Gwarawa Da Hausawa Duk Ɗaya Ne Buƙatar Mu Cin Zaɓe- Shugaban PDP A Neja

Gwarawa Da Hausawa Duk Ɗaya Ne Buƙatar Mu Cin Zaɓe- Shugaban PDP A Neja

 

 

Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna

 

 

An bayyana cewar masu yawo da kalmomin ƙabilanci a siyasa ba masoya cin gaban ƙasa ba ne, dan haka Bahaushe da Bagware ɗaya ne a wajen mu buƙatar jam'iyyar  PDP karɓo mulki daga hannun APC da ta ruguza tsarin dimukuraɗiyya ta hanyar amfani da ƙiyayya a tsakanin al'umma da ke zaman amana wanda a shekaru bakwai zuwa takwas ta kasa aiwatar da komai na cigaban ƙasa face mayar da abubuwa baya da ya jefa rayuwar al'umma cikin halin ha'ula'i ta fuskar raahin tsaro, walwala da ƙarin tsadar rayuwa.

Shugaban jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Bosso ta jihar Neja, Malam Ɗanlami Aliyu ne ya bayyana hakan a lokacin da ɗan takarar majalisar dokokin jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar, Ambr. (Dr) Nura Hashim (Tallafin Bosso Ƙarami) ya ziyarci sakatariyar jam'iyyar dan gabatar da buƙatarsa na tsayawa takarar a shekarar 2023 mai zuwa.

Malam Ɗanlami, ya cigaba da cewar zuwa yanzu ‘yan takara biyar ne suka sayi fom dan yin wannan takara, amma yau Dr. Nura Hashim kai ne na farko da ka ziyarci sakatariyar mu ta ƙaramar hukuma dan bayyana mana burin ka na takara a hukumance, kowa ya shaida jam'iyya ta baka damar cigaba da zantawa da iyayen jam'iyya, wakilai masu zaɓe dan gwada ƙunjin ka a wannan manufar ta alheri.

"Sanin kowa ne, jam'iyya na da ƙudurin samar da ɗan takara tilo da aka yi yarjejeniyar  amincewa da takararsa tsakanin ƴan takara amma idan hakan bai samu ba, ba mu da wani zaɓin da ya wuce yin zaɓen cikin gida na fitar da ɗan takara kamar yadda dokar ƙasa ta amince da shi.

Ina jawo hankalin ka akan abinda ka sani dole cikin ku biyar ɗin nan dole ɗaya ne zai zama ɗan takara, dan haka ina ƙara nusar da kai da ku haɗa kai a tsakanin ku dan ganin jam'iyyar mu ta kai ga nasarar da muke buƙata. Yau ina zango na biyu a wannan kujerar kuma babban burina in tabbatar PDP ta ƙwace dukkanin kujerun da APC ta mamaye a zaɓen 2023.

Da yake bayani, darakta janar na yaƙin neman zaɓen ɗan takarar, Alhaji Abubakar Boboi, yace ya amince da jagoranci wannan tafiyar ne saboda dacewar ɗan takararsa, domin ya taɓa riƙe matsayin mai taimakawa gwamna na musamman a ɓangaren matasa kowa ya shaida irin rawar da ya taka, bayan nan ko bayan APC ta ƙwace mulki, Dr. Nura Hashim bai zauna kara zube ba, ya cigaba da lalubo hanyoyin da mata da natasa ke anfana ta hanyar haɗa hannu da ƙungiyoyin waje dan tallafawa rayuwar matasa.

Saboda haka ina da tabbacin idan PDP ta ba shi wannan damar, tarihi ba zai iya mantawa da Dr. Nura zai samar a ƙaramar hukumar Bosso ba.

Ɗan takarar a bayaninsa, ya bayyana cewar yazo jam'iyya ne dan haɗuwa da shugabannin jam'iyya, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki dan bayyana ƙudurinsa na neman tsayawa takarar wannan kujerar.

justify;">" Ku sani iyaye na da shugabanni a wannan jam'iyyar mai albarka, ga Allah mu ke nema kuma gare ku muke nema. Idan Allah ya ba mu iko kun amince mana kuma har mun kai ga nasara, a ƙaramar hukumar Bosso kuma a wannan kujerar za mu tabbatar mun kafa tarihi, muna da hanyoyi da dama da al'ummar Bosso zasu anfana, amma muna buƙatar wannan kujerar ne ta zamo mana matakala, duk abinda muka samo tsarin da shugabannin jam'iyya suka fitar da shi za mu yi anfani.

Tun daga yanzu har zuwa samun nasarar mu ƙofa a buɗe take ga dukkanin wani mai shawara, buƙatar mu haɗin kai, lalubo hanyar cigaban jama'ar Bosso"

A ƙarshe shugaban jam'iyyar PDP ɗin ya bayyana cewar kar wani ɗan takara ya riƙa farfagandar cewar shugaban jam'iyya ta jiha, Barr. Tanko Beji ne ya fito da shi takara dan ganin cewar shugaban jam'iyyar ta jiha ɗan ƙaramar hukumar ne, Tanko Beji duk ƴaƴan jam'iyyar nan na shi ne bai da gefe, muna buƙatar haɗa kai PDP ce a gaban mu ba ƙabilanci domin dukkanin wani gida da ka sani a Bosso akwai auratayya tsakanin Hausawa da Gwarawa, dan cigaban jam'iyya, cigaban ƙaramar hukumar Bosso shi ne burin mu.