2023 Tambuwal ne maslahar Najeriya -------Kungiyar Matasan Arewa

2023 Tambuwal ne maslahar Najeriya -------Kungiyar Matasan Arewa
2023 Tambuwal ne maslahar Najeriya -------Kungiyar Matasan Arewa
 
Daga Habu Rabeel, Gombe
 
Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya ta Northern Youth for Tambuwal (NYT) sun bayyana cewa gwamna Aminu  Waziri Tambuwal, ne maslaha ga matsalalon kasar nan muddin ya yarda ya amsa kira ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2023.
 
Matasan sun bayyana hakan bayan zaman mitin da suka gudanar daban-daban inda suke kiran gwamnan jihar Sakkwato Aminu  Waziri Tambuwal, da ya amince ya amsa kiran matasan Arewacin Najeriya ya tsaya takarar shugabancin Najeriya domin shi ne ake ganin zai iya cirewa Najeriya kitse a wuta.
 
Matasan sun bayyana hakan ne ta bakin shugaban kungiyar su na shiyar arewa maso gabas Hon Ibrahim Muhammad Inuwa, a lokacin da ya jagoranci mambobin a taron su  da 'yan jarida a tsangayar yan jarida dake Gombe  ya ce kasancewar Tambuwal shugaban kungiyar gwamnoni kuma tsohon shugaban majalisar Wakilai ta taraya ya bar abun misali da ya isa a ba shi damar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa.
 
Ibrahim Inuwa, yace a lokacin da yake shugaban Majalisa ya yi shugabancin da har ya gama ba’a same shi da almundahana ba kuma a yanzu da yake shugaban kungiyar gwamnoni da yana da matsala da za su sauke shi amma ganin ya iya jagoranci yasa suke jin dadin sa kuma suma za su mara masa baya.
 
A cewar sa batun bangaren ci na cewa yankin kudu na son mulki Arewa n son mulki ba zai hana su marawa Tambuwal baya ba domin su damuwar su shi ne ana yin gwamnati babu su ne amma idan suka tabbatar za’a ja su a jiki a tafi tare za su yarda su marawa dan arewa baya.
 
Sannan yace Tambuwal Matashi ne da yake da jini a jiki da duk inda ake bukatar sa zai iya zuwa ba tare da jin kiri ba saboda mafi yawan lokaci mutum mai shekaru baya iya gudanar da ayyukan da ake bukata akan lokaci saboda shekaru sun kama shi.
 
Shi ma da yake tofa albarkacin bakin sa Kodinatan NYT na jihar Gombe Malam Jamilu Muhammad Inuwa, karin haske ya yi da cewa ko su gwamnonin PDP  da Tambuwal yake shugabanta za su iya gamsar da yan kudu hanyoyin da Tambuwal zai karbu a wajen su duk da cewa idan ana maganar yawa ne su basu da yawan 'yan Arewa.
 
Malam Jamilu Inuwa, yace ta kowacce hanya Aminu Waziri Tambuwal bai da illar da za’a kama shi da wani laifi na zargin da zai hana shi takara a jam’iyyar sa ta PDP.
 
Daga nan sai suka kara yin kira da babbar murya kan cewa addu’ar su shi ne Tambuwal ya yarda ya amince ya amsa kiran matasan arewacin Najeriya ya tsaya takarar neman kujerar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar PDP domin a yanzu babu kamar sa  wanda idan aka tantance sauran zai iya zama dan takara sabaoda nagartar sa.