NNPP ta tsayar da mace a matsayin ƴar takarar Ciyaman a Kano

NNPP ta tsayar da mace a matsayin ƴar takarar Ciyaman a Kano

A yayin da zaɓen ƙananan hukumomi ke kusantowa a Kano, jam'iyyar NNPP ta zaɓi Sa'adatu Salisu Tudunwada daga Kano ta kudu a matsayin ƴar takara r shugaban ƙaramar hukumar.

Sa'adatu dai ta zama ƴar takara ɗaya tilo cikin 44 da aka tsayar domin neman kujerar shugabancin ƙaramar hukuma.

Haka kuma, jam'iyyar ta tsayar da ƴan takarar Kansiloli 484 a faɗin jihar.

Shugaban jam'iyyar NNPP na Kano, Hashim Dungurawa ya tabbatar da cewa ƴan takarar sun shirya shiga zaɓen.

"Hanyar fitar da ƴan takarar mu ya haɗa da zaɓuka da tabbatarwa da nuna goyan baya, waɗanda dukkan su an amince da su", inji shi.

Dungurawa ya kuma yabawa Sanata Rabi'u Kwankwaso kan rawar da ya taka wajen fitar da ƴan takarar inda ya ce, Kwankwaso ya shafe kusan sati guda wajen lura da yadda aka zaɓi ƴan takarar.

Ya kuma bayyana kokarin jam'iyyar na shigar da mata a dama dasu inda ya ce bada takarar ga Sa'adatu yana nuni ne da kwarin gwiwar da ake da shi kan shugabancin mata.