INA DA HUJJA: Labari Mai Sosa Zuciya Fita Ta 13

INA DA HUJJA: Labari Mai Sosa Zuciya Fita Ta 13

 Page 13      

 

 

Washe gari ranar Litinin ce, kuma ranar Malam Muntasir zai dawo daga garinsu, ga shi Lantai duk abin ta tana matuƙar shakkar Malam Muntasir domin bai wasa da ita, haka bai dukanta amma yana sakata aiki harta gaji tai kuka don kanta.

 

Hakan yasa tana tashi yau da wuri ta dubi Inna Kande ta ce, "Don Allah Inna Kande Idan Malam Muntasir ya dawo kada ki ba shi labarin komi ki rabu da shi kawai saboda yana iya cewa wani abin na kwashe na gayama Yayana Barbushe kin san dai tsab zai sossoke shi da adda Wallahi."

 

Inna Kande ta saki baki tana kallon Lantai wadda ita littafi ne a hannunta tana karantawa take maganar.

 

"Wai ni Lantai da gaske labarun ƙaryai za ki dinga karantawa mutanen ƙauyen nan ?

Kallon Inna Kande take tana jin inama ace ba ita ce tai wannan furucin ba ? Inama ace wani ne ko wata daga ƙauyen nan ? Tabbas yau da yasan ya ambaci sunan labarin Jarumi Nasimat da ƙarya, domin babu abin da zai hanata fashe ma shi baki.

Sarai Inna Kande ta fahimci Lantai ta ji haushi sai ta share ta ce ta je ta siyo mata goronta wanda a rana sai ta ci na ɗari biyu ko fiye da hakan ma.

 

Lantai na zumɓura baki ta amshi kuɗin goron ta fice daga gidan.

 

Tana cikin tafiya baban ɗan mai gari ya ganta, ya kwana biyu bai ƙauyen safiyar yau ya dawo ake ba shi labarin abin da taima mahaifinsa don haka bai tsaya jiran komi ba ya saka ƙafa ya kifar da ita ƙasa ya kama dukanta.

 

Malam Muntasir da zuwansa kenan ƙauyen yana kan mashin ya hango Lantai da abin da yaron yayi mata ya sauka daga kan mashin ɗin ya isa gun da gudu ya dinga kashe fuskar yaron da mari yana ƙarawa.

 

Lantai kuwa duk abin nan hankalinta a tashe yake domin taji kamar littafinta ya yage lokacin da ya kadata yana duka.

 

Da hanzari ta tashi tsaye tana duban yadda littafin ya cukuikuye kamar ba shi ba.

Ganin Malam Muntasir ne ya shigar mata faɗan ga shi littafin nasa ne sai ta tura littafin cikin hijabinta ta ɓoye ta kama kama Malam Muntasir dake ta jibgar ɗan gidan mai gari ta ce, "Malam ka ƙyalesa nayi masa Allah Ya isa ai, tunda ba abin da nayi masa ."

 

Da mamaki Malam Muntasir yake bin Nuratun domin dai yasan ta sarai kan neman faɗa balle an tone ta.

 

Amma dai ya ƙyale yaron yana tambayarta ina zata ?

 

Sai da ta zumɓura baki ta ce, "Inna Kande mana ta aike ni. Ni Allah na gaji da siyen goron nan kullum ma sai ta fashe da kuka sosai kamar yanzu ake dukanta.

 

Malam Muntasir ya dafa kanta, "Haba Nuratu yanzu aiken Inna kike ma kuka ba dukan da yaron can yayi maki ba ?"

 

"Tab ina zan ma aiken Inna Kande kuka Malam ? Ai kukan zuwanka nake lokacin da bai kamata ba, na rantse da Allah da baka zo ba da yanzu nayi abin da sai Lado yayi kuka shi da mai gari, amma ko yanzu sai yasan yayi min mugunta...

"Nuratu ki daina kukan ki koma gida ni zan kawo mata goron kin ji ?

Kanta ta ɗaga tana ƙara ɓoye littafin a cikin hijabinta.

 

"Amma Nuratu kamar da littafi na hangoki kina karantawa ko ? Yana ina littafin ? (Yana maganar yana kallon wajen wai ko littafin ya faɗi)

 

Lantai ta ƙara ƙarfin kukanta ta nufi hanyar gidansu tana ihu da ambatar ta bani ta lalace ta shiga uku ita Lantai.

Girgiza kanshi yayi ya wuce yana ƙara jinjina halin Nuratu na nuna masa wayau muraran.

 

Tunda Inna Kande ta jiyo ihun Lantai hantar cikinta ta katsa zawo na neman kubce mata, tasan duk wanda ya taɓo Lantai ya jawo masu bala'i yau.

 

Lantai kuwa tana shigowa gidan ta shige ɗaki sai ta haye gado ta fito da littafin tana kallon yadda ya koma.

 

Hankalinta sosai ya tashi ganin littafin ya yage har bangon littafin ya fita daga jikinshi.

 

Ido ta runtse ta cigaba da zabga uban ihu tana kiran ta bani ta shiga uku ta lalace ita Wallahi ba zata yadda ba, dole ran uban kowa ya ɓaci tunda aka yaga mata ido Wallahi Tallahi ta rantse har da girman Allah yau kowa sai ya ji abin da ta ji.

 

Musa da shima ya ji to kukan Lantai ɗin daga inda yake zaune cikin zaurensu sai da gabanshi ya faɗi, amma tunanin ko Yayanta Hafiz ne ya dawo yasa hankalinshi ya ɗan kwanta kaɗan, domin kowa yasan kukan Lantai bala'i ne mai digiri a ƙauyen.

Kawai ji yayi hankalinshi bai kwanta ba don haka ya shiga gidan don jiyo abin da akai mata.

 

Yana shiga ya iske Inna Kande sai zare ido take tana duban hanya sai ya ji shima kamar ya koma , amma ta riga ta ganshi dole ya shiga.

 

Sanda suka ji Lantai ta ce, sai kowa ya ji abin da taji a ƙauyen kallon juna su kai a firgice sun san yanzu ta kira Barbushe ya nemi kashe mutum a banza.

 

Musa ne yayi ƙarfin halin zuwa kusa da ita.

 

"Lantai ba girmanki bane ki dinga kuka irin wannan ba, kada ki manta kin gama primary fa haba Lantai."

 

"Bayan an yaga min littafi kake cewa wai ba girma na bane kuka ? Wallahi yau sai an san an yaga min littafin Jarumi Nasimat na rantse da Allah."

Musa ya ƙara karya murya zuwa ta lallashin Lantai.

 

"Lantai kin fa girma kin isa zance don dai kawai kowa tsoranki yake da yanzu an fitar maki da miji ai, ki tuna fa ƙawayenki duk sun tsaida maza baɗi za a kai su ɗakunansu na aure, don Allah Lantai ki daina samu a tashin hankali kin ji ?"

 

Dirowa tayi daga gadon bata damu da yadda yatsanta ya kwashe ba har jini na zuba ta miƙa masa littafin hawaye wani na bin wani a idonta ta ce,  "Yaushe Lantai za tai haƙuri an yaga wannan muhimmin littafin na Jarumi Nasimat ?

 

Yaushe Lantai tasan ta girma indai ba gama karanta duk wasu littafan jarumi Nasimat tayi ba ?

Kasan Allah ? Yau ba sai gobe ba sai na girgiza duk wanda ke cikin garin nan idan ka cire mutane biyu rak !

Shima na farko don littafin nasa ne, sai kuwa Inna Kande Kakata amma bayansu kowa zai san ni Lado ya daka ya yagama littafi Musa."

 

Muƙut Musa ya haɗe miyau cike da gasgata tunanin aljanu ne akan Lantai yace, "Lantai don Allah ki yi haƙuri Lado fa bai san komi akan ki ba yau ya dawo daga Maraya don Allah ki bar mai gari haka nan an ce yana can kwance bai da lafiya ."

 

"Musa ni fa da a taɓa littafin nan gara an kashe ni Wallahi."

 

"Subhanallahi !

Lantai me ya kawo maganar kisa kuma ? To me yasa baki hana shi taɓa littafin ba Lantai ? Ai dai Lado ba fin ƙarfinki yayi ba."

 

"Ai Wallahi ban san da shi ba kawai ya rufe ni da duka sai da Malam Muntasir ya ƙwace ni.

Naso a ce ba shi ne ba ya zo wajen nan ba, Allah da yau Lado ya gane kurensa hannuna amma ko yanzu sai na rama kanku tunda nasan daɗi kuka ji a ranku."

 

Ko da Musa ya ji Malam Muntasir ya zo sai ya ji sanyi a ranshi yasan shi ne kawai mai iya lanƙwasa Lantai kaf ƙauyen nan a yanzu.

Don haka ya samu ya fice ya nufi gidan Malam Muntasir kai tsaye cike da tashin hankali.

 

Malam Muntasir yana ta fiddo sabbin littafai wanda ya dawo da su daga gida, domin Allah yayi masa son karatun littafan Hausa sai ga Musa ya shiga ko sallama babu don a ruɗe yake kada Lantai ta nufi gun Barbushe.

 

Musa cike da ruɗani ya korama Malam Muntasir abin da ya faru sanda bai nan tas.

 

"Nuratu Kabir yarinya mai abin mamaki tare da shiga rai." Cewar Malam Muntasir yana murmushi.

 

Har ga Allah yarintar yarinyar birge shi yake don haka ya nace ma zama ƙauyen duk da cewa danginsa na son ya koma garinsu da aiki amma saboda Nuratu Kabir ya kasa barin ƙauyen.

 

Musa kuwa sai ya koma sakarai ganin Malam Muntasir sai murmushi yake dan jin daɗin abin da Lantai ta aikata .

 

"Malam Musa ka je gani nan zuwa yanzu insha Allah.

Wane littafi ne gun Nuratun yanzu ?

 

"INA DA HUJJA, shi ne Lado ya yaga mata." Cewar Musa.

 

Ganin Musa duk ya tsorata yasa Malam Muntasir tashi yace su je gidansu Lantai ɗin.

 

Suna shiga suka iske mai gari da jama'arsa zaune jugum-jugum kamar anyi mutuwa kowa fuska ba fara'a kamar ace ƙat ya ruga.

 

Tambaya yake "ina Nuratu Inna?"

 

"Lantai ta tafi da kukanta gun Barbushe ta rantse yau ƙauyen nan kowa sai ya ji yadda ta ji wai."

 

Sai mutanen wajen suka ɗauka baki ɗaya.

 

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un !

 

Abin kamar yayi dariya sai kuma ya dake, wai akan ƙaramar yarinya suke wannan sokoncin hada mai gari ?

 

Sai ya nemi waje ya zauna shi ma yana sake nazarin yadda kowa ke cike da fargaba a wajen.

 

Ƙarar busar sarewar Barbushe su ka ji sai ga su mai gari ana rige-rigen ɓoyewa, sai gwara kawuna suke ƙum suna zubewa ƙasa.

 

Shi dai Malam Muntasir kallonsu yake cike da mamaki .

 

"Kai ina namiji ga ubanshi ?

Ina jarumi ga ubanshi ?

Ina sadauki ga ubansa ?

Yayan Nuratu ikon Allah, baka dariya sai ka ga jini.

Fara'arka ka ga jini na gudu .

Waye ya taɓo Nuratu yau ya kwana kiyama ?

Cau-cau maigida kai ne uban duk wani marar kunya."

 

 

Haupha