka ya kaini asibiti haihuwa zan yi. Kamar ba zai kalleni ba, kuma sai ya yi sauri ya ɗauki makullin mota dake aje gefensa ya kama Ni muka fice zuwa asibiti.
Da yake haihuwar ta zo gadan-gadan yasa bai nufi asalin asibitin da muke zuwa ba ya kaini mafi kusa kar da na haihu a mota.
Ban jima ba na haifi yarana biyu duk maza cikin ƙoshin lafiya.
Matuƙar murna tasa ya manta da laifin da yake kallona da shi ya rungume ni yana kukan farin ciki yana ta saka mun albarka.
Tun a kan hanya yake faɗawa mutane gidansa an haifi yara biyu duk maza yanzu, ina ga murna ta sa ya manta da gayama su Hajiya Turai haihuwar, sai da mu ka je gida suka ganmu ɗauke da yara a hannu suka zaburo kamar kamun hauka suna tambayar yaran waye kuma mata ne ko maza?
Ni dai da yake ya kira wata tsohuwa ya ce ta dinga ma yaran wanka tana dafa mana ruwan wanka sai na shige ɗaki ina godiya ga Allah da baiwar yaran da ya ban lokaci guda ba tare da na zata ba.
Tamkar hauka haka Alh ya dinga kwaso kaya yana labta min a ɗaki na yara da nawa ne kawai, su kuma su Hajiya ya basu Naira miliyan biyar-biyar ya ce kowacce ta sai kayan suna.
Ranar suna aka raba atamfa da takalma har da dardumar sallah ga duk wanda ya zo taron sunan.
Ni dai da yake ban san kowa ba sai ya kasance duk mutanensu ne cike da gidan da jama'ar Alh.
Bayan suna da sati guda ne suka tare tsohuwar dake zuwa saka mana ruwan wanka sukai mata kashedi suka ce kada ta sake zuwa gidan an kore ta.
Ta shigo ta gayamin nace ta gayama maigidan ya yi masu magana don tana taimaka min sosai duk lokacin da take nan nake samun damar aiwatar da ayyukana yadda ya kamata saboda ban manta kashedin da sukai min ba na cewar sune ajalin yarana duk daren daɗewa sai sun kashe su sun kashe ni idan ta kama har maigidan sai sun haɗa sun kashe ba uwar da za ai.
To sai na dinga rufe sashenina idan Alh bai nan ko tsohuwar ta zo sai na saka makulli na barshi a jikin ƙofar saboda kar su shigo don na tsorata da su sosai na shaida rashin imaninsu gabana suka kashe jaririn wata bakwai.
Cikin nasara tsohuwar ta samu ganin maigidan ta gaya mai ya bata haƙuri ya ce ta dinga zuwa har su girma ita ce mai kula da su shi ya kawo ta ba su ba.
Su ma a ranar sunga ruwan masifa har ya yi iƙirarin duk wadda bata yadda da abin da yake so ba to ƙofar gidan a buɗe take ba wadda ya riƙe a cikinsu zata iya tafiyarta.
Tun daga lokacin sai wasu manyan abubuwa suka fara faruwa a gidan na bayyanar wasu halittu duk sanda aka kwantar da yaran sai su bayyana su kama yagin yaran kamar mage ta yakushe su su dinga kuka, da an zo kuma sai su ɓace.
Tun bai yarda ba har dai wata rana shi ma ya gani da idonsa, hankalinsa ya tashi sosai yana tambata "Daga ina suke Fatima? Waye ya turo su? Kashe min yara za su yi ne?"
Ni dai na gode wa Allah da Yasa ya gani da idonsa, hakan yasa ya ce min na shirya zai ɗauke Ni daga gidan ya sauya min gida saboda rayuwar yaransa.
Ranar da ya tara su Hajiya Turai ya gaya masu abin dake faruwa da abin da ya yanke shawara daya yanke sai su kai tsalle suka dire suka ce ba su yarda ba babu inda zai kai mu.
Shi kuma ya ce basu isa ba ya gama shawara dole yabar gidan nan da yaransa kada wani abu ya same su a banza su ne kawai yaransa duk duniyar nan.
Daren ranar da ya ce washegari za mu tafi wani gidan ina kwance ina barci kawai naga wata mata ta tsago bango ta fito kafin in motsa ta huro min iskar bakinta cikin idanuna kawai sai naji wani irin zafi ya ratsa fuskata kamar wasa na dinga jin zogi a idanuna shike nan sai naga ban gani.
Saboda makantar da ta sameni yasa Alh yabar maganar tashina daga gidan don dole tunda ban gani ga yara kuma.
Sai ya nemi alfarmar tsohuwar nan ta dawo wajena da zama baki ɗaya tunda ga lalurin daya same Ni kuma babu irin neman maganin da ba ai ba amma ba wani alamar zan samu waraka duk asibitin da aka je sai su ce basu ga komai ba su don haka ba abin da za su iya yi min su.
Wata rana muna zaune da tsohuwar nan mai suna Baraka sai ga wasu ƙattin maza sun shigo su Hajiya Turai na biye da su a bayansu, Ni dai ban gani ba amma naji tsohuwar nan na basu haƙuri amma haka suka kwashe yarana suka fice bayan sun yi ma tsohuwar duka guda wanda yasa ta sume. Ni ma haka ba tausayi suka buga min bakin bingida ban sake sanin abin da ke faruwa ba.
Kawai na farka na jini a kan gadon asibiti Alh na zaune riƙe da hannuna yana kuka.
Sai da na kwana biyu sannan aka sallame Ni domin naji rauni a kaina sosai don har aske gashin wajen su kai suka saka min magani.
Lokacin da muka koma gida ashe Alh bincike ya fara na sanin inda aka kai mai yara da su waye suka turo aka kwashe mai yara.
Ban sani ba ko zargi ne yake koko me ya faru oho ashe wai ya saka Camera ko'ina a cikin gidan duk abin da ke faruwa yana kallo a cikin ɗakinsa duk motsin kowa yana gani.
Bayan sati biyu da saka Camerar sai ya zauna ya buɗe don yaga me ya faru da bai nan don ya yi tafiya kwana biyu.
Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin abin da ke faruwa ba, Hajiya Turai da Hajiya Tani ne a zaune sai ga wasu ƙatti su huɗu duk sun rufe fuskarsu ba a gane ko su waye su suna zaune.
Hajiya Turai ce ta fara magana, "Yawwa Dauda yanzu aikinku ya kammala yadda muke so saura abu guda ya rage ku ida mana shi ne ku kawo mana bidiyon kashe yaran da za ku yi mu gani don mu shaida cewar da gaske kun yi mana komai yadda mu ke buƙata."
Ɗaya daga cikinsu ya ce, "Kin gane ko Hajiya wannan duk ba wani abin ji bane ba, kawai ku fara bamu kaso biyar cikin goma da za ku bamu don komai ya tsaya mana."
Hajiya Tani ta gyara zama tace, "Kai Dauda kar da ka kawo mana rainin hankali man, ko ka manta miliyan biyar muka baku ranar da kuka ɗauki yaran? To bari ka ji na gayama mun fi ku son kuɗi domin akan kuɗi muka shiga ƙungiyar asiri har muka bada iyayenmu da ƙwayayenmu kyauta ga dodon tsafi muka zaɓi mu rayu ba 'ya'ya mu tara dukiya shi ne za ka zo kana maganar kuɗi kamar ku ne kuka bamu su ?"
Hajiya Turai ta amshe tace, "Gaya masu dai, tsabar son kuɗi yasa muka haƙura da ganin ƴaƴanmu na yawo a doron duniya don haka kuwa babu sakarkarun da zamu kwashe dukiya mu ba."
Cikin alamar rashin gaskiya ƙattin suka miƙe tsaye suna tafiyar mashaya suna cewa, "No wahala Hajiyoyi sai mun haɗe a ganin gaba mun barku lafiya." Suka fice daga falon.
Kuka ya ƙwace mai ya fito ba kowa falon ya shigo ɗakina ya kama hannuna muka koma ɗakinsa ya ce, "Fatima duk da baki gani amma nasan kina ji don haka saurara ki ji abin da su Turai suka aikata min,duk abin da nake masu bai sa sun tausaya min ba sun bar min yarana biyu da Allah Ya azurta Ni da su ba, so suke su kashe min su kamar yadda suke kashe nasu kamar yadda suka kashe maki idanuwa tabbas sai nayi Shari'a mai girman gaske tsakanina da su Fatima." Ni da shi baki ɗaya kuka muke ba mai iya lallashin kowa.
A haka su Hajiya Turai suka iske mu ɗakin, suka kwashe da dariya suka tafa suka ce, FATIMA ki gode wa Allah da Yasa ba kowane asiri ke tasiri kan ki ba, ki sani duk cikinki da ya zube a gidan nan mu ne nan ke zubar da shi ta hanya ba Dr. maƙudan kuɗaɗe tunda ke tsafi bai kama cikinki yasa muka haɗa baki da shi duk lokacin da kike awon ciki yake zubar da shi kafin ya yi ƙwari.
Shima wannan cikin na yaran nan tsautsai ne yasa muka yanke shawarar mu yi maki sharri ga maigidan kan cewa ke ce ke zubar da duk wani cikin da yake zubewa saboda baki son shi. Cikin nasara kuwa ya yadda da sharrin mu ya juya maki baya har kika samu cikin yaran nan bamu farga ba, lokacin da muka farga kuma ba yadda ba mu yi ba amma cikin ya ƙi zubewa dole muka yanke shawarar idan an kai ki asibiti gun haihuwa Dr ya kashe ko miye ya ce ma Alh kin kashe abin ki gun haihuwa. Da yake munafukan yaran sai sun zo duniya sai ranar haihuwar ta zo mana a bazata kuma sai ba can asibitin ba aka kai ki shi ne yasa har ku ka dawo da yaran a raye.
Amma a Yau za a yita ta ƙare a tsakaninmu da ku, za mu kashe yaran mu kashe uban yaran ke kuma mu ɗora alhakin a kanki , yadda duniya zata shekara tana tsine maki albarka mutanen cikinta na Allah wadai da halinki, mu kuma mu cigaba da cin dukiyar Alh da tsinke hankali kwance...
Shigowar ƙattin nan tasa Alh saurin rarumo inda yake ajiyar bindigarsa amma bata gun.
Ban san ya akai ba na dai ji lokacin da suke ta kokowa har naji kakarin Alh sai kuma naji an kama hannuna an saka min wuƙa a ciki an tura Ni kan jikin mutum. Ina ta lalube na gane Alh ne kwance kuma jini na zuba daga cikinsa, ina a haka na ji ihun su Hajiya Turai suna cewa na kashe Alhaji a taimaka masu.
Sai ji nayi an kama Ni an amshe wuƙar an tasani gaba wanda na fahimci ƴan sanda ne.
Sai jiya bayan fitarku an zo har nan an ja min kunne kan idan ban hana ɗiyata Alawiyya kare Ni a kotu ba za a kashe ta kuma su ma yaran nawa za su kashe su domin har yanzu wai yaran na raye ba abin da ya same su domin jikinsu wuƙa da bindiga duk basu kama su.
Wannan shi ne asalin abin da ya faru bayan rabuwarmu da ku Alawiyya." Cewar Fatima cikin goge hawayen idonta.
Gandurobar data kawo Fatima ce ta dawo tace, "Ranku ya daɗe lokaci ya yi na komawarta ciki."
Ba tare da Barista Alawiyya ta dube ta ba ta kama hannun Fatima ta miƙar da ita tsaye tace, "Mama ku je ki kwanta Yau ki yi barci ki huta indai da gaske Ni ɗin ke kika haifeni kuma ta hanya mai inganci to ko sama da ƙasa za su haɗe sai na ƙwatar maki ƴancinki haka sai na nemo ƙannena duk duniyar da suke.
Tabbas wuƙa da bindiga basu tasiri a jikin zuri'arki domin ko Ni nan basu kama Ni ba ƙarya su kai ba."
Ta fice ba tare da ta sake waigen kowa ba a gun.
Fitar su ke da wuya sai maigadin gidan ya fito da waya ya kira wata lamba ya yi magana ya kashe ya koma ya zauna yana tsira ma motocindu ido kamar mai yin nazari.
To fa ya kenan jama'a? Ana wata ga wata fa!
Taku a kullum Haupha!!!
managarciya