INA HUJJAR TAKE:Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Hudu

Bakinta ta riƙe (Kai ni fa Malam idan ba ganin littafin can nagani a hannuna ba na rantse ba ganin natsuwata za kai ba) cikin ranta take maganar.

INA HUJJAR TAKE:Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Hudu

     Page 4

 

 

Natsuwa tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa, amma sunan marubucin na yawo acikin zuciyarta.

 

NURA SADA NASIMAT.

 

Sunan kanshi ya matuƙar birgeta, gaskiya ko ina marubucin nan yake na dabanne, duba ga yadda ko kalaman cikin littafin na daban ne.

 

Yau kam ko zata kwana nan sai ta tafi da littafin can.

Ɗagowa tayi don taga sunan littafin amma sai taga ya a je littafin ya kafa mata mayun idanunsa masu tsorata ta.

Nan da nan ta birkice ta kama in'ina "Ma.. lam... Ina wuni ?

 

Banza yayi da ita  ya cigaba da kallonta kawai.

 

Ta sake maimaitawa "Ina wuni Malam?

 

"Daman yanzu wuni muke ciki?

 

Bakinta ta riƙe (Kai ni fa Malam idan ba ganin littafin can nagani a hannuna ba na rantse ba ganin natsuwata za kai ba) cikin ranta take maganar.

 

"Nuratu Kabir me ke faruwa dake ne ?

Kina abu kamar wata wadda bata san kanta ba?

 

Kallon inda ya aje littafin tayi tana maganar zuci "Aiki ya sameka Malam indai akan littafin Jarumina Nasimat ne na rantse ka kira ni da kowane suna zan amsa."

 

"Nuratu ba magana nake maki ba ?

 

Ta dube shi a ɗan tsorace ta ce, "Malam ina fama da ciwon kai ne mai saka hawaye a kwanakin nan."

 

Ya dubeta da mamakin yadda take son raina masa hankali yace, "Shi ne kuma kike ta surutai kina ambatar Hidaya dasu Sadik ?

 

Da sauri ta kalleshi "Haba Malam kamar dai wadda ta ci kai ? Sai kuma tai sauri ta dafe bakinta.

 

"Nuratu wane littafi ne kike karantawa wanda kika ce nan aka baki shi ?

 

"Nan kuma ɗaya Malam na rantse ko da wasa baka sanin shi." Cewar zuciyarta a fili kuma sai ta fara dafe kanta alamar ya fara sara mata .

 

Murmushi yayi ya fice daga office ɗin.

Da gudu ta isa kan tebur ɗin ta ɗauki littafin ta karanta sunan...

    DORON MAGE

            Na

 

Nura Sada Nasimat

 

 

"Wayyo daɗi kashe ni kowa ya huta kawai !

 

Bangon littafin take kallo yadda taga zanen yasha banbam da wancan littafin sai abin ya sake birgeta ainun.

 

Ta sumbaci littafin tana cewa "Yau zan gama karanta ina hujjar take na ɗora da kai...

Jin motsin shigowar Malam Muntasir yasa ta aje littafin ta koma yadda take, fuskarta ɗauke da murmushi.

 

Magani ya miƙa mata tare da ruwa.

 

Yi tayi tamkar bata fahimci me yake nufi ba.

 

"Maza ki sha maganin ciwon kan mu fara karatun."

 

"Yau nake ganin ikon Allah ni Lantan Inna magani kamar wadda ke magashiyan ?

 

"Au sai kina magashiyan kike shan maganin ? Cewarsa.

 

"Malam maganar gaskiya Inna Kande faɗa take idan ina shan irin wannan maganin na turawa tafi amincewa dana gargajiya."

 

Kallonta kawai yake yarinyar akwai shegen wayau.

 

"To indai mutum yasan bai son magani kada ya sake cemin bai da lafiya ."ya faɗi yana aje maganin da ruwan.

 

Kallonshi take tana kallon inda littafin yake aje .

 

"Malam ni ba wani karatu ko ciwo ne damuwata ba, yadda zan mallaki littafin can shi ne kawai babbar damuwata na rantse ko kaffara banyi dole littafin nan ya je hannuna yau." Abin da kawai take nanata wa kenan a zuciyarta.

 

Littafin daya tsara zai dinga koya mata ya ɗauko ya  bata wani ya soma karanta mata.

 

Sai dai hankalinta baki ɗaya yana kan wancan littafin don haka da yayi magana sai taga kamar labarin littafin ne zai bata.

 

Shi kam ya dage tsakani da Allah sai koya mata yake bai kula da hankalinta ba kanshi yake ba sai da ya tambaye ta , ita kuma sai taji kamar yace Nura Sada, ai kuwa da hanzari ta ida ma shi da "NASIMAT."

 

Kallonta yake yana don fahimtar me take nufi, don sam bai san ma'anar abin da ta ce ba domin Hausa yake koya mata ba turanci ba, balle yace wata kalmar turanci ce ta yi ma shi ƙwaba .

 

"Nuratu me kika ce ?

Tana murmushi ta sake maimaitawa "NASIMAT nace Malam."

 

"Ina kika samo wannan kalmar ?

Cikin wane darasi take ?

 

Sai yanzu ta ankara da kwabsawar da tayi, ta gimtse fuska ta ce,  "Malam sai naji kamar kace hakan ai, daman Inna Kande ta ce banjin magana sosai ashe daman da gaske take ?

 

"Kallonta yake yana tunanin idan ta ƙara girma wai ya za ai kenan ?

Tabbas akwai tarin abubuwa kan lamarin yarinyar nan, gata da shegen wayau ga mugun rashin ji da uwar kafiya duk halayenta ne.

 

Ta kalleshi ta ce, "Malam zan iya tambaya ?

 

Sosai ma kuwa za ki iya indai ta shafi karatunmu ."

 

"Malam miye fassarar Nasimat da Hausa ?

 

Kallonta yayi yace, "Da turanci kika faɗi kalmar kenan ?

 

Kanta ta ɗaga domin harga Allah so take ta san abin da Nasimat yake nufi tasan dai zai bada ma'ana mai inganci .

 

"A cikin wane darasi aka koya maki wannan kalmar ?

 

"Malam na ɗauka Hausa muke kuma kalmar ta Hausa ce ai."

 

"To maza ki aje domin ban san kalmar ba amma idan kika gayamin cikin darasin da aka koya maki ita zan iya bincika na sani ."

 

"Akwai aiki kuwa domin sunan Jarumi Nura Sada Nasimat ne ta tambaye shi saboda tasan dai Nura sunan ne hakama Sada amma Nasimat ne abin da bata gane ba .

 

"Malam inaga ba haka kalmar take ba , idan na gano zan gayama."

 

Kallon lokaci yayi yace, "Zamu dakata anan sai kuma gobe idan mai duka ya kai mu."

 

"Kambu ! Wallahi zama yanzu na fara tunda bai zo hannuna ba littafin can Malam." Maganar zuciyarta kenan.

 

Ganin tayi kamar bata ji abin da yace ba yasa ya sake maimaita mata.

In'ina ta fara yi, "Am daman da zan fito daga gida, am Inna Kanden ta tafi gidan barka ta ce am kar na koma sai ta koma saboda ɓarna."

 

Mamaki bayyane kan fuskarshi wai Nuratu ce da son zaman makaranta tai karatu, tabbas ya ji daɗin sauyin da aka samu.

 

Don haka ya miƙe tsaye yana cewa, "To ni zan shiga class don haka ki karanta abin da mu kai sai na dawo sai mu ƙara wani darasin." Ya fice .

 

Ta kuwa miƙe tsaye taita juyi tana rawa bakinta ya ƙi rufuwa don farin ciki .

Har rawa hannunta ke yi wajen ɗaukar littafin.

 

Sunan littafin kansa abin mamaki da al'ajabi ne wai DORON MAGE kai jama'a Allah ya zubawa jarumina Nasimat shegiyar basira ta bugawa a labarai ni Lantai.

 Ai tunda Malam Muntasir ka bari na fahimci kana karanta littattafan jarumi Nasimat na rantse babu mai rabani da kai duk ƙauyen nan .

 

Sunan marubucin kawai take kallo tana murmushi, "Tabbas nasan duk inda kake kyakkyawan gaske ne, sannan dole komi naka ya fice daban Nasimat.

 Tunano wasu kalamai da Hasib ke gayama Hidaya take tana ƙara sallamawa jarumin marubucin nata Nasimat.

Kawai sai ta ga dacewar ta gwada yadda masoyan ke furta kalaman soyayya ga junansu ranar da suke cikin shauƙi .

 

Lantai ta karkace ta buɗe murya irinta maza ta ce.

 

"Soyayya ruwan zuma,

In ka sha ka ba masoyi. Hidaya ƙaunarki

ta tsotse dukkan jikina ta sa ni zubar hawaye Hidaya ki taimaka ki mallaka min zuciya da ruhinki haɗa da gangar jikinki don cikar soyayyarmu."

 

Sai kuma ta sake maƙale murya ta ce.

"Hasib nawa gwanina akanka ban da buri balle ra'ayi kulawarka ke samun natsuwa sonka ke samun farin ciki ga ni ga jikina baki ɗaya babu bare gareka."

 

Ya jima yana kallonta yana mamakin yadda akai ta iya wannan dirama.

Wai su waye Hasib da Hidaya ne gareta ?

 

Yana da kyau ya bita sannu don gane inda ta dosa.

Bai magana ba ya samu waje ya zauna ya cigaba da kallonta ita kuma ta dage sai tai muryar namiji tayi ta mace .

 

Daya kula bata da niyyar dawowa hayyacinta ya daka mata tsawa.

"Nuratu yaushe kika koma mawakiyar soyayya ne ?

 

Cikin sauri ta rarumi littafin ta ɓoye ta sadda kanta ƙasa tana haɗe rai wai kada yace zai bugeta bayan ta gama makarantar.

 

Hanya ya gwada mata yace, "Maza wuce gida kada ki sake na sake jin labarin an ce kina kuka ko wani shirmen banza."

 

Da gudunta ta wuce tana dariya ƙasa-ƙasa don ta ɗauke littafin, burinta ya gama cika.

 

Tana fita ya duba yaga ba littafin ya fita da saurinshi don ya kirata sai ya hango ta gudu kawai take ba ko waiwaye .

 

Dariya yayi yace, "Nuratu baki ji sam, amma zan maganinki."

 

 

Mu je dai zuwa Lantai ta samo wani littafin marubuci Nasimat ko ya zata kaya kuma ?

 

Wane mataki Malam Muntasir zai ɗauka akan Nuratu tunda ya gane ita ce ke ɗauke littafan ?

 

Haupha 

 _Wannan page ɗin kyauta ne sukutum gareki Hubby ta Real Nana A'isha Maraɗi, tabbas ke ɗin ƙawata ce ta amana ina fatan Allah Ya barni dake har ƙarshen rayuwa