Tambuwal Ya Fasa Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2023?

Tambuwal Ya Fasa Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2023?

 

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ce zai fara tuntuɓa kan tsayawa takarar shugaban ƙasa da mutane da dama ke bukatar ya fito a zaɓen 2023 dake tafe nan da karshen watan Fabarairu zai sanar da matsayar da aka cimma.

Gwamna Tambuwal a harabar hidikwatar jam'iyar PDP bayan ya kaddamar da babban ofishin jam'iya na jiha a Litinin data gabata  ya ce kowane al'amari na Allah ne yana yin yanda yake so haka abubuwa ke tafiya sun gode Allah  siyasa haka take a cikin gwagwarmaya.

"Na fara wannan aikin ne daga yau(litinin) za mu kare wannan aikin na tuntuba na dawo wa 'yan Nijeriya da bayani karshe abin aka cimma a karshen watan biyu da ikon Allah," a cewar Tambuwal.

 Managarciya ta jefa wannan tambayar Tambuwal ya fasa tsayawa takarar shugaban kasa a 2023? Saboda ganin yanda ya tsara  sanar da duniya tsarinsa kan tsayawa takarar shugaban kasa ba a cika maganar ba, abin da ya kawo tangarda bai fito ba a hukumance.

Da yawan mutane sun zuba ido da cewa Tambuwal zai sanar da matsayar da aka samu a wurin tuntuba da ya yi a karshen wata Fabarairu kamar yadda ya alkawanta, amma an ji shiru har wani wata ya fara tafiya hakan ya jefa alamar tambaya kan wannan tafiyar da ake son samun nasararta, amma ta fara da samun tsaiko wanda ba a fito fili aka gayawa mutane mine ne dalili ba.

Duk kokarin samun mai baiwa Gwamna shawara kan yada labarai Muhammad Bello lamarin ya ci tura ya kasa daga kiran wayar da aka yi masa domin sanin mine ne ya kawo wannan tsaikon na cika alkawalin da aka yi wa al'ummar Nijeriya saboda an barsu suna garari kan takarar Tambuwal a 2023.