Mawakin Finafinnan Hausa ya rasu sakamakon bugun zuciya

Mawakin Finafinnan Hausa ya rasu sakamakon bugun zuciya
Allah Ya yi wa fitaccen mawaƙin Hausan nan Elmuaz Birniwa rasuwa a ranar Laraba da maraice.
Rahotanni sun ce ya rasu ne sakamakon bugun zuciya a lokacin da yake halartar bikin abokin sana’arsa mawaƙi Auta Waziri.
“An je ƙwallo irin ta aure ɗin nan wasu ma sun ce ba a gama ta ba sai ya ce jiri na kwasarsa, daga haka sai ya faɗi. Aka ɗauke shi aka wuce da shi asibiti a nan Kaduna, to bayan kamar awa guda ne asibitin suka ba da sanarwar cewa Allah Ya yi masa rasuwa," kamar yadda Furodusa kuma jarumi a Kannywood Falalu Dorayi ya shaida wa TRT Afrika Hausa.
Elmuaz ya kasance mawaƙi, marubucin waƙoƙi, furodusan fina-finai, sannan kuma shi ne mataimakin ƙungiyar mawaka ta Murya Daya.
Waƙoƙinsa sun haɗa da jan-hankali da wa’azantarwa da kuma na siyasa.
Za a yi jana’izarsa a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 1 na rana a Kaduna